Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 11/1 pp. 4-6
  • Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Mafi Kyau Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Mafi Kyau Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Manne wa Matarka
  • Idan Matsala ta Taso Kuma Fa?
  • Yin Gaskiya a Dukan Abu
  • Dukan Jama’a Sukan Amfana
  • Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Ita ce Tarbiyya Mafi Kyau
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Kasance Da Ra’ayi Mai Kyau Idan Kana Fuskantar Matsala A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 11/1 pp. 4-6

Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Mafi Kyau Ce?

“JAM’IYYA tana bukatar dokoki da za su ba wa jama’arta kāriya da ja-gora.” Haka wani Bajamushe ƙwararen marubuci kuma mai ba da labarai a telibijin ya ce. Babu shakka, wannan haka yake. Domin jam’iyyar ’yan Adam ta kafu kuma ta ci gaba, jama’a suna bukatar tushe mai ƙarfi na mizanai da kowa ya yarda da shi wanda zai bambanta abu mai kyau daga mara kyau, nagarta daga mugunta. Tambayar ita ce: Waɗanne mizanai ne suka fi kyau, ga jam’iyya da kuma jama’arta?

Idan ɗabi’un Littafi Mai Tsarki ne mizani da aka karɓa, ya kamata su taimake mutane su samu rayuwa mai kyau, na farin ciki. Idan aka ci gaba kuma, za su sa jam’iyyar jama’ar da suke bin waɗannan mizanan farin ciki kuma su kafu sosai. Haka ne yake? Bari mu bincika abin da Littafi Mai Tsarki zai ce a kan batutuwa biyu masu muhimmanci: aminci cikin aure da kuma yin gaskiya a rayuwar yau da kullum.

Ka Manne wa Matarka

Mahaliccinmu ya halicci Adamu sai ya yi Hauwa’u ta zama masa mataimakiya. Haɗa su ne aure na farko a tarihi kuma domin ya tabbata ne. Allah ya ce: “Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa.” Shekara 4,000 bayan haka, Yesu Almasihu ya sake faɗan wannan mizani na aure ga dukan mabiyansa. Kuma, ya haramta jima’i da wadda ba ka aura ba.—Farawa 1:27, 28; 2:24; Matiyu 5:27-30; 19:5.

Littafi Mai Tsarki ya ce, muhimman abu guda biyu domin farin ciki a aure su ne ƙauna, da kuma ladabi daga wurin ma’auratan dukansu biyu. Maigidan, wanda shi ne shugaban gidansa, ya kamata ya nuna ƙauna ba ta son kai ba ta wajen yin abin da yake da kyau ga matarsa. Ya kamata ya “yi zaman ɗa’a da” ita kuma kada ya yi mata “kaushin hali.” Matar kuma ya kamata ta daraja ‘mijinta yadda ya dace.’ Idan ma’aurata suka bi wannan umurnin, yawancin damuwar aure za a guje musu ko kuma a magance su. Mijin zai so ya manne wa matarsa matar kuma ga mijinta.—1 Bitrus 3:1-7; Kolosiyawa 3:18, 19; Afisawa 5:22-33.

Mizanin Littafi Mai Tsarki na manne wa matarka yana kawo farin ciki ne a aure? Ka yi la’akari da sakamakon wani bincike da aka yi a Jamus. Aka tambayi mutane, waɗanne abubuwa ne suke da muhimmanci a aure mai kyau. Abu na farko da suka faɗa shi ne aminci tsakanin mata da miji. Ba za ka yarda da cewa mutane masu aure sun fi farin ciki ba idan suka san cewa matansu ko mazansu amintattu ne?

Idan Matsala ta Taso Kuma Fa?

To, yaya idan mata da miji ba su jitu ba ƙwarai bisa wani abu? Yaya idan ƙaunarsu ta shuɗe? A irin wannan yanayin bai fi kyau ba kawai a kashe auren? Ko kuma dai mizanin Littafi Mai Tsarki na cewa miji ya manne wa matarsa har ila abu ne mai kyau da za a yi?

Marubuta Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa ga dukan ma’aurata matsala za ta taso domin ajizancinmu na ’yan Adam. (1 Korantiyawa 7:28) Duk da haka, ma’aurata da suka bi mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a suna ƙoƙari su gafarta wa juna kuma su warware matsalolinsu tare. Hakika, da akwai yanayi—kamar su zina ko kuma cin mutunci—da zai sa Kirista ta yi yaji ko kuma ta nemi kashe aure. (Matiyu 5:32; 19:9) Kashe aure cikin hanzari ba da wani kakkaurar dalili ba domin a sake wani aure yana nuna son kai na rashin la’akari da wasu. Babu shakka ba ya kawo zaman lafiya da farin ciki a rayuwa. Mu ga wani misali.

Peter ya fuskanci cewa aurensa babu farin ciki da yake da shi dā.a Saboda haka, ya bar matarsa ya je yana zama da Monika, wadda ta gudu daga gidan mijinta. Sai me ya faru? Cikin watanni kaɗan, Peter ya yarda cewa zama da Monika “ba shi da sauƙi kamar yadda na yi tsammani.” Me ya sa? Rashin hali na ’yan Adam ya bayyana a wannan dangantakar kamar yadda yake a tsohon. Shawararsa da yake cikin hanzari kuma na son kai ya jefa shi cikin matsala mai tsanani na rashin kuɗi, wannan kuwa ya tsananta abubuwa. Bugu da ƙari, wannan canji a yanayin rayuwa ya tsotsa wa ’ya’yan Monika rai.

Kamar yadda wannan labarin ya nuna, idan aure ya fuskanci matsala, guje wa auren ba shi ne zai magance matsalar ba. A wani ɓangare, idan aka fuskanci matsala, bin mizanan Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, sau da yawa yakan riƙe aure ya kuma magance matsalar. Abin da ya faru ke nan tsakanin Thomas da Doris.

Thomas da Doris sun yi aure fiye da shekara 30, sai Thomas ya shiga maye. Doris ta faɗa cikin baƙin ciki, dukansu biyu suka soma zancen kashe aurensu. Doris ta gaya wa wata Mashaidiyar Jehovah. Mashaidiyar ta nuna wa Doris abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da aure, ta ƙarfafa ta kada ta yi hanzarin kashe aurenta, amma da farko ta haɗa hannu da maigidanta su yi ƙoƙari su magance matsalar. Haka Doris ta yi. Cikin watanni kaɗan ba a zancen kashe aure kuma. Thomas da Doris sun haɗa hannu wajen magance matsalolinsu tare. Bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa aurensu kuma ya ba su lokacin magance matsalolinsu.

Yin Gaskiya a Dukan Abu

Manne wa mata ko miji yana bukatar ɗabi’a mai kyau da kuma ƙaunar mizani. Waɗannan halaye ne ake bukata a kasance da su a wannan duniyar ta rashin gaskiya. Littafi Mai Tsarki yana da abin faɗa da yawa game da yin gaskiya. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci na ƙarni na farko a Yahudiya: “Muna kuwa so mu tafiyar da al’amuranmu da halin kirki ne.” (Ibraniyawa 13:18) Menene wannan yake nufi?

Mutum mai yin gaskiya yana faɗan gaskiya kuma ba ya zamba. Ba shi da son kai a hulɗansa da wasu—yana yin gaskiya, yana ba da daraja, ba ya yaudara. Bugu da ƙari, mutum mai yin gaskiya mai aminci ne wanda ba ya cutan mutane. Mutane masu yin gaskiya suna kawo yarda da dogara wanda yake kai wa ga halaye nagari kuma yakan kyautata dangantaka tsakanin mutane.

Masu yin gaskiya suna farin ciki kuwa? Hakika, suna da dalilin farin ciki. Duk da yawan rashawa da cuta—ko kuma dominsu—galibi na son mutane masu yin gaskiya. Bisa ga wani bincike da aka yi tsakanin matasa, yin gaskiya hali ne da kashi 70 bisa ɗari na waɗanda aka yi musu tambaya suka ɗaukaka. Ƙari ga haka, ko nawa shekarun mu, yin gaskiya shi ne hali na farko ga waɗanda muke yin abota da su.

An koya wa Christine sata tun tana ’yar shekara 12 da haihuwa. Da shigewar shekaru sai ta zama ƙwararriyar ’yar sane. Ta ce: “Da akwai ranakun da nake zuwa gida da sabar kuɗi har DM 5,000 [dala 2,200].” An kama Christine sau da yawa, kuma tana zama cikin haɗarin zuwa gidan yari. Da Shaidun Jehovah suka yi mata bayani game da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yin gaskiya, Christine ta yi sha’awar abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ɗabi’a. Ta koyi yin biyayya ga gargaɗin nan: “Kada ɓarawo ya ƙara yin sata.”—Afisawa 4:28.

A lokacin da Christine ta yi baftisma ta zama Mashaidiyar Jehovah, ta bar sata. Tana ƙoƙari ta yi gaskiya a dukan abu, tun da Shaidu sun ba da ƙarfi wajen nanata yin gaskiya da wasu halayen Kirista. Jaridar Lausitzer Rundschau ta ba da rahoto: “Kalmomin ɗabi’a kamar su yin gaskiya, daidai wa daida, ƙaunar maƙwabci ana ɗaukaka su a imanin Shaidu.” Yaya Christine ta ji game da canji da ta yi a rayuwarta? “Na fi farin ciki yanzu da na daina sata. Ina jin ina da daraja a cikin jama’a.”

Dukan Jama’a Sukan Amfana

Mutane da suke da aminci ga matansu kuma waɗanda suke yin gaskiya ba kawai suna da farin ciki ba amma kuma suna da amfani ga jam’iyya duka. Masu ba da aiki sun fi son mutane da ba sa cuta. Dukanmu muna son mu sami maƙwabta masu aminci, muna son cefane a kantin ɗan kasuwa mai yin gaskiya. Ba ma daraja ’yan siyasa, ’yan sanda, da kuma alƙalai waɗanda suke guje wa rashawa ne? Jam’iyya tana amfana ƙwarai idan jama’arta suna yin gaskiya domin mizani ne ba domin kawai sun sami sukunin yin haka ba.

Bugu da ƙari, ma’aurata masu aminci tushe ne na iyalai masu ƙarfi. Kuma mutane da yawa za su yarda da ɗan siyasan Turai wanda ya ce: “Iyali na [al’ada] ya kasance har wa yau mafaka mafi muhimmanci na kwanciyar rai da ma’ana.” Iyali mai zaman lafiya, inda manya da ’ya’ya suke da damar su sami kwanciyar rai ne. Waɗanda suke da aminci a aurensu suna taimakawa wajen gina jam’iyya mai ƙarfi.

Ka yi tunanin yadda kowa zai amfana idan babu mata da aka sake, babu kotun kashe aure, ko na riƙe yara. Kuma yaya idan babu ’yan sane, ɓarayi, masu almubazzaranci, ma’aikata masu cin hanci, ko kuma masana kimiyya masu zamba? Wannan kamar mafarki ne kawai? Ba ga waɗanda suka ɗauki Littafi Mai Tsarki da muhimmanci ba da kuma abin da ya ce game da abin da zai faru a nan gabanmu. Kalmar Allah ta yi alkawarin cewa Mulkin Jehovah ta hannun Almasihu ba da daɗewa ba zai karɓi sarautar dukan jam’iyyun ’yan Adam a duniya. A ƙarƙashin wannan Mulkin dukan talakawansa za a koya musu su rayu bisa ɗabi’un Littafi Mai Tsarki. A wannan lokacin, “adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, su gāje ta har abada.”—Zabura 37:29.

Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Ita ce Tarbiyya Mafi Kyau

Miliyoyin mutane da suka bincika Nassosi Masu Tsarki sun zo ga fahimtar cewa gargaɗin Littafi Mai Tsarki yana bisa hikimar Allah ce, wanda ya fi tunanin mutane sosai. Waɗannan sun ga Littafi Mai Tsarki amincecce ne kuma yana da amfani a rayuwa ta duniyar zamani. Sun san cewa bin gargaɗin Kalmar Allah zai amfane su.

Saboda haka, irin waɗannan mutane suke bin abin da Mahaliccinmu ya ce ta bakin annabi Ishaya: “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da ke daidai.” (Karin Magana 3:5, 6) A yin haka, sun kyautata rayuwarsu ƙwarai, kuma sun inganta rayuwar waɗanda suka kewaye su. Kuma sun sami gaba gaɗi ga “rai . . . na nan gaba,” lokacin da dukan talikai za su bi tarbiyyar Littafi Mai Tsarki.—1 Timoti 4:8.

[Hasiya]

a An canja sunaye a wannan talifin.

[Bayanin da ke shafi na 5]

Idan aka fuskanci matsala a aure, bin mizanan Littafi Mai Tsarki sau da yawa yakan riƙe aure ya kuma magance matsalar

[Bayanin da ke shafi na 6]

Duk da yawan rashawa da cuta—ko kuma dominsu—galibi suna son mutane masu yin gaskiya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba