Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 1/1 pp. 11-16
  • Bari Mu Zama Cikin Waɗanda Suke Da Bangaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Mu Zama Cikin Waɗanda Suke Da Bangaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Nuna Amincewa da Juna
  • Yin Amfani da Ya Dace da Kalmar Allah
  • Kwatanta Misalai na Bangaskiya
  • Yadda Za Mu Yi Ƙarfi a Bangaskiya
  • Ka Dogara ga Jehobah Don Ka Rayu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Nawa Ne Yawan Lokaci Da Ya Rage Ma Miyagu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Yin Murna Cikin Allah Mai Cetonmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 1/1 pp. 11-16

Bari Mu Zama Cikin Waɗanda Suke Da Bangaskiya

“Mu . . . cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.”—IBRANIYAWA 10:39.

1. Me ya sa za a iya cewa bangaskiyar kowanne bawan Jehovah mai-tamani ne?

LOKACIN da ka ke a cikin Majami’ar Mulki da ke cike da masu yin sujada ga Jehovah, ka dakata ka duba waɗanda suka kewaye ka. Ka yi tunanin hanyoyi da yawa da suke nuna bangaskiya. Za ka ga tsofaffi da sun bauta ma Allah na shekaru da yawa, matasa da suke tsayayya ma matsi na tsara kullum, da kuma iyaye da suke ƙoƙari sosai a yin renon yara masu tsoron Allah. Da akwai dattiɓai na ikklisiya da kuma bayi masu hidima, da suke idar da nawaya da yawa. Hakika, za ka ga yan’uwa maza da mata na ruhaniya da shekarunsu dabam dabam da suka fi ƙarfin kowaɗanne abubuwan hani a bauta ma Jehovah. Lallai bangaskiyar kowanne tana da tamani!—1 Bitrus 1:7.

2. Me ya sa gargaɗin Bulus a Ibraniyawa surori 10 da 11 suke da amfani garemu a yau?

2 ’Yan Adam kalilan ne, in ma akwai, da suka gane muhimmancin bangaskiya da kyau fiye da manzo Bulus. Hakika, ya lura cewa bangaskiya tabbataciya tana kaiwa ga “ceton rai.” (Ibraniyawa 10:39) Amma, Bulus ya sani cewa za a faɗā ma bangaskiya kuma a so hallaka ta cikin duniyar nan da ba ta da bangaskiya. Ya damu ƙwarai game da Kiristoci Ibraniyawa a Urushalima da kuma Yahudiya da suke kokawa su tsare bangaskiyarsu. Yayinda muka duba sashe na Ibraniyawa surori 10 da kuma 11, bari mu yi la’akari da hanyoyi da Bulus ya yi amfani da su don ya gina bangaskiyarsu. A yin haka, za mu ga yadda za mu gina bangaskiya mafi ƙarfi cikinmu da kuma waɗanda suka kewaye mu.

Ku Nuna Amincewa da Juna

3. Ta yaya ne kalmomin Bulus da ke a Ibraniyawa 10:39 sun nuna cewa ya amince da yan’uwansa maza da mata a bangaskiya?

3 Abu na farko da za mu iya lura shine hali mai-kyau na Bulus ga masu sauraronsa. Ya rubuta: “Amma mu ba mu cikin masu-noƙewa zuwa hallaka ba; amma cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibraniyawa 10:39) Bulus ya yi tunani mai-kyau, ba mafi muni ba, game da yan’uwansa Kiristoci masu aminci. Ka lura kuma cewa ya yi amfani da furcin nan “mu.” Bulus mutum ne mai-adalci. Duk da haka, bai yi zance da masu sauraronsa da reni ba, sai ka ce duk ya fi su adalci. (Gwada da Mai-Wa’azi 7:16.) Maimako, ya haɗa kansa cikinsu. Ya nuna amincewa da dukan zuciya cewa shi da kuma masu karatunsa Kiristoci masu aminci dukansu za su fuskanci abin sa sanyin gwiwa da ke gabansu, cewa da gabagaɗi za su ƙi noƙewa zuwa hallaka, kuma cewa za su zama cikin waɗanda suke da bangaskiya.

4. Domin waɗanne dalilai ne Bulus ya amince da yan’uwansa masu-bi?

4 Me ya sa Bulus yake da irin amincewar nan? Shin ba ya ganin laifuffukan Kiristoci Ibraniyawa ne? Ba haka ba, ya ba su takamaiman gargaɗi don ya taimake su su sha kan kasawarsu a ruhaniya. (Ibraniyawa 3:12; 5:12-14; 6:4-6; 10:26, 27; 12:5) Har ila yau, Bulus yana da dalilai biyu masu kyau na amincewa da yan’uwansa. (1) Domin shi mai koyi da Jehovah ne, Bulus ya yi ƙoƙarin ya ɗauka mutanen Allah yadda Jehovah yake ɗaukansu. Hakan ba game da laifuffukansu ba kawai amma game da ingancinsu masu kyau da kuma niyar zaɓa yin nagarta a nan gaba. (Zabura 130:3; Afisawa 5:1) (2) Bulus yana da dogara ta gaske cikin ikon ruhu mai-tsarki. Ya sani cewa babu wasu hani, ba kumamanci na ’yan Adam, da zai iya hana Jehovah daga bada “mafificin girman iko” ga kowane Kirista da yake ƙoƙarin ya bauta Masa da aminci. (2 Korinthiyawa 4:7; Filibbiyawa 4:13) Saboda haka, amincewar da Bulus ya nuna ga yan’uwansa maza da mata ba kuskure ba ne, mara tabbaci, ko kuma yana yi ba ji ba gani ba. Kafaffe ne kuma daga Nassi.

5. Ta yaya za mu iya yin koyi da amincewar Bulus, wataƙila da wane sakamako?

5 Babu shakka, amincewar da Bulus ya nuna ya zama abin da ya bazu da wuri ga wasu. Lallai zai zama abu mai girma ga ikklisiyoyin a Urushalima da kuma Yahudiya su ga Bulus ya yi zance na ban ƙarfafa garesu. A fuskar yawan reni da rashin marmari na taurin kai da Yahudawa ’yan hamayya suke da shi, an taimake Kiristoci Ibraniyawa ta wurin irin maganganun nan don su tsai da shawara cikin zukatansu su zama cikin waɗanda suke da bangaskiya. Shin za mu iya yin irin wannan ga juna a yau? Yana da sauƙi mu ga jerin laifuffuka da kuma bambanci cikin wasu. (Matta 7:1-5) Duk da haka, za mu iya taimakon juna sosai idan mun lura kuma muka daraja bangaskiyarsu na musamman da kowanne yake da shi. Tare da irin ƙarfafan nan, yana da sauƙi bangaskiya ta yi girma.—Romawa 1:11, 12.

Yin Amfani da Ya Dace da Kalmar Allah

6. Daga ina ne Bulus ya ɗauko wani furci yayinda ya rubuta kalmomin da ke a Ibraniyawa 10:38?

6 Bulus ya kuma gina bangaskiya cikin yan’uwansa masu-bi ta yin amfani mai kyau da ya yi da Nassosi. Alal misali, ya rubuta: “Amma adilina da bangaskiya za shi rayu: idan kuwa ya noƙe, raina ba shi jin daɗinsa ba.” (Ibraniyawa 10:38) Anan Bulus ya ɗauko abin da annabi Habakkuk ya faɗa ne.a Mai-yiwuwa Kiristoci Ibraniyawa, masu karatun Bulus da sun san littattafan annabcin sosai, sun san furcin nan. A yin la’akari da manufarsa—ya ƙarfafa bangaskiyar Kiristoci a ciki da kuma kusa da Urushalima a misalin shekara ta 61 A.Z.—misalin Habakkuk ne ya fi dacewa. Me ya sa?

7. Yaushe ne Habakkuk ya rubuta annabcinsa, kuma menene yanayin da ke a Yahuda a lokacin?

7 Hakika Habakkuk ya rubuta littafinsa shekara ashirin kafin a hallaka Urushalima a 607 K.Z. A cikin wahayi, annabin ya ga Chaldiyawa (ko kuma, Babiloniyawa), “al’umma mai-zafin rai, mai-garaje,” da ta faɗā farat ɗaya akan Yahuda kuma ta hallaka Urushalima, ta share mutane da kuma al’ummai a garin yin haka. (Habakkuk 1:5-11) Amma an yi annabcin bala’in nan tun kwanakin Ishaya, sama da ƙarni guda da farko. A lokacin Habakkuk, Jehoiakim ya ɗauki matsayin nagarin Sarki Josiah, kuma mugunta ta cika Yahuda. Jehoiakim ya tsananta har ma ya kashe waɗanda suke magana cikin sunan Jehovah. (2 Labarbaru 36:5; Irmiya 22:17; 26:20-24) Ba abin mamaki ba ne da annabi Habakkuk mai-baƙinciki ya yi kuka: “Ya Ubangiji, har yaushe?”—Habakkuk 1:2.

8. Me ya sa misalin Habakkuk yake da ban taimako ga Kiristoci a cikin ƙarni na farko da kuma a yau?

8 Habakkuk bai san yadda hallakar Urushalima take kusa ba. Hakanan ma, Kiristoci na ƙarni na farko ba su san ko yaushe tsarin abubuwa na Yahudawa zai ƙare ba. Ba kuwa mu a yau mun san “ranan da sa’an” da hukuncin Jehovah zai zo bisa mugun tsarin nan ba. (Matta 24:36) To, bari mu lura da amsa ninki biyu da Jehovah ya ba Habakkuk. Na ɗaya, ya tabbatar ma annabin cewa ƙarshen zai zo akan lokaci daidai. “Ba za ta yi jinkiri ba,” in ji Allah, ko da shike a ganin mutane zai zama kamar ya makara. (Habakkuk 2:3) Na biyu, Jehovah ya tunatar da Habakkuk: “Amma adili ta wurin bangaskiyatasa za ya rayu.” (Habakkuk 2:4) Lallai gaskiyar nan tana da kyau kuma da sauƙi! Abu mafi-muhimmanci shine ba lokacin da ƙarshen ya zo ba, amma cewa ko muna ci gaba da rayuwa ta bangaskiya.

9. Ta yaya ne bayi masu biyayya na Jehovah suka rayu da bangaskiyarsu (a) a 607 K.Z.? (b) a 66 A.Z.? (c) Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

9 Lokacin da aka faɗā ma Urushalima a 607 K.Z., Irmiya sakatarensa Baruch, Ebed-melech, da kuma ’ya’yan Rechab masu aminci sun ga gaskiyar alkawarin Jehovah ga Habakkuk. Sun ‘ci gaba da rayuwa’ ta wurin tsira ma mummunar hallakar Urushalima. Me ya sa? Jehovah ya albarkaci amincinsu. (Irmiya 35:1-19; 39:15-18; 43:4-7; 45:1-5) Hakanan ma, Ibraniyawa Kiristoci na ƙarni na farko sun mayar da martani da kyau ga gargaɗin Bulus, domin lokacin da rundunar Romawa suka faɗā ma Urushalima a 66 A.Z. kuma ja da baya babu dalili, waɗancan Kiristoci cikin aminci suka bi gargaɗin Yesu da ya ce su gudu. (Luka 21:20, 21) Sun ci gaba da rayuwa domin bangaskiyarsu. Hakazalika, za mu ci gaba da rayuwa idan an iske mu da bangaskiya lokacin da ƙarshe ya zo. Wannan muhimmiyar dalili ce na ƙarfafa bangaskiyarmu yanzu!

