Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 9 pp. 29-31
  • Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KU ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH
  • 2 KU JI DAƊIN IBADA TA IYALI
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Mece Ce Bauta ta Iyali?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Ku Sa Ibada ta Iyalinku ta Yi Armashi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • ‘Ka Yi Kusa da Allah, Shi Kuwa Zai Yi Kusa da Kai’
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 9 pp. 29-31
Ma’aurata suna yin nazarinsu na Littafi Mai Tsarki tare

SASHE NA 9

Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali

“Ku yi sujada ga wanda ya yi sama da duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 14:7

Kamar yadda kuka koya a wannan ƙasidar, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari da yawa da za su taimaka wa ku da iyalinku. Jehobah yana so ku zauna lafiya. Ya yi alkawari cewa idan kuka ba wa ibadarsa fifiko a rayuwarku, sauran “waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku.” (Matta 6:33) Allah yana so ku ƙulla abota da shi. Saboda haka, ku yi iyakacin ƙoƙarinku ku ƙarfafa dangantakarku da Allah. Babu gatan da ya kai wannan a rayuwar ɗan Adam.​—Matta 22:37, 38.

1 KU ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH

Mata da miji suna wa’azi tare

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Zan zama Uba gare ku, ku za ku zama ’ya’ya maza da mata gare ni, in ji Ubangiji.’ (2 Korintiyawa 6:18) Allah yana so ku zama abokansa na kud da kud. Addu’a tana ɗaya daga cikin hanyoyin yin hakan. Jehobah yana so ku riƙa yin “addu’a ba fasawa.” (1 Tasalonikawa 5:17) Yana ɗokin jin abin da ke cikin zuciyarku. (Filibiyawa 4:6) Idan ka yi addu’a tare da iyalinka, za su ga cewa ka gaskata da Allah sosai.

Ƙari ga yin addu’a ga Allah, kuna bukatar ku saurare shi. Za ku iya yin hakan ta wajen karanta Kalmarsa da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. (Zabura 1:1, 2) Ku yi bimbini a kan abubuwan da kuka koya. (Zabura 77:11, 12) Kuna bukatar ku riƙa halartan taron Kirista idan kuna so ku saurari Allah.—Zabura 122:1-4.

Yin wa’azi ma zai taimaka muku ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Idan kuna yin hakan a kai a kai, za ku kusaci Jehobah sosai.​—Matta 28:19, 20.

SHAWARA:

  • Ku keɓe lokaci don yin addu’a da kuma karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana

  • A matsayin iyali, ku ɗauki ibada da muhimmanci fiye da nishaɗi da shaƙatawa

2 KU JI DAƊIN IBADA TA IYALI

Baba yana nazari wato shirin don su ji dadin ibadarsu ta iyali da za su yi

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙub 4:8) Kuna bukatar ku tsara yadda za ku yi ibada ta iyali* kuma ku riƙa bin wannan tsarin. (Farawa 18:19) Ƙari ga hakan, wajibi ne ku yi nufin Allah a kowace rana. Ku ƙarfafa dangantakar iyalinku da Allah ta wajen tattaunawa game da shi “sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Ku ƙudurta cewa za ku bi misalin Joshua, wanda ya ce: “Da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”​—Joshua 24:15.

SHAWARA:

  • Ku kasance da tsarin ibada ta iyali da zai shafi bukatun kowa a iyalinku

Mama tana wa danta karatu; iyali suna kwaikwayon labarin wani daga Littafi Mai Tsarki; baba yana yin nazari da ’yarsa

BAYIN JEHOBAH MASU ZAMAN LAFIYA

Babu abin da ya fi bauta wa Jehobah muhimmanci. Jehobah yana farin cikin ganin yadda ku da iyalinku kuke yi masa ibada da gaske. Idan kuka ci gaba da bauta wa Jehobah, za ku ƙaunace shi kuma ku yi koyi da shi a koyaushe. (Markus 12:30; Afisawa 5:1) Idan kuna bin ja-gorancin Allah, hakan zai sa kai da matarka ku kusaci juna sosai. (Mai-Wa’azi 4:12; Ishaya 48:17) Ku da iyalinku za ku ci gaba da zama lafiya har abada, domin “Ubangiji Allahnku ya albarkace ku.”​—Kubawar Shari’a 12:7.

KA TAMBAYI KANKA . . .

  • Yaushe rabona da yin addu’a da matata?

  • Mene ne zan tattauna da iyalina da zai ƙarfafa bangaskiyarmu?

SHAWARA GA UBANNI

  • Kada ku bar wani abu ya hana ku yin ibada ta iyali

  • Kafin ranar ibada ta iyali, ku sanar da iyalinku abin da za ku tattauna don su shirya

  • Ku tabbata cewa kowa a iyalin yana nan

  • Ku sa yanayin ya kasance yadda kowa zai ji daɗin ibadar

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba