Hagu: Taron da aka yi a fili a Landan, Ingila, a 1945; dama: Ranar taro na musamman a Malawi, Afirka a 2012
SASHE NA 5
Ilmantarwa Game Da Mulkin—Koyar da Bayin Sarkin
A CE ka halarci wani babban taro, kuma wani ɗan’uwa matashi daga ikilisiyarku yana ba da jawabinsa na farko a babban taron. Yayin da kake jin daɗin jawabin da yake yi, zuciyarka ta cika da mamakin yadda Allah yake koyar da mutanensa. Ka tuna da jawabinsa na farko a Majami’ar Mulkinku, kuma ga shi yanzu ya zama ƙwararre! Ya samu wannan koyarwar ce a Makarantar Hidima ta Allah da Makarantar Hidima ta Majagaba, kuma shi da matarsa ba su daɗe da halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki ba. Yayin da kake tafawa bayan ɗan’uwan ya kammala jawabinsa mai daɗi, sai ka soma tunanin irin koyarwar da bayin Allah da suka halarci taron suka samu.
Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da lokacin da Jehobah zai koyar da mutanensa. (Isha. 54:13) Muna raye ne a wannan lokacin. Muna samun koyarwa ta hanyar littattafanmu da taron ikilisiya da manyan taro da kuma makarantu dabam-dabam da aka tsara don su taimaka mana mu ƙware wajen gudanar da ayyuka a ƙungiyar Jehobah. A wannan sashen, za mu tattauna yadda waɗannan koyarwar suke ba da tabbaci cewa Mulkin Allah yana sarauta a yau.