Kwatanta Misalai na Bangaskiya

10. Yaya Bulus ya kwatanta bangaskiyar Musa, kuma ta yaya za mu iya yin koyi da Musa game da haka?

10 Bulus ma ya gina bangaskiya ta wurin yin amfani da misalai masu kyau. Yayinda ka ke karatun Ibraniyawa sura 11, ka lura da yadda ya kwatanta misalan mutane na cikin Littafi Mai-Tsarki. Alal misali, ya ce wai Musa “ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Ibraniyawa 11:27, tafiyar tsutsa tamu ce.) A wata sassa, Jehovah a bayane yake ga Musa har da kamar yana ganin Allah mara ganuwa. Shin za a iya faɗin haka game da mu? Yana da sauƙi a yi zance game da dangantaka da Jehovah, amma a gina kuma ƙarfafa dangantakar nan tana bukatar aiki. Aikin da muke bukatar yi kenan! Shin muna ganin Jehovah sosai har muna la’akari da shi yayinda muke tsai da shawarwari, har da wasu da suke ƙanana ma? Irin bangaskiyar nan zai iya taimakonmu mu jimre ma hamayya mai-tsanani ma.

11, 12. (a) A ƙarƙashin waɗanne yanayi ne aka gwada bangaskiyar Ahnuhu? (b) Wane lada mai kyau ne Ahnuhu ya samu?

11 Ka yi la’akari kuma da bangaskiyar Ahnuhu. Yana da wuya mu iya ƙaga irin hamayyar da ya fuskanta. Dole ne Ahnuhu ya idar da saƙon hukunci mai harbi akan mugayen mutane na lokacin. (Yahuda 14, 15) Tsanantawa da wannan mutum mai aminci ya fuskanta lallai yana da muni, na nuna ƙarfi sosai, har sai da Jehovah ya “ɗauke shi,” ya ɗauke shi daga yanayin rayuwa zuwa barci a mutuwa kafin magabtansa su kama shi. Saboda haka Ahnuhu bai iya ganin cikar annabci da ya yi ba. Amma dai, ya sami kyauta, da a wata hali, mafi kyau ce.—Ibraniyawa 11:5; Farawa 5:22-24.

12 Bulus ya bayyana: “Tun gaban ɗaukassa [Ahnuhu] aka shaida shi mai-game Allah ne sarai.” (Ibraniyawa 11:5) Menene wannan yake nufi? Kafin ya shiga barci na mutuwa, mai-yiwuwa ne Ahnuhu ya shaida wani wahayi, wataƙila na Aljanna a duniya da za a tashe shi ciki wata rana bada daɗewa ba. Ko menene dai, Jehovah ya sanar ma Ahnuhu cewa Ya gamsu da tafarkinsa na aminci. Ahnuhu ya faranta ma Jehovah rai. (Gwada da Misalai 27:11.) Yin tunanin rayuwar Ahnuhu abin tausayi ne, ko ba haka ba? Shin za ka so ka yi irin rayuwar nan ta bangaskiya? Sai ka yi tunani kan irin misalan nan; ka ƙaga su ainihin mutane. Ka ƙuduri aniyar rayuwa da bangaskiya, kowace rana. Ka kuma tuna, cewa waɗanda suke da bangaskiya ba sa bauta ma Jehovah bisa kwanan wata ko kuma wani lokaci da Allah zai cika dukan alkawuransa ba. Maimako, mun tsai da shawarar za mu bauta ma Jehovah har abada! Yin haka yana nufin hanyar rayuwa mafi kyau cikin wannan tsarin abubuwa da kuma a nan gaba.

Yadda Za Mu Yi Ƙarfi a Bangaskiya

13, 14. (a) Ta yaya kalmomin Bulus da ke a Ibraniyawa 10:24, 25 za su taimake mu mu sa taruwanmu ta zama na farinciki? (b) Menene dalili na musamman na taruwan Kirista?

