Mu Waɗanda Suke Da Bangaskiya Ne
Yaɗa Begen Kirista a Senegal
KIFI abinci ne na musamman tun daga lokatan dā. Shekaru dubbai yanzu, mutane suna kamun kifi a teku, tafkuna, da kuma koguna. Wasu manzannin Yesu Kristi masunta ne a Tekun Galili. A garesu, Yesu ya nuna musu wani irin kamun kifi. Wannan su na ruhaniya ne da ba masuntan kawai za su amfana ba amma har kifayen.
Game da wannan, Yesu ya gaya wa masunci Bitrus: “Daga nan gaba za ka kama mutane.” (Luka 5:10) A yau ana irin wannan aikin kama kifi a sama da ƙasashe 230, har da Senegal. (Matta 24:14) A nan “masunta” na zamani suna yaɗa begensu na Kirista.—Matta 4:19.
Senegal tana kan iyakar yammacin Afirka. Ta kama daga hamada ta arewa har ta dangana da kurmi mai zafi na yankin Casamance a kudu. Senegal ƙasa ce da iskar hamada take hurawa sosai da kuma sanyi, iska mai sanyi daga tekun Atlantika. A nan da akwai fiye da mutane miliyan tara. An san mazaunan Senegal da marabtar baƙi. Yawanci ba Kiristoci ba ne. Da yawa makiyaya ne, wasu suna kiwon shanu, wasu raƙuma wasu kuma awaki. Da akwai manoma, da suke nomar gyaɗa, auduga, da kuma shinkafa. Hakika, da akwai masunta, da suke dawowa da tarunsu cike da kifi daga Tekun Altantika ko kuma daga manyan koguna dabam dabam da suka bi cikin ƙasar. Kamun kifi yana da babban matsayi wajen taimaka wa tattalin arzikin Senegal. Hakika, sanannen abincin ƙasar shi ne ceebu jën, shinkafa, kifi, da kuma ganyaye.
“Masu Kama Mutane”
Da akwai masu wa’azin Mulkin Allah 863 da himma a Senegal. A farkon shekara ta 1950 ne aka fara kamun kifi na ruhaniya a can. Aka buɗe ofishin reshe na Watch Tower Society a Dakar, babban birnin ƙasar a shekara ta 1965. ’Yan wa’azi na ƙasashen waje “masunta” suka zo daga ƙasashe masu nisa. Aka soma aikin “kama kifi,” kuma yaɗa begen Kirista a Senegal ya yi gaba gaba. Daga bisani sai aka gina sabon reshe a Almadies, a iyakar Dakar, kuma aka yi bikin keɓewansa ga Jehovah a Yuni na shekara ta 1999. Lallai lokaci ne na farin ciki!
Kaluɓalen Karɓan Gaskiya
Ana saduwa da mutane daga wurare dabam dabam kowane lokaci, kuma wasu suna na’am da saƙon bege da ke cikin Kalmar Allah. Ko da yake mutane da yawa ba su da sani na Littafi Mai-Tsarki, suna murna da suka koyi cewa ba da daɗewa ba, alkawura da Jehovah Allah ya yi wa annabawa masu aminci na dā za su cika.
Sau da yawa yana bukatar gaba gaɗi a tsaya tsayin daka ga ƙa’idodin Kirista, musamman ma idan ya shafi al’adun gargajiya. Alal misali, auren fiye da mace ɗaya ana yi ko’ina cikin Senegal. Ka yi la’akari da yanayin wani mutum da ke da mata biyu kafin ya soma nazarin Littafi Mai-Tsarki. Zai sami gaba gaɗin da ake bukata don ya karɓi gaskiyar Kirista kuma ya bi farillan Nassi na ya zama mijin mace ɗaya? (1 Timothawus 3:2) Kuma zai riƙe matarsa ta ƙuruciyarsa kuwa, matar da ya aura da farko? Abin da ya yi ke nan, kuma yanzu yana hidima, dattijo ne mai himma a cikin ɗaya daga manyan ikklisiyoyin da suke a Dakar. Matarsa ta fari ta karɓi gaskiya tare da dukan yaransa 12, 10 daga matarsa ta fari 2 kuma daga matarsa ta biyu.
