Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Ba da Ruwa ga Iri na Gaskiya a Chile
A HAMADAR arewancin Chile, a kan yi shekaru da yawa kafin a yi ruwan sama. Amma idan aka yi ruwa, ƙasa da ta tsastsage, da inda duwatsu suka bazu sai furanni su tsiro launi dabam dabam. Wannan yana jawo hankalin masu ziyara daga ko’ina a cikin ƙasar.
Amma, akwai abu mafi kyau da ke faruwa tsakanin mutane da suke Chile. Ruwayen gaskiyar Littafi Mai Tsarki suna malala zuwa ko’ina a cikin ƙasar, kuma sahihan mutane da yawa suna “yin fure” su zama almajiran Yesu Kristi. Hanya ɗaya da ake amfani da ita wajen yaɗa wannan ruwayen gaskiya ita ce ta yin amfani da tarho. Labarai na biye sun nuna sakamako mai kyau da ake samu ta wurin yin wa’azi a wannan hanyar.
• Aka ce wata mai shela ta cikakken lokaci mai suna Karina ta gwada yadda za a yi wa’azi da tarho a wani taron ɗa’ira. Amma kuma, Karina ba ta taɓa yin irin wannan wa’azi ba. Don a ƙarfafa ta ta cika hakkinta a cikin taron, wani dattijo da matarsa suka maimaita wasu darussa a kan yadda za a yi wa’azi da tarho da ita. Sun ƙarfafa ta ta yi addu’a don ja-gora daga Jehovah cikin al’amarin. Ta yi hakan, sai ta shawarta ta gwada kiran wani.
Karina ta zaɓi lambar tarho na wani ƙauye na kusa. Mai kula da tarho ta amsa, Karina ta bayyana dalilin kira da ta yi. Matar ta amsa da kyau, suka shirya ta sake kira bayan kwana uku. Sake koma ziyara ta tarhon wadda ta yi ya kai ga nazarin Littafi Mai Tsarki, suka yi amfani da mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu? Tun lokacin, suna ta more nazari mai kyau, Karina kuwa ta aika da littattafai da za su amsa tambayoyin matar.
• Bernarda ta yi amfani da zarafi ta yi wa’azi wa wani mutum da ya kira lambar tarhonta cikin kuskure. Maimakon ta yi fushi, Bernarda ta gabatar da kanta cewa ita ɗaya ce cikin Shaidun Jehovah kuma ta ce za ta taimake shi. Suka fara taɗi, mutumin ya saurara yayin da take bayanin yadda Mulkin Allah zai kawar da rashin gaskiya ba da daɗewa ba. Mutumin ya ba Bernarda lambar tarhonsa, kuma ta koma ziyara a ta tarho. A wani taɗi da suka yi, ta karanta masa wani sashen littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Ya tambaye ta yadda zai iya samun nasa, sai Bernarda ta aika masa da ɗaya tare da Littafi Mai Tsarki. Aka shirya wani ɗan’uwa da yake yankin ya ziyarce shi kuma yanzu yana ci gaba da ‘ba da ruwa’ ga wannan “tsiro” da ke girma.
Hakika, a cikin busashiyar ƙasa ta ruhaniya ta wannan duniya, da akwai ɓoyayyun iri da suke jira su tsiro yayin da an kai musu ruwan ba da rai na ruhaniya. Dubbai masu ƙishi suna ci gaba da ‘yin fure’ kuma su yi “kumari” su zama amintattun bayin Jehovah Allah.—Ishaya 44:3, 4.