13 Bulus ya nuna ma Kiristoci Ibraniyawa hanyoyi masu amfani da za su iya ƙarfafa bangaskiyarsu. Bari mu bincika biyu kawai. Mai-yiwuwa mun san gargaɗinsa a Ibraniyawa 10:24, 25, ya aririce mu mu taru kullum a wurin taruwanmu na Kirista. Amma, ka tuna cewa hurarren kalmomin Bulus ba wai suna nufin cewa mu zauna kawai babu marmari a wurin irin taruwan nan ba. Maimako, Bulus ya kwatanta taruwan cewa zarafi ne na sanin juna, na motsa juna mu bauta ma Allah sosai, da kuma na ƙarfafa juna. Muna zuwa wurin don mu bayar, ba kawai don mu karɓa ba. Wannan yana sa taruwanmu ya zama lokutta na farinciki.—Ayukan Manzanni 20:35.

14 Amma, muna halartan taruwan Kirista ainihi domin mu bauta ma Jehovah Allah ne. Muna yin haka ta wurin haɗuwa cikin addu’a da waƙa, ta wurin saurara da kyau, da kuma ta wurin bada “ ’ya’yan leɓuna”—furcin yabo ga Jehovah cikin kalaminmu da kuma a wasu sashe na taruwan. (Ibraniyawa 13:15) Idan mun tuna da manufar nan kuma mun yi aiki akansu a kowane taro, babu shakka bangaskiyarmu za ta yi girma kowane lokaci.

15. Me ya sa Bulus ya aririce Kiristoci Ibraniyawa su riƙe hidimarsu, kuma me ya sa gargaɗin ya dace a yau?

15 Wata hanya na gina bangaskiya ita ce ta wurin yin aikin wa’azi. Bulus ya rubuta: “Bari mu riƙe shaidar begenmu da ƙarfi kada ta yi rawa; gama shi mai-aminci ne wanda ya yi alkawari.” (Ibraniyawa 10:23) Kana iya ƙarfafa wasu su riƙe wani abin da kamar zai suɓule daga hannunsu. Hakika Shaitan yana matsa ma waɗancan Kiristoci Ibraniyawa su bar hidimarsu, kuma hakanan yana matsa ma mutanen Allah a yau. A fuskar irin matsin nan, menene ya kamata mu yi? Ka yi la’akari da abin da Bulus ya yi.

16, 17. (a) Ta yaya Bulus ya sami ƙarfin hali don hidima? (b) Waɗanne matakai za mu ɗauka idan muna tsoron wasu fasalolin hidimarmu ta Kirista?

16 Zuwa ga Kiristoci da suke Tassaluniki, Bulus ya rubuta: “Da muka rigaya muka sha wuya, har da wulakanci, yadda kun sani, cikin Filibbi, muka yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah cikin [fama, NW ] mai-yawa.” (1 Tassalunikawa 2:2) Ta yaya ne aka ‘wulakanta’ Bulus da abokan aikinsa a Filibbi? Bisa ga wasu ɗalibai, kalmar Hellenancin da Bulus ya yi amfani da ita anan tana nuna ashar, abin kunya, ko kuma baƙon abu. Masu iko na Filibbi sun bulale su, suka jefa su cikin fursuna, kuma suka tsare su cikin gidan yari. (Ayukan Manzanni 16:16-24) Ta yaya wannan abin da suka fuskanta ya taɓa Bulus? Shin waɗanda suke a birni na gaba cikin tsarin tafiye-tafiyensa, Tassaluniki, sun ga Bulus yana noƙewa cikin tsoro ne? A’a ya yi ‘ƙarfin zuciya.’ Ya sha kan tsoro kuma ci gaba da yin wa’azi da ƙarfin zuciya.

17 Daga ina ƙarfin zuciyar Bulus ya fito? Daga ciki? A’a, ya ce wai ya yi ƙarfin zuciya “cikin Allahnmu.” Wata majiya ta ’yan tarjaman Littafi Mai-Tsarki ta ce wai za a iya sa wannan furcin haka “Allah ya cire tsoro daga zukatanmu.” Saboda haka idan kai musamman ba ka da ƙarfin zuciya game da hidimarka, ko kuma idan akwai wasu fasalolin na musamman da suke ba ka tsoro, me ya sa ba za ka roƙi Jehovah ya ba ka ƙarfin zuciya ba? Ka biɗe shi ya ɗauke tsoro daga zuciyarka. Ka ce ya taimake ka ka yi ƙarfin zuciya don aikin. Ƙari ga haka, ka ɗauki wasu matakai. Alal misali, ka shirya ka yi tafiya da wani da ya inganta ƙwarai cikin fasalin wa’azi da ya shafe ka. Wataƙila yankin kasuwanci ne, wa’azi a tituna, wa’azi na rashin shiri, ko kuma wa’azi a tarho. Wataƙila abokin tafiyarka zai iya so ya soma. Idan haka ne, sai ka lura kuma ka koya. Amma sai ka yi ƙarfin hali don ka gwada shi.

18. Waɗanne albarkatai za mu iya samu idan mun yi ƙarfin hali cikin hidimarmu?

18 Idan ka yi ƙarfin zuciya, ka yi tunanin abin da zai faru. Yayin da ka nace kuma ba ka yi sanyin gwiwa ba, zai yiwu ka sami albarkatai a raɓa gaskiyar, albarkatai da dā ka yi hasararsu. Za ka gamsu da sanin cewa ka yi abin da ke faranta ma Jehovah rai ta yin wani abin da yake maka wuya. Za ka sami albarkatansa da kuma taimako a shan kan abubuwan tsoro gareka. Bangaskiyarka za ta yi ƙarfi. Gaskiya, ba za ka iya gina bangaskiyar wasu ba tare da gina taka bangaskiyar ba.—Yahuda 20, 21.

19. Wane lada mai tamani ne yake a ajiye domin “waɗanda suke da bangaskiya”?

19 Bari ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka da kuma bangaskiyar waɗanda suka kewaye ka. Za ka iya yin haka ta gina kanka da wasu ta wurin gwanin yin amfani da Kalmar Allah, ta yin nazarin misalan cikin Littafi Mai-Tsarki na bangaskiya kuma ƙaga su, ta shirya da kuma yin rabo cikin taruwa ta Kirista, da kuma ta riƙe gata mai tamanin nan na hidimar fage. Yayinda ka ke yin abubuwan nan, ka tabbata cewa da gaske, kana ɗaya “cikin waɗanda su ke da bangaskiya.” Ka tuna kuma, cewa waɗanda suke hakan suna da lada mai tamani. Suna “cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.”b Bari bangaskiyarka ta ci gaba da girma, kuma bari Jehovah Allah ya kiyaye ranka har abada!

[Hasiya]

a Bulus ya ɗauko yadda Septuagint ya juya Habakkuk 2:4, wanda ya haɗa da furcin nan “idan kuwa ya noƙe, raina ba shi jin daɗinsa.” Wannan furcin bai auku cikin wani rubutun hannu na Ibrananci ba. Wasu sun ce wai Septuagint an yi shi ne daga rubutun fari na Ibrananci da babu su kuma. Ko menene dai, Bulus ya haɗa wannan ta wurin tasirin ruhu mai-tsarki na Allah ne. Saboda haka yana da izinin Allah.

b Jigon shekara na Shaidun Jehovah don shekara ta 2000 shine: “Mu ba mu cikin masu-noƙewa . . . amma cikin waɗanda su ke da bangaskiya.”—Ibraniyawa 10:39.

Yaya Za Ka Amsa?

◻ Ta yaya ne Bulus ya nuna amincewa ga Kiristoci Ibraniyawa, kuma menene za mu iya koya daga wannan?

◻ Me ya sa nunin da Bulus ya yi ga annabi Habakkuk ya dace sosai?

◻ Waɗanne misalan Nassi na bangaskiya ne Bulus ya ambata?

◻ Wane hanyar gina bangaskiya ne Bulus ya yaba ma?

[Hoto a shafi na 15]

Bayan wulakanci da aka yi masa a Filibbi, Bulus ya yi ƙarfin hali ya ci gaba da yin wa’azi

[Hotuna a shafi na 16]

Shin za ka iya yin ƙarfin hali a gwada fasalolin wa’azi dabam dabam?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba