Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 9/1 pp. 9-14
  • Hadayu Na Yabo Da Ke Faranta Wa Jehovah Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hadayu Na Yabo Da Ke Faranta Wa Jehovah Rai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Domin a Koya Mana Kuma a Yi Mana Ta’aziyya
  • Ka Miƙa Hadayu Masu Tsarki Marasa Aibi
  • Ka Miƙa Hadayu na Yabo da Dukan Zuciyarka
  • Albarka Mai Yawa Daga Jehovah Yana Jiran Mu
  • Hadayu Da Suke Faranta Wa Allah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Koya Daga “Surar Gaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ba da Hadayu da Dukan Zuciyarmu ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Za Ka Yi Sadaukarwa Saboda Mulkin Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 9/1 pp. 9-14

Hadayu Na Yabo Da Ke Faranta Wa Jehovah Rai

“Ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah.”—ROMAWA 12:1.

1. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da amfanin hadayu a ƙarƙashin Dokar Musa?

“TUN da ya ke Shari’a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda ke kusatar Allah ta waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.” (Ibraniyawa 10:1) A furci da yake a fayyace, manzo Bulus ya tabbatar da cewa dukan hadayu da aka miƙa a ƙarƙashin Dokar Musa amfaninsu ba na dindindin ba ne a batun ceton mutane.—Kolossiyawa 2:16, 17.

2. Me ya sa ba ɓata lokaci ba ne kawai mu yi ƙoƙari mu fahimci abin da yake cikin Littafi Mai Tsarki game da sadakoki da hadayu na Doka dalla-dalla?

2 Wannan yana nufin cewa abin da yake cikin littattafai biyar na farko game da sadakoki da hadayu ba su da amfani ga Kiristoci a yau ke nan? Hakika, shekara ta shige da kaɗan, waɗanda suke Makarantar Hidima ta Allah a cikin iklisiyoyi na Shaidun Jehovah a duka duniya sun karanta littattafai biyar na farko a cikin Littafi Mai Tsarki. Wasu sun yi ƙoƙari sosai su karanta kuma su fahimci dukansu dalla-dalla. Duk ƙoƙarinsu a banza ne? Ba zai kasance haka ba, domin “duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta ne domin a koya mana, domin mu ɗore cikin sa zuciyan nan tamu ta haƙuri da ta’aziyyar da Littattafai ke yi mana.” (Romawa 15:4) Tambayar ita ce, wace ‘koyarwa’ da ‘ta’aziyya’ za mu iya samu daga abubuwa masu yawa da ke cikin Doka game da sadakoki da hadayu?

Domin a Koya Mana Kuma a Yi Mana Ta’aziyya

3. Wace bukata ta musamman muke da ita?

3 Ko da ba a bukatar a miƙa hadayu na zahiri yadda Doka ta faɗa, har ila muna bukatar abin da hadayu suka yi wa Isra’ilawa, wato, a gafarta mana zunubanmu kuma mu more alherin Allah. Tun da yake ba ma miƙa hadayu na zahiri, yaya za mu sami irin wannan albarka? Bayan ya yi maganar kasawan hadayun dabbobi, Bulus ya ce: “Da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, ‘Hadaya da sadakoki kam, ba ka so, amma ka tanadar mini jiki. Ba ka farin ciki da hadayar ƙonawa, da kuma hadayar kawar da zunubai. Sa’an nan na ce, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,’ Kamar yadda yake rubuce game da ni a Littafi.’ ”—Ibraniyawa 10:5-7.

4. Ta yaya Bulus ya yi amfani da Zabura 40:6-8 ga Yesu Kristi?

4 Da ya ɗauko ayoyi daga Zabura 40:6-8, Bulus ya nuna cewa Yesu bai zo ba don ya sa “hadayu da [sadakoki]” “hadayun ƙonawa da [sadakoki] na kawar da zunubi” su zama na dindindin ba, duka a lokacin da Bulus yake rubutu Allah ya daina karɓansu. Maimako, Yesu ya zo da jiki da Ubansa na samaniya ya shirya, wanda ya yi daidai ta kowace hanya da wanda Allah ya shirya lokacin da Ya halicci Adamu. (Farawa 2:7; Luka 1:35; 1 Korinthiyawa 15:22, 45) Kamiltacce Ɗan Allah, Yesu yana matsayin “zuriyar” macen, yadda aka annabta a Farawa 3:15. Zai ɗauki matakai ya ‘ƙuje kan Shaiɗan,’ ko da Yesu kansa za a ‘ƙuje diddigensa.’ A ta haka, Yesu ya zama hanya da Jehovah ya yi wa mutane tanadin ceto, wanda mutane masu bangaskiya suke sauraro tun kwanakin Habila.

5, 6. Wace hanya mafi kyau ce Kiristoci suke da ita da za su iya kusatowa ga Allah?

5 Da yake magana game da wannan matsayi na musamman da Yesu yake da shi, Bulus ya ce: “Shi da bai san zunubi ba Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.” (2 Korinthiyawa 5:21) Za a iya fassara furcin nan “mai da shi zunubi” zuwa ‘hadaya ta zunubi.’ Manzo Yahaya ya ce: “Shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.” (1 Yahaya 2:2) Saboda haka, yayin da Isra’ilawa suna da hanya na ɗan lokaci ta kusatowa da Allah ta hadayunsu, Kiristoci suna da hanya mafi kyau na zuwa wurin Allah—hadayar Yesu Kristi. (Yahaya 14:6; 1 Bitrus 3:18) Idan muka ba da gaskiya a hadayar fansa da Allah ya yi tanadinsa kuma muka yi masa biyayya, mu ma za a gafarta mana zunubanmu kuma za mu more alheri da albarkar Allah. (Yahaya 3:17, 18) Wannan bai zama da ban ta’aziyya ba ne? To, ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya cikin hadayar fansar?

6 Bayan ya bayyana cewa Kiristoci suna da tushe mafi kyau na kusato Allah, manzo Bulus ya tsara kamar yadda muka karanta a Ibraniyawa 10:22-25 hanyoyi uku da za mu nuna bangaskiyarmu da godiya don tanadi mai kyau da Allah ya yi. Ko da yake gargaɗin Bulus ga waɗanda musamman suke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki” ne—wato, shafaffun Kiristoci da aka kira su zuwa sama—babu shakka dukan mutane suna bukatar su mai da hankali ga kalmomin Bulus da aka hure idan suna so su amfana daga hadayar fansa ta Yesu.—Ibraniyawa 10:19.

Ka Miƙa Hadayu Masu Tsarki Marasa Aibi

7. (a) Yaya Ibraniyawa 10:22 ya nuna yadda ake hadaya? (b) Menene za a yi don a tabbata cewa Allah ya karɓi hadaya?

7 Da farko, Bulus ya aririce Kiristoci: “Sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatanmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.” (Ibraniyawa 10:22) Kalmomi da aka yi amfani da su a nan suna nuna abin da aka yi a hadaya ta zahiri a ƙarƙashin Doka. Wannan ya dace domin kafin a amince da wata hadaya, sai an miƙa ta da muradi mai kyau kuma aba mai tsarki mara aibi. Ana kawo dabbobi na hadaya daga garken shanu da na tumaki, wato dabbobi masu tsabta, ‘lafiyayyu’ marasa lahani. Idan hadayu na tsuntsaye ne, za su zama kurciyoyi ko kuma ’yan tantabarai. Idan an yi waɗannan, “[za a] karɓa masa, a kuwa yi masa gafara.” (Littafin Firistoci 1:2-4, 10, 14; 22:19-25) Ba a saka yisti a hadaya ta gari, wanda alama ne na aibi; ba za a zuba zuma ba, mai yiwuwa yana nufin ruwan ’ya’yan itace da aka kwaɓa, da zai sa garin ya kumbura. Yayin da ake miƙa hadayu—dabba ko gari—a kan bagade ana haɗa gishiri da zai sa ya daɗe.—Littafin Firistoci 2:11-13.

8. (a) Menene ake bukata daga mutum da yake miƙa hadaya? (b) Yaya za mu tabbata cewa Jehovah ya amince da bautarmu?

8 Mutumin da ke miƙa hadayar fa? Doka ta ce duk wanda yake zuwa gaban Jehovah dole ne ya kasance mai tsarki kuma mara aibi. Wanda yake da aibi don wani dalili, zai fara da miƙa hadaya ta zunubi ko ta laifi ga Jehovah don ya mayar da tsayawansa mai tsarki a gaban Allah, don ya karɓi ƙonanniyar hadayarsa ko kuma hadayarsa ta salama. (Littafin Firistoci 5:1-6, 15, 17) Saboda haka, mun fahimci muhimmancin riƙe kasancewa da tsarki koyaushe a gaban Jehovah? Idan muna so Allah ya amince da bautarmu, dole ne mu yi hanzari mu daidaita kowane dokokin Allah da muka karya. Ya kamata mu yi sauri mu yi amfani da taimako da Allah ya ke bayarwa—“dattawan iklisiya” da “hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu,” Yesu Kristi.—Yakubu 5:14; 1 Yahaya 2:1, 2.

9. Menene bambanci na musamman tsakanin hadayu da ake yi wa Jehovah da waɗanda ake miƙa wa allolin ƙarya?

9 Kasance a ware daga kowace irin ƙazanta ita ce bambanci na musamman tsakanin hadayu da ake miƙa wa Jehovah da waɗanda mutane cikin al’ummai da suke kewaye Isra’ila ke miƙa wa allolin ƙarya. Da yake maganar wannan bambanci na hadayu cikin Dokar Musa, wani aikin bincike ya lura: “Mun lura cewa ba abin da ya haɗa dokar Musa da duba; bori, mutum ya gurgunta kansa, ko kuma karuwanci mai tsarki, an haramta yin bukukuwa na ɗaukaka allan ni’ima; ba a hadaya da mutum; babu hadayu ga matattu.” Duka waɗannan sun nuna gaskiyar cewa: Jehovah mai tsarki ne, bai amince da zunubi ba da kuma kowane irin ɓatanci. (Habakuk 1:13) Sujjada da hadayu da ake yi masa dole su zama masu tsarki marasa aibi—ta jiki, ta ɗabi’a, da kuma ta ruhaniya.—Littafin Firistoci 19:2; 1 Bitrus 1:14-16.

10. Cikin jituwa da gargaɗin Bulus da ke rubuce a Romawa 12:1, 2, wane bincike ya kamata mu yi wa kanmu?

10 Saboda haka, ya kamata mu binciki kanmu a duk fannonin rayuwa don mu tabbata cewa Jehovah yana amincewa da hidimarmu. Bai kamata mu yi tunani cewa muddin muna zuwa taron Kirista kuma muna hidima, babu wani damuwa game da abin da muke yi a ɓoye. Bai kamata muna jin cewa sa hannu cikin ayyukan Kirista zai fitar da mu daga bukata na bin dokokin Allah a wasu wurare na rayuwarmu ba. (Romawa 2:21, 22) Ba za mu yi zaton alheri da albarkan Allah ba idan mun bar wani abu mara tsarki ko kuma mai ƙazanta a gabansa ya ɓata tunaninmu da ayyukanmu. Ka tuna da kalmomin Bulus: “Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi. Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabonta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.”—Romawa 12:1, 2.

Ka Miƙa Hadayu na Yabo da Dukan Zuciyarka

11. Menene furci “bayyana yarda” da aka ambata a Ibraniyawa 10:23 ya ƙunsa?

11 A rubutu da ya yi zuwa ga Ibraniyawa, Bulus ya jawo hankali ga fanni na musamman a bautar gaskiya: “Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga sa zuciyan nan tamu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne.” (Ibraniyawa 10:23) Furci “bayyana yarda” a zahiri yana nufin “ikirari,” Bulus kuma ya yi maganar ‘hadaya ta yabo.’ (Ibraniyawa 13:15) Wannan ya tuna mana irin hadayar da mutane kamar su Habila, Nuhu, da Ibrahim suka miƙa.

12, 13. Menene Ba’isra’ile ya fahimta lokacin da ya miƙa hadaya ta ƙonawa, menene za mu iya yi don mu nuna irin wannan halin?

12 Yayin da Ba’isra’ile ya miƙa hadaya ta ƙonawa, yana yi ne “ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.” (Littafin Firistoci 1:3) Da irin wannan hadaya, yana shaidar bege da son rai, ko kuma amincewa da albarka mai yawa da jinƙan Jehovah ga mutanensa. Ka tuna cewa bambancin hadayar ƙonawa ita ce wuta za ta cinye hadayar gaba ɗaya a kan bagade—alama da ta dace da ba da kai gaba ɗaya da kuma keɓewar kai. A yin daidai da wannan, muna nuna bangaskiyarmu a hadayar fansa da kuma godiyarmu don wannan tanadi yayin da da yardan rai da kuma dukan zuciyarmu muna miƙa ‘hadaya ta yabo wato ’ya’yan leɓuna,’ ga Jehovah.

13 Ko da Kiristoci ba sa miƙa hadayu na zahiri na dabba ko ganye suna da hakkin yin shaidar bisharar Mulki kuma su almajirantar da mutane wa Yesu Kristi. (Matiyu 24:14; 28:19, 20) Kana yin amfani da zarafin da ka ke da shi ka yi shelar bisharar Mulkin Allah ga mutane don ƙarin mutane da yawa su zo ga sanin abubuwa masu ban al’ajibi da Allah ya ke da shi ga mutane masu biyayya? Da yardan rai kana ba da lokacinka da ƙarfinka a koya wa waɗanda suke da marmari kuma suke son ka taimake su su zama almajiran Yesu Kristi? Yin hidima da ƙwazo, kamar ƙanshi mai daɗi na hadaya ta ƙonawa tana faranta wa Allah rai.—1 Korantiyawa 15:58.

Ka Yi Murna a Yin Zumunci da Allah da Mutane

14. Ta yaya kalmomin Bulus a Ibraniyawa 10:24, 25 suka yi daidai da ra’ayin hadaya ta salama?

14 A ƙarshe, Bulus ya jawo hankali ga dangantakarmu da ’yan’uwa Kiristoci yayin da muke bauta wa Allah. “Mu kuma riƙa kula da juna, ta yadda za mu ta da juna a tsimi mu yi ƙauna da aiki nagari. Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu ke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranan nan tana kusatowa ba.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Furcin nan “ta da juna a tsimi mu yi ƙauna da aiki nagari,” “yin taronmu,” da “ƙarfafa wa juna zuciya” duka sun tuna mana abin da hadaya ta salama a cikin Isra’ila ta yi wa mutanen Allah.

15. Wane hannun riga ne yake tsakanin hadaya ta salama da taron Kirista?

15 Kalmar Ibrananci ta “salama” a cikin furcin nan “hadaya ta salama” jam’i ce, da wataƙila yake nuna cewa sa hannu cikin irin waɗannan hadayu yana kawo salama da Allah kuma da ’yan’uwa masu bi. Game da hadaya ta salama, wani manazarci ya lura: “Hakika wannan lokaci ne na zumunci na farin ciki tare da Allah na Alkawari, da Yake ƙasƙantar da kansa ya zama Baƙon Isra’ilawa a lokacin hadaya, yadda Yake Mai marabtansu koyaushe.” Wannan ya tunatar mana da alkawarin Yesu: “Inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.” (Matiyu 18:20) Koyaushe da muka halarci taron Kirista, muna amfana daga cuɗanya mai ginawa, koyarwa da ke ƙarfafawa, da kuma sanin cewa Ubangijinmu Yesu Kristi yana tare da mu. Wannan yana sa taron Kirista ya zama lokacin farin ciki na gaske da kuma lokacin ƙarfafa bangaskiya.