Wani abin da yake hana karɓan begen Kirista shi ne jahilci. Wannan yana nufin cewa jahili ba zai iya karɓan gaskiya kuma ya bi ta ba ke nan? Mai zai hana. Ka yi la’akari da misalin Marie, mace mai ƙwazo uwar ƙananan yara takwas. Nan da nan ta ga muhimmancin tattauna nassin Littafi Mai-Tsarki da yaranta kowace rana kafin su tafi makaranta ita kuma ta je aiki. Amma ta yaya za ta yi wannan, tun da yake ba ta iya karatu ba? Da safiya, ta ɗauki littafin nan Examining the Scriptures Daily ta tsaya a kan titi a gaban gidanta. Yayin da mutane suke shigewa, sai ta tambaye su ko sun iya karatu. Idan ta sami wanda ya iya karatu, sai ta ba shi littafin ta ce: “Ban iya karatu ba, don Allah za ka iya karanta mini wajen nan na yau?” Sai ta saurari karatun sosai. Sai kuma ta yi wa mutumin godiya ta shiga gida, sai nan da nan ta tattauna nassin da yaranta kafin su tafi makaranta!
Dukan Iri Irin Mutane Suna Na’am
A Senegal, ana iske mutane a zaune a kan tituna suna sayar da kifi, ganyaye, ko kuma ’ya’yan itatuwa a kasuwa ko kuma a zaune a gindin babbar bishiyar kuka suna shan ataya, wani shayi mai ɗaci. Da yake suna son su yaɗa bishara ga dukan wanda suka sadu da shi, wasu ’yan’uwa biyu suka yi magana da wani maroƙi a kan titi. Bayan sun gaishe shi, suka ce: “Mutane da yawa suna ba ka kuɗi amma ba sa tsayawa su yi magana da kai. Mun zo ne mu gaya maka wani abu da ke da muhimmanci sosai da ya shafi rayuwarka a nan gaba.” Maroƙin ya yi mamaki. “Za mu so mu tambaye ka,” sai ’yan’uwan suka ci gaba. “Me ya sa ka ke jin ake wahala sosai a duniya haka?” “Nufin Allah ne,” in ji maroƙin.
’Yan’uwan suka bayyana masa daga Nassosi kuma suka fassara masa Ru’ya ta Yohanna 21:4. Saƙon begen nan ya taɓa maroƙin nan sosai da kuwa ganin cewa da akwai wani da yake ƙaunarsa har ya tsaya ya tattauna Littafi Mai-Tsarki da shi. Hawaye ya cika masa idanu. Maimakon ya roƙi kuɗi, ya ce ’yan’uwan su kwashe dukan tsaba da ke cikin tasarsa! Shi dai ya nace har ya jawo hankalin waɗanda suke shigewa. Da ƙyar ’yan’uwan suka ce ya bar kuɗin. A ƙarshe ya yarda amma ya nace cewa su sake ziyartarsa kuma.
Babban jami’ar da ke Dakar ma tana daɗa nata gudummawa ga kamun da ake yi cikin taru na ruhaniya. Wani ɗalibi mai suna Jean-Louis da ke karatu ya zama likita ya soma nazarin Littafi Mai-Tsarki. Nan da nan ya karɓi gaskiya, ya keɓe kansa ga Jehovah, kuma aka yi masa baftisma. Burinsa shi ne ya bauta wa Allah ta yin hidimar majagaba ta cikakken lokaci, amma kuma ya so karatunsa na zama likita. Domin alkawari da ya yi da ƙasarsa, ya zame masa dole ya gama makarantarsa. Duk da haka, ya soma hidima ta majagaba na ɗan lokaci. Ba da daɗewa ba bayan ya sami takardar izinin zama likita, aka gayyace shi ya yi aiki a babban Bethel a Afirka inda ya zama likitar iyalinsu. Wani matashi kuma da aka sadu da shi a Jami’ar Dakar, shi ma yanzu yana hidima tare da iyalin Bethel na ƙasarsa.
Kamun kifi na ruhaniya a Senegal lallai yana da albarka. Ana son littattafan Shaidun Jehovah na Littafi Mai-Tsarki sosai kuma yanzu ana buga su a cikin harshen Wolof na wajen. Jin bishara a yarensu ya ƙarfafa masu zuciyar kirki da yawa suna na’am da godiya. Tare da albarkar Jehovah, babu shakka za a samu ƙarin wasu kifi da za a kama, yayin da “masuntar mutane” masu himma na Senegal sun ci gaba da yaɗa begen Kirista da aminci kuma da gaba gaɗi.
[Taswira a shafi na 31]
SENEGAL
[Inda aka Dauko]
Mountain High Maps® Copyright © 1997 Digital Wisdom, Inc.
[Hoto a shafi na 31]
Yaɗa begen Kirista a Senegal