Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ishaya sura ta 53 tana ɗauke da muhimmin annabci game da Almasihu. Aya ta 10 ta ce: “Ubangiji ya nufa a ƙuje shi; ya sa masa azaba.”a Menene wannan take nufi?
Yana da sauƙi a ga abin da ya sa za a yi tambaya game da Ishaya 53:10. Kiristoci na gaskiya ba za su yi tunanin cewa Allah mai juyayi da ƙauna zai nufa ya ƙuje ko kuma ya gana wa wani azaba ba. Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalilin yin gaba gaɗi cewa Allah ba ya farin ciki wajen gana wa talikai azaba. (Kubawar Shari’a 32:4; Irmiya 7:30, 31) A cikin ƙarnuka da suka shige Jehovah a wasu lokatai ya ƙyale wahala don dalilai da suka jitu da hikimarsa da kuma ƙaunarsa. Babu shakka bai haddasa azabar da ƙaunataccen Ɗansa Yesu, ya sha ba. To, menene ainihi wannan ayar take nufi?
Za a iya taimakonmu mu fahimci ma’anar wannan idan muka bincika ayar ga baki ɗayanta, muka lura da bayyanar kalmar nan “nufa” da irinta. Ishaya 53:10 ta ce: “Ubangiji ya nufa a ƙuje shi; ya sa masa azaba: lokacin da za ka maida ransa hadaya domin zunubi, za ya ga zuriyarsa, za ya tsawanta kwanakinsa, nufin Ubangiji kuma za ya yi albarka a cikin hannunsa.”
A nan Littafi Mai Tsarki yana nuna cewa ‘nufi na Ubangiji,’ da aka ambata a ƙarshen aya, yana nuni ne ga cika ƙudurinsa ta Mulkin. Yin haka zai sa Jehovah ya kunita ikon mallakarsa da zai sa a cire zunubi da mutane masu biyayya suka gada—zunubanmu. (1 Labarbaru 29:11; Zabura 83:18; Ayukan Manzanni 4:24; Ibraniyawa 2:14, 15; 1 Yohanna 3:8) Hanya da za a samu dukan wannan shi ne Ɗan Allah ya zama mutum kuma ya yi tanadin hadayar fansa. Yadda muka sani, a yin haka Yesu ya sha wuya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ya “koya biyayya ta wurin wahala da ya sha.” Saboda haka Yesu ya amfana daga wannan wuya da ya sha.—Ibraniyawa 5:7-9.
Yesu ya sani tun da fari cewa tafarki mai kyau da zai ɗauka zai ƙunshi shan wasu azaba. Wannan a bayane yake a kalmominsa da ke rubuce a Yohanna 12:23, 24, inda muka karanta: “Sa’a ta zo da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. Hakika, hakika, ina ce maku, Ƙwayar alkama idan ba ta faɗi a cikin ƙasa ta mutu kuma, sai ta zauna ita ɗayanta; amma idan ta mutu sai ta bada ’ya’ya dayawa.” Hakika, Yesu ya san cewa ya kamata ya tsaya da ƙarfi har mutuwa. Labarin ya ci gaba: “Yanzu a raina yana wahala; me zan ce kuma? Ya Uba ka cece ni daga cikin lokacin nan? Amma saboda wannan na zo cikin lokacin nan. Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji murya daga sama ta ce, “Na rigaya na ɗaukaka shi, kuma zan sake ɗaukaka shi.”—Yohanna 12:27, 28; Matta 26:38, 39.
A wannan matanin ne za mu fahimci Ishaya 53:10. Jehovah ya san cewa abin da Ɗansa zai fuskanta zai ƙunshi ƙuje shi. Amma saboda ɗaukaka da sakamako mai kyau da zai kawo, Jehovah ya ji daɗin abin da Yesu zai fuskanta. A wannan azanci Jehovah ‘ya nufa a ƙuje shi’ ko kuma ƙujewan Almasihun. Yesu ya yi murna da abin da zai iya yi, ya cika ta. Hakika, yadda Ishaya 53:10 ya kammala, ta wurinsa ‘nufin Jehovah kuma zai cika.’
[Hasiya]
a Sai dai ko an ba da alama, dukan ayoyi da aka yi amfani da su a cikin wannan talifin an ɗauko su ne daga cikin Litafi Mai-Tsarki.