Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rk sashe na 2 pp. 4-5
  • Mene ne Cikakken Imani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Cikakken Imani?
  • Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Za Ka Iya Samun Cikakken Imani?
  • Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Bangaskiya​—Tana Sa Mu Kasance da Karfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • An Fallasa Makiyin Imani
    Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
Dubi Ƙari
Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
rk sashe na 2 pp. 4-5

SASHE NA 2

Mene ne Cikakken Imani?

Wani mutum ya rike kudi yana kallo

Kamar kuɗi, ya kamata imani ya zama na ainihi idan ana so ya kasance da tamani

KASANCEWA da cikakken imani ya wuce gaskata cewa akwai Allah kawai. Akwai miliyoyin mutane da suka yarda cewa akwai Allah amma duk da haka suna yin miyagun ayyuka da gangan. Irin wannan “imanin” yana kama ne da jabun kuɗi. Ya yi kama da na gaske amma na banza ne. Amma, mene ne cikakken imani?

Cikakken imani ya dogara ne ga cikakken sani na Nassosi Masu Tsarki. Waɗannan hurarrun kalaman sun gaya mana gaskiya game da Allah kuma sun taimaka mana mu san shi. Sun bayyana dokokinsa, manufofinsa, da koyarwarsa. Waɗannan koyarwar sun haɗa da:

  • Allah ɗaya ne. Ba shi da na biyu.

  • Yesu (Isah) ba Allah Maɗaukaki ba ne. Shi annabin Allah ne.

  • Allah ya haramta kowanne irin bautar gumaka.

  • Ranar da za a hukunta ’yan Adam tana tafe.

  • Matattu masu ɗimbin yawa za su tashi daga matattu su shiga Aljanna.

Cikakken imani yana motsa mu mu yi ayyuka masu kyau. Irin waɗannan ayyukan suna daraja Allah kuma suna sa mu da wasu mu amfana. Waɗannan ayyuka masu kyau sun ƙunshi abubuwan nan kamar

  • bauta wa Allah.

  • kasancewa da halayen da Allah yake so, musamman ƙauna.

  • yin watsi da tunani da kuma muradi marar kyau.

  • kasancewa da imani ga Allah duk da matsaloli.

  • koya wa wasu game da Allah.

Wata iyali ta kawo ma wata tsohuwa abinci

Cikakken imani yana haifar da ayyuka masu kyau

Ta Yaya Za Ka Iya Samun Cikakken Imani?

Wani mutum yana watsa jiki don ya karfafa jijiyoyin jikinsa

Imani, kamar jijiyar ƙarfi yake, yana ƙara girma idan ana amfani da shi

Ka roƙi Allah ya taimaka maka. Annabi Musa ya yi addu’a ga Allah: “Ka koya mani tafarkunka, don in san ka, domin in sami tagomashi a gare ka.”a Allah ya ji addu’arsa kuma ya amsa ta. Musa ya zama fitaccen misali na mutum mai imani. Allah zai kuma taimaka maka ka samu cikakken imani.

Ka keɓe lokaci don yin nazarin Nassosi Masu Tsarki. Za a iya samun hurarrun Nassosi, har da Attaura, Zabura, da Linjila, a cikin Littafi Mai Tsarki, littafin da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a duniya. Shin kana da waɗannan hurarrun rubutun kuwa?

Ka yi amfani da shawarar da ke cikin Rubutu Masu Tsarki a rayuwarka ta yau da kullum. Imani, kamar tsoka yake, yana ƙara girma idan ana amfani da shi. Yayin da kake amfani da imaninka, shi ma zai yi girma. Za ka ga cewa shawarar Allah tana da amfani. Hakika, shawara mai amfani da ke cikin Nassosi Masu Tsarki ta kyautata rayukan mutane da yawa. Ka ci gaba da wannan karatun don ka ga wasu misalai.

a Attaura, Fitowa 33:13.

Yaya Za Ka Amsa?

  • Cikakken imani ya dogara ne ga me?

  • Cikakken imani yana sa a yi waɗanne ayyuka masu kyau?

  • Ta yaya za ka iya samun cikakken imani?

Allah Ya Kāre Kalmarsa

Muna da tabbaci cewa Allah ya adana Nassosi Masu Tsarki su kasance tsarkakke don amfaninmu a yau. Allah Maɗaukaki zai iya kāre littafinsa. Kalmarsa ta ce: “Ciyawa ta kan yi yaushi, fure shi yanƙwane, amma maganar Ubangiji za ta tsaya har abada.”—Ishaya 40:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba