SASHE NA 13
Cikakken Imani Yana Kai ga Farin Ciki na Har Abada
“WANDA yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu,” in ji Nassosi Masu Tsarki. (Romawa 1:17) Waɗannan kalaman suna ɗauke da alkawari mai ban sha’awa da ya shafe ka. A waɗanne hanyoyi?
Bayan ya kammala aikinsa a duniya, Yesu Almasihu, ya koma sama don ya kasance tare da Allah. Yayin da almajiransa suke cikin dubawa, “aka ɗauke shi bisa; girgije ya karɓe shi har ya ɓace wa ganinsu.” (Ayyukan Manzanni 1:9) A sama, Allah ya naɗa shi a matsayin Sarki mai girma na samaniya. A nan gaba kaɗan, Yesu, “Ɗan mutum” zai zo “cikin darajassa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajassa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi ya kan rarraba tumaki da awaki.” (Matta 25:31, 32) A wane lokaci ne hakan zai faru?
Nassosi Masu Tsarki sun annabta lokacin da dukan duniya za ta fuskanci masifa, kuma hakan zai zama alamar cewa hukuncin da Almasihun zai yi wa al’ummai ya kusa. Yesu ya bayyana abin da alamar ta ƙunsa: “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki: za a yi manyan rayerayen duniya, wurare dabam dabam kuma yunwa da aloba; da al’amura masu-ban tsoro.”—Luka 21:7, 10, 11.
Matsaloli da ake gani a yau sun nuna cewa Almasihu zai hukunta al’ummai nan ba da daɗewa ba
A yau, muna ganin yadda kalaman Yesu suke cika dalla-dalla. Ba da daɗewa ba, Yesu zai zo ya halaka mugaye. A ƙarshe, za a halaka Shaiɗan! Duniya za ta zama aljanna. Dukan mutane har da dabbobi za su zauna lafiya da juna. “Kerkeci za ya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayayyen ɗan sā za su zauna wuri ɗaya; ɗan yaro kuwa za ya bishe su. Ba za su yi ciwutaswa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba.” (Ishaya 11:6, 9) “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba. . . . Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe.” (Ishaya 33:24; 35:5) Su ma matattu za su tashi. “Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki,” kuma “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba. (Ishaya 25:8; Ru’ya ta Yohanna 21:4) A wannan lokacin nufin Allah na ainihi ga duniya zai tabbata. Lallai wannan bege ne mai kyau!
Ka Ci Gaba da Kyautata Imaninka
Waɗanne irin mutane ne Allah zai sāka masu da ladar yin rayuwa a duniya? Mutane masu imani, wato, cikakken imani.
Ka tuna cewa cikakken imani ya dangana ne ga samun cikakken sani na Kalmar Allah. Saboda haka, ka ci gaba ƙoƙartawa don samun sanin Allah da kuma Yesu!
Mutane masu imani za su more Aljanna har abada!
Cikakken imani yana tattare ne da nagargarun ayyuka. Kalmar Allah ta ce: “Bangaskiya ba tare da ayyuka mataciya ce.” (Yaƙub 2:26) Ta wajen yin irin waɗannan ayyukan nagari, za ka nuna halaye masu kyau na Allah, wato, iko, adalci, hikima, da ƙauna. Ka ci gaba da koyon waɗannan halaye masu kyau!
Kasancewa da cikakken imani zai albarkace ka sosai. Hakika, zai sa ka yi farin ciki a rayuwa, a yanzu da kuma har abada!