Tarbiyya Tana Lalacewa
“IRIN wannan abin ba ya faruwa,” in ji Helmut Schmidt, ministan jiha na dā a Jamus. Yayin da yake nuna ɓacin ransa a kan maguɗi da ma’aikata suke yi da ya zama kan magana a jaridu. Ya ce: “Ɗabi’a ta lalace domin haɗama.”
Mutane da yawa za su yarda da abin da ya ce. Ɗabi’u da suka yi jijiya a Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, waɗanda da yawa suka karɓa da daɗewa a kan magwajin nagarta da mugunta, an tura su gefe guda. Haka yake a ƙasashe ma da ake ɗaukansu na Kirista.
Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki Tana da Muhimmanci Kuwa?
Tarbiyyar da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ta haɗa da yin gaskiya da kuma aminci. Duk da haka, cuta, rashawa, da kuma zamba sun zama ruwan dare gama gari. Jaridar The Times ta London ta ba da rahoton cewa wasu ’yan sandan ciki “ana zaton suna saka fam 100,000 cikin aljihunsu kowane lokaci da suka mai da miyagun ƙwayoyi ga masu shi domin su sayar ko kuma idan suka yi hasarar tabbacin adadin waɗannan miyagun.” A Austria aka ce zamba ta inshora ita ce abin da ake yi kullum. A Jamus ’yan kimiyya sun razana lokacin da manazarta a baya bayan nan suka gano “ɗaya daga cikin zamba mafi ban kunya a kimiyyar Jamus.” Wani shehun malami, “mafi ɗaukaka tsakanin masana jintsi a Jamus,” an tuhume shi da ƙage mai yawa.
Tarbiyya daga Littafi Mai Tsarki har ila ta ƙunshi aminci cikin aure, wanda ake yi domin ya tabbata. Amma aure-aure da yawa suna ƙarewa a kotun kashe aure. Jaridar Katolika Christ in der Gegenwart (Kiristoci na zamani guda) ta ba da rahoto cewa “har a Switzerland mai ‘al’ada’ ma, ana kashe aure-aure da yawa.” A Netherlands ana kashe
kashi 33 bisa ɗari na dukan aure-aure da aka yi. Wata mata da ta lura da canji da aka yi a Jamus a cikin shekaru kaɗan da suka gabata ta rubuta damuwarta: “Yanzu an ɗauki aure tsohon yayi wanda ba shi da amfani. Mutane yanzu ba sa aure don ya tabbata.”
A gefe ɗaya kuma, miliyoyin mutane sun ɗauki ɗabi’a da aka koyar a cikin Littafi Mai Tsarki aba ce da za a dogara da ita kuma muhimmiyar aba ce a duniyarmu ta zamani. Wasu ma’aurata da suke da zama a iyakar Swiss da Jamus sun gano cewa rayuwa bisa ɗabi’un Littafi Mai Tsarki ta ba su farin ciki ƙwarai. A gare su kam, “dukan fannonin rayuwa suna da mai ja-gora ɗaya ne kawai. Littafi Mai Tsarki.”
Yaya ka ke ji? Littafi Mai Tsarki zai iya kasancewa mai ja-gora mai amfani kuwa? Tarbiyyar Littafi Mai Tsarki tana da amfani kuwa a yau?