16. Da hadaya ta salama a zuci, me ke sa taron Kirista ya zama na farin ciki ƙwarai?

16 A hadaya ta salama, duk kitsen—da ke wajejen hanji, ƙodoji, gefen jikin hanta, da kwankwaso, haɗe da wutsiya mai kitse na tunkiyar—ana miƙa wa Jehovah ta wurin ƙonawa, a sa su yi hayaƙi a kan bagade. (Littafin Firistoci 3:3-16) Ana ɗaukan kitse mafi amfani kuma mafi kyau a jikin dabbar. Miƙa kitsen a kan bagade tana nuna cewa ana ba Jehovah mafi kyan. Abin da yake sa taron Kirista ya zama da murna musamman shi ne, ba samun koyarwa kawai muke yi ba amma kuma muna yabon Jehovah. Za mu yi wannan ta sa baki—da gwargwadon iyawarmu—a rera waƙa da dukan zuciyarmu, sauraro sosai, da yin kalami inda ya yiwu. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji!” in ji mai zabura. “Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi cikin taron jama’arsa masu aminci!”—Zabura 149:1.

Albarka Mai Yawa Daga Jehovah Yana Jiran Mu

17, 18. (a) Wace hadaya mai girma ce Sulemanu ya miƙa lokacin da ake keɓe haikali cikin Urushalima? (b) Wace albarka ce biki na keɓe haikali ya kawo wa mutanen?

17 Lokacin da ake keɓe haikali a Urushalima, a watan bakwai na shekara ta 1026 K.Z., Sarki Sulemanu ya miƙa ‘hadaya mai girma ga Ubangiji,’ da ta ƙunshi “hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama.” Ƙari ga abin da aka miƙa a kan hadayu na gari, an yi hadayar shanu 22,000 da tumaki 120,000 a wannan lokacin.—1 Sarakuna 8:62-65.

18 Za ka iya kwatanta yawan kuɗi da aiki da wannan biki ya ƙunsa? Duk da haka, albarka da babu shakka Isra’ilawa suka samu ya fi kuɗin. A ƙarshen idodin, Sulemanu “ya sallami jama’ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa’an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dauda, da jama’arsa, Isra’ilawa.” (1 Sarakuna 8:66) Da gaske, kamar yadda Sulemanu ya ce, “albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.”—Karin Magana 10:22.

19. Menene za mu yi don mu karɓi albarka mai yawa daga Jehovah yanzu da kuma har abada?

19 Muna zama a lokacin da “kyawawan abubuwan da ke gaba” sun sake “ainihin siffarsu.” (Ibraniyawa 10:1) Yesu Kristi a matsayin Babban Firist na alama, ya riga ya shiga cikin sama kanta kuma ya miƙa amfanin jininsa don a yi gafara ga duk waɗanda suka ba da gaskiya ga hadayarsa. (Ibraniyawa 9:10, 11, 24-26) Domin wannan babbar hadaya da kuma miƙa hadayun mu na yabo da yake da tsarki kuma mara aibi da dukan zuciya ga Allah, mu ma za mu ci gaba ‘muna murna, muna farin ciki,’ muna duba gaba ga albarka mai yawa daga Jehovah.—Malakai 3:10.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane koyarwa da ta’aziyya za mu iya samu daga abubuwa da ke cikin Doka game da hadayu da sadakoki?

• Menene bukata ta farko don a karɓi hadaya, kuma menene ma’anarsa a gare mu?

• Menene za mu iya miƙawa da ke daidai da hadayar ƙonawa ta yardan rai?

• A waɗanne hanyoyi za a gwada taron Kirista da hadaya ta salama?

[Hoto a shafi na 10]

Jehovah ya yi tanadin hadayar fansa da Yesu ya bayar don ceton mutane

[Hoto a shafi na 12]

Don Jehovah ya amince da hidimarmu, dole mu kasance a ware daga kowane irin ƙazanta

[Hoto a shafi na 13]

Muna nunawa a fili cewa mun amince da nagartar Jehovah lokacin da muke wa’azi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba