Yin Hidima Tare Da Mai Tsaro
“Ya Ubangiji, da rana ina nan tsaye tuttur a bisa bene na dako, dare duk kuma ina nan kafe a wurin tsarona.”—ISHAYA 21:8.
1. Ga waɗanne alkawura masu girma ne Jehovah da kansa yake shaida?
JEHOVAH ne Babban Mai Ƙuduri. Mala’ika da ya yi tawaye da ya zama Shaitan Iblis ba zai iya yin kome da zai wargaje ƙudurin Allah mai girma na tsarkake Sunansa ba da kuma na kafa Mulki mai kyau bisa duniya ta aljanna. (Matta 6:9, 10) A ƙarƙashin wannan sarautar, za a albarkaci mutane da gaske. Allah zai“haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” Mutane masu farinciki, masu haɗin kai za su more salama da ni’ima madawwami. (Ishaya 25:8; 65:17-25) Jehovah ne ya bada tabbacin waɗannan alkawura masu girma!
2. Waɗanne shaidu ne Jehovah ya tada a mutane?
2 Ko da yake, Mahalicci Mai Girma yana da shaidu ’yan Adam ma. Kafin lokacin Kiristoci “shaidu mai-girma” farawa da Habila, sun yi tsere na dauriya, sau da yawa a cikin yanayi mai tsanani. Misali mai kyau da suka bari yana ƙarfafa Kiristoci a yau. Kristi Yesu ne misali mafi girma na mashaidi mai gabagaɗi. (Ibraniyawa 11:2–12:2) Alal misali, ka tuna da shaida ta ƙarshe da ya bayar a gaban Bilatus Ba-Bunti. Yesu ya bayyana: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin im bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Daga 33 A.Z. har zuwa wannan shekara ta 2000 A.Z., Kiristoci masu himma sun bi misalin Yesu sun ci gaba da bada shaida, da gabagaɗi suna bayyana “ayuka masu-girma na Allah.”—Ayukan Manzanni 2:11.
Ɗarikokin Babiloniyawa
3. Ta yaya Shaitan ya yi hamayya da shaida da aka bayar game da Jehovah da kuma nufinsa?
3 Cikin shekaru aru-aru babban Ɗan Hamayya, Shaitan Iblis, cikin mugunta ya yi ƙoƙari ya hana a bada gaskiya ga shaidar shaidun Allah. Da yake “uban ƙarya” ne wannan “babban dragon, tsofon macijin,” yana ta “ruɗin dukan duniya.” Ya daɗa zafi a yaƙi da yake yi da waɗanda suke “kiyaye da dokokin Allah,” musamman ma a waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Yohanna 8:44; Ru’ya ta Yohanna 12:9, 17.
4. Ta yaya Babila Babba ta soma?
4 Shekaru 4,000 da suka shige, bayan Rigyawan kwanakin Nuhu, Shaitan ya tada Nimrod, “ƙarƙarfan mai-farauta ne a gaban Ubangiji.” (Farawa 10:9, 10) Babban birnin Nimrod, Babila (Babel), ta zama cibiyar addinin aljanu. Lokacin da Jehovah ya rikita yaren magina benen Babel, aka tarwatsa mutanen zuwa wajeje dabam dabam na duniya, kuma suka tafi tare da addinansu. Saboda haka Babila ta zama tushen daular duniya ta addinin ƙarya, da aka kira Babila Babba a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna. Wannan littafin ya annabta hukunci na wannan tsarin tsohon addini.—Ru’ya ta Yohanna 17:5; 18:21.
Al’umma ta Shaidu
5. Wace al’umma ce Jehovah ya tsara ta zama masa shaida, amma me ya sa ya ƙyale su zuwa hijira?
5 Kamar shekaru 500 bayan lokacin Nimrod, Jehovah ya tsara zuriyar Ibrahim mai aminci ta zama al’ummar Isra’ila ta zama Shaidarsa a duniya. (Ishaya 43:10, 12) Mutane da yawa na al’ummar sun bauta wa Jehovah da biyyaya. Amma dai, a cikin ƙarnuka imani na ƙarya na al’ummai da suke maƙwabtaka da Isra’ila ya lalata su, sai mutanen alkawari na Jehovah suka juya masa baya suka juya ga bautar allolin ƙarya. Saboda haka, a 607 K.Z., sojojin Babila, waɗanda Sarki Nebuchadnezzar ya ja-gorance su suka hallaka Urushalima da haikalinta suka kuma kwashe yawancin Yahudawan zuwa hijira a Babila.
6. Wace bishara ce mai tsaro na annabci na Jehovah ya sanar, kuma yaushe ne ta cika?
6 Nasara ce ƙwarai ga addinin ƙarya! Amma dai, mallaka da Babila ta yi bai jima ba. Shekaru 200 kafin aukuwar, Jehovah ya bada umurni: “Je ka, ka sa mai-tsaro: shi shaida abin da ya ke gani.” Wane labari ne wannan mai-tsaro zai sanar? “Babila ta fāɗi, ta fāɗi: dukan ƙerarrun sifofi na allolinta kuma an farfasa su har ƙasa.” (Ishaya 21:6, 9) Haka ya faru, a 539 K.Z., wannan furci na annabci ya faru da gaske. Babila ƙarƙarfa ta fāɗi, bada daɗewa ba sai mutanen alkawari na Allah suka koma ƙasar haihuwarsu.
7. (a) Menene Yahudawa suka koya daga horo na Jehovah? (b) Cikin wane tarko ne Yahuda da suka je hijiran suka faɗa, kuma menene sakamakon?
7 Yahudawa da suka komo sun koyi darussa su yi watsi da bautar gumaka da addini na sihiri. Amma dai, da shigewar lokaci suka faɗa cikin wasu tarkuna. Wasu ussan ilimi na Hellenawa ne ya ruɗe su. Wasu suka nanata al’adun mutane fiye da Kalmar Allah. Har ila yau wasu wariyar al’ummace ta rinjaye su. (Markus 7:13; Ayukan Manzanni 5:37) Yayinda aka haifi Yesu, al’ummar ta riga ta juya wa sujada mai tsarki baya. Ko da yake wasu cikin Yahudawa sun ƙarɓi bisharar mulki da Yesu ya sanar, gabaɗayar al’ummar ta ƙi shi kuma Allah ya ƙi ta. (Yohanna 1:9-12; Ayukan Manzanni 2:36) Isra’ila ba ta ci gaba da zama mashaidiyar Allah ba, a cikin shekara ta 70 A.Z., aka sake hallaka Urushalima da haikalinta, wannan lokacin sojojin Roma ne suka hallaka ta.—Matta 21:43.
8. Waye ya zama mashaidin Jehovah, kuma me ya sa gargaɗin Bulus ga wannan shaida na kan lokaci ne?
8 A wannan lokacin, an haifi “Isra’ila ta Allah” ta Kirista, kuma wannan yanzu ta zama shaida ta Allah ga dukan Al’ummai. (Galatiyawa 6:16) Shaitan ya yi dabara da sauri ya lalata wannan sabuwar al’umma ta ruhaniya. A ƙarshen ƙarni na farko, rinjayar ɗarikoki ya bayyana a cikin ikklisiyoyi. (Ru’ya ta Yohanna 2:6, 14, 20) Gargaɗin Bulus ya zo akan lokaci: “Ku yi hankali kada kowa shi same ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga ruknai na duniya ba bisa ga Kristi ba.”—Kolossiyawa 2:8.
9. Kamar yadda Bulus ya yi gargaɗi, waɗanne aukuwa ne suka kai ga kasancewar Kiristendom?
9 Daga ƙarshe dai, ussan ilimi na Hellenawa, ra’ayin addinin Babiloniyawa, daga baya kuma irin “hikima” ta mutane kamar su ra’i na haɓaka a hankali da kuma masu sukan ra’ayin Littafi Mai-Tsarki suka gurɓata addinin mutane da yawa da suke da’awar su Kirista ne. Kamar yadda Bulus ya annabta ne: “Na sani bayan tashina kerketai masu-zafin hali za su shiga wurinku, ba za su kewaye ma garke ba; daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (Ayukan Manzanni 20:29, 30) Saboda wannan riddan, Kiristendom ya kasance.
10. Wace aukuwa ce ta nuna sarai cewa ba kowa ba ne ya noƙe ga lalatattun ayyukan sujada ta Kiristendom?
10 Waɗanda suka bada kansu da gaske ga sujada mai tsarki dole ne su yi “yaƙi domin imani, wanda aka bayas ga tsarkaka so ɗaya ɗungum.” (Yahuda 3) Tabbaci na sujada mai tsarki da kuma ga Jehovah za ya ɓace ne daga duniya? A’a. Yayinda lokacin hallaka ɗan tawayen nan Shaitan da dukan ayyukansa take gusowa, ya bayyana cewa ba dukan mutane ba ne suka noƙe ga sujada ta ridda da ake yi cikin Kiristendom. A kusan ƙarshen ƙarni na 19, a Pittsburgh Pennsylvania, U.S.A., an kafa rukunin ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki masu gaskiya kuma ya zama cibiyar ajin shaidun Allah na zamanin yau. Waɗannan Kiristoci sun jawo hankali ga tabbaci na Nassosi cewa ƙarshen tsarin duniya mai ci yanzu ya kusa. Kamar yadda annabcin Littafi Mai-Tsarki ya ce, “cikar zamani” ɗin nan ta fara a shekara ta 1914 kuma ɓarkewan yaƙin duniya na fari ya bayyana hakan. (Matta 24:3, 7) Akwai tabbaci mai ƙarfi cewa Shaitan da taron aljanunsa an jefo su daga sama biye da wannan shekarar. Ƙarni na 20 da ya cika da bala’i ya bada tabbaci sarai na ayyukan Shaitan da kuma cikar alamu na musamman na bayyanuwar Yesu a ikon Mulkin sama.—Matta, surori 24 da 25; Markus, sura 13; Luka, sura 21; Ru’ya ta Yohanna 12:10, 12.
11. Menene Shaitan ya yi ƙoƙarin yi, amma me ya sa ƙoƙarinsa ya kasa?
11 A Yuni 1918, Shaitan a fusace ya yi ƙoƙari ya shafe waɗannan ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki, waɗanda a lokacin suna wa’azi a ƙasashe da yawa. Ya yi ƙoƙari ma ya hallaka rukuninsu da aka ba izini, Watch Tower Bible and Tract Society. Aka tsare manyan ma’aikata na Society a fursuna, aka yi masu tuhumar ƙarya ta tada zaune tsaye, kamar yadda aka yi wa Yesu a ƙarni na farko. (Luka 23:2) Amma a 1919, an sake waɗannan ma’aikata, da ya ba su damar ci gaba da hidimarsu. Daga baya, aka wanke su daga wannan tuhumar.
‘Mai da Hankali Sosai’ ga Yadda Ka Ke Tsaro
12. Su waye suke ajin mai tsaro na Jehovah a yau, ko “masu mai da hankali sosai,” kuma wane hali ne suke da shi?
12 Babu shakka lokacin da “kwanakin ƙarshe” suka fara, Jehovah har yanzu yana da mai tsaro, wanda yana yi wa mutane gargaɗi ga aukuwa waɗanda suke da alaƙa da cikar Ƙudurinsa. (Daniel 12:4; 2 Timothawus 3:1) Har zuwa yau, wannan ajin mai tsaron—shafaffun Kiristoci, Isra’ila ta Allah—suna kan yin aiki daidai da kwatancin mai tsaro na annabcin Ishaya: “Kadan fa ya ga karusar yaƙi, mahaya masu-tafiya biyu biyu, taron jākai, da garken rakumai, sai shi kasa kunne sarai shi lura da kyau. Ya yi ruri kamar zaki, ya ce, Ya Ubangiji, da rana ina nan tsaye tuttur a bisa bene na dako, dare duk kuma ina nan kafe a wurin tsarona.” (Ishaya 21:7, 8) Wannan mai tsaro ne wanda ya ɗauki aikinsa da muhimmanci!
13. (a) Wane saƙo ne mai tsaro na Jehovah ya sanar? (b) Yaya za a iya cewa Babila Babba ta faɗi?
13 Menene wannan mai tsaron ya gani? Har ila yau, mai tsaro na Jehovah, ajin shaidunsa, ya sanar: “Babila ta fāɗi, ta fāɗi: dukan ƙerarrun sifofi na allolinta kuma [Jehovah ya] farfasa su har ƙasa.” (Ishaya 21:9) A wannan ƙaron, bayan Yaƙin Duniya na I, Babila Babba ce, daular addinin ƙarya ta duniya, da ta faɗo daga kujerar ɗaukakarta na iko. (Irmiya 50:1-3; Ru’ya ta Yohanna 14:8) Ba abin mamaki ba ne! Yaƙi Mai Girma, kamar yadda aka kira shi a lokacin, ya fara ne daga Kiristendom, inda limamai na ɓangarori biyu suka ƙarfafa samari masu kyau su je yaƙi. Lallai abin kunya ne! A 1919, Babila Babba ba ta iya ta hana Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki, yadda ake kiran Shaidun Jehovah a lokacin, daga tsira daga yanayinsu na rashin aiki kuma daga ɗaukan aikin wa’azi na dukan duniya wanda ya ci gaba har wa yau. (Matta 24:14) Wannan ya nuna faɗuwar Babila Babba, kamar yadda barin Isra’ila a ƙarni na shida K.Z. ya nuna faɗuwar Babila ta dā.
14. Wace jarida ce ajin mai tsaro na Jehovah ya yi amfani da ita sosai, kuma yaya Jehovah ya albarkaci yin amfani da ita?
14 Ajin mai tsaron kullum yana aikinsa da himma da muraɗi mai ƙarfi na yin abin da yake nagari. A Yuli 1879, Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki suka fara buga wannan jaridar, wanda dā aka sani da Zion’s Watch Tower and Herald of Christ’s Presence. Daga 1879 har zuwa 15 ga Disamba, 1938, kowace fita tana ɗauke da wannan kalmomin a shafinta na farko “ ‘Mai-tsaro, Ina Labarin Dare?’—Ishaya 21:11.”a Hasumiyar Tsaro ta Turanci ya yi tsaro ga aukuwa ta duniya da kuma muhimmancin annabcinsu da aminci na shekara 120. (2 Timothawus 3:1-5, 13) Ajin mai tsaro na Allah da abokanan tarayyarsu “waɗansu tumaki” sun yi amfani da wannan jaridar wajen shela da ƙwazo ga ’yan Adam cewa kunita ikon mallaka na Jehovah ta Mulkin Kristi ya yi kusa. (Yohanna 10:16) Jehovah ya albarkace wannan shaida kuwa? Tun daga fitar farko guda 6,000 a 1879, Hasumiyar Tsaro ta Turanci ta bunƙasa zuwa fiye da 22,000,000 a dukan duniya a harsuna 132—121 cikin waɗannan ana buga su sau biyu a wata. Daidai ne jaridar addini da aka fi bayarwa a duniya, ta zama wadda take ɗaukaka sunan Allah na gaskiya, Jehovah!
Tsabtacewa a Hankali
15. Wace tsabtacewa ta fara a hankali kafin ma 1914?
15 Cikin shekaru 40 har sai da Kristi ya fara Mulkin a sama a 1914, an ’yantar da Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki daga koyarwa da yawa na Kiristendom waɗanda ba na Littafi Mai-Tsarki ba ne, kamar su yi ma jarirai baftisma, kurwa mara mutuwa na ’yan Adam, gidan azaba, azaba a wutar jahannama, da kuma Dunƙulin-Alloli-Uku. Amma ya ɗauki ƙarin lokaci a yi waje da dukan ra’ayi da ba daidai ba. Alal misali, a 1920 da yawa cikin Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki suna saka sarƙa mai ɗauke da alamar giciye, kuma suna bikin Kirsimati da wasu bikin arna. Amma dai, don sujada ta zama a tsarkake, duk wata alama ta bautar gumaka dole a kawar da ita. Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki, dole ta zama ƙashin bayan bangaskiyar Kirista da kuma hanyar rayuwarsa. (Ishaya 8:19, 20; Romawa 15:4) Ba daidai ba ne a ƙara wa Kalmar Allah ko kuma a rage wani abu da ke ciki.—Kubawar Shari’a 4:2; Ru’ya ta Yohanna 22:18, 19.
16, 17. (a) Wace koyarwa ce ajin mai tsaro suka yarda da ita na shekaru da yawa? (b) Wane bayani ne ke daidai na “bagadi” da kuma “umudi” a “Masar”?
16 Wani misali guda zai nuna yadda wannan ƙa’ida take da muhimmanci. A 1886 lokacin da C. T. Russell ya buga wani littafi da aka kira The Divine Plan of the Ages, wannan littafin ya ƙunshi taswira da ya gama tsarararraki na ’yan Adam da Babban Gini na Duwatsu inda ake binne sarakunan Masar. An koyar da cewa wannan abin tuni na Fir’auna Khufu shine umudi wanda Ishaya 19:19, 20 yake nufi: “A cikin ranan nan bagadi za ya kasance ga Ubangiji a tsakiyar ƙasar Masar, da umudi kuma ga Ubangiji a kan iyakatta. Za ya zama alama da shaida kuma ga Ubangiji mai-runduna a cikin ƙasar Masar.” Wane dangantaka ne babban gini na duwatsu inda ake binne sarakunan Masar yake da shi da Littafi Mai-Tsarki? Alal misali, tsawon hanyar da take cikin wannan babban ginin dutse inda ake binne sarakunan Masar an yi tunanin tana nuna lokacin da “ƙunci mai-girma” na cikin Matta 24:21 zai fara ne, kamar yadda aka fahimta a wancan lokacin. Wasu Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki suka duƙufa wajen auna ɓangarori dabam dabam na babban ginin dutse inda ake binne sarakunan Masar don su gano batuttuwa kamar su ranar da za su tafi sama!
17 Shekaru da yawa an ɗaukaka wannan Babban Gini na Duwatsu inda ake binne sarakunan Masar, har sai da Hasumiyar Tsaro ta fitar 15 ga Nuwamba da 1 ga Disamba, 1928 (Turanci), ya bayyana sarai cewa Jehovah ba ya bukatar wani dutse na tuni da fir’auna arna suka gina da ta ƙunshi alamun aljanu na ilimin taurari don ya tabbatar da shaida da aka bayar a cikin Littafi Mai-Tsarki. Maimakon haka, an ga cewa annabcin Ishaya yana da ma’ana ta ruhaniya. Kamar a Ru’ya ta Yohanna 11:8, “Masar” alama ce ta duniyar Shaitan. “Bagadin Ubangiji” ya tunatar mana da aminceccen hadayu da shafaffun Kiristoci suke yi sa’ilin da suke zama na ɗan lokaci cikin wannan duniyar. (Romawa 12:1; Ibraniyawa 13:15, 16) Umudi da yake “a kan iyakatta [Masar]” yana nuna ikklisiya ta shafaffun Kiristoci, wadda ‘umudi ne ta gaskiya da ƙarfinta’ kuma wadda shaida ce ga “Masar,” duniya da suke bakin bari.—1 Timothawus 3:15.
18. (a) Yaya Jehovah ya ci gaba da bayana batuttuwa sarai ga Ɗaliɓan Littafi Mai-Tsarki na gaskiya? (b) Idan Kirista ya iske bayanin Nassosi da wuyan fahimta, wane kyakkyawan hali ya kamata ya nuna?
18 Da shigewar shekaru, Jehovah ya ci gaba da ba mu ƙarin bayyanin gaskiya, haɗe da fahimtar kalmarsa ta annabci sarai. (Misalai 4:18) A shekarun baya bayan nan, an ƙarfafa mu mu sake dubawa da fahimta mai zurfi—a cikinsu da—tsara da ba za ta wuce ba kafin ƙarshe ya zo, almara ta tumaki da awaki, abin ƙyama da kuma lokacin da za ta tsaya a wuri mai tsarki, sabon alkawari, sake kamani, da kuma wahayin haikali na littafin Ezekiel. Wani lokaci zai yi wuya a fahimci waɗannan sabobin bayanai, amma dalilinsu zai bayyana sarai a nan gaba. Idan Kirista bai fahimci sabon bayani na wani nassi ba, yana da kyau ya yi ƙoƙari cikin tawali’u ya maimaita kalmomin Mikah: “Zan jira Allah na cetona.”—Mikah 7:7.
19. Ta yaya shafaffun Kiristoci da abokan tarayyarsu waɗansu tumaki suka nuna gabagaɗi irin na zaki a waɗannan kwanaki na ƙarshe?
19 Ka tuna cewa mai tsaron “ya yi ruri kamar zaki, ya ce, Ya Ubangiji, da rana ina nan tsaye tuttur a bisa bene na dako, dare duk kuma ina nan kafe a wurin tsarona.” (Ishaya 21:8) Ringin shafaffun sun nuna gabagaɗi irin na zaki wajen fallasa addinin ƙarya kuma suna nuna wa mutane hanyar ’yanci. (Ru’ya ta Yohanna 18:2-5) Yadda “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suna tanadar da Littafi Mai-Tsarki, jaridu, da wasu littattafai a harsuna da yawa—‘abinci a lotonsa.’ (Matta 24:45) Suna ja-gaba a tara “taro mai-girma . . . daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” Waɗannan ma an wanke su sarai da jinin Yesu na fansa kuma sun nuna zuciya irin ta zaki wajen yi wa Allah sujada “dare da rana cikin haikalinsa.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, 15) Wane sakamako ne ƙaramin rukunin shafaffu Shaidun Jehovah da abokan aikinsu, taro mai-girma suka samu a wannan shekara da ta shige? Talifinmu na gaba zai yi bayani.
[Hasiya]
a Daga 1 ga Janairu, 1939, an canja wannan zuwa “ ‘Za su kuma sakankance ni ne Ubangiji.’—Ezekiel 35:15.”
Ka Tuna?
• Wane shaidu ne Jehovah ya tada su cikin shekaru na baya baya?
• Menene asalin Babila Babba?
• Me ya sa Jehovah ya ƙyale aka hallaka Urushalima babban birnin al’ummar shaidunsa, a 607 K.Z.? da kuma a 70 A.Z.?
• Wane ruhu ne ajin mai tsaro na Jehovah da abokan tarayyarsu suke nuna?
[Hoto a shafi na 18]
“Ya Ubangiji, da rana ina nan tsaye tuttur a bisa bene na dako”
[Hotuna a shafi na 21]
Ajin mai tsaro na Jehovah sun ɗauki aikinsu da muhimmanci