‘Lokacin Hukunci’ Ya yi
WAHAYIN YAHAYA, littafi na ƙarshe cikin Littafi Mai Tsarki ya faɗakar da mu cewa mala’ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama yana da “madawwamiyar bishara domin ya sanar.” Da babbar murya ya ce: “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi.” (Wahayin Yahaya 14:6, 7) Wannan ‘lokacin hukunci’ ya haɗa da sanarwa da kuma zartar da hukunci ne na Allah. Zartar da hukuncin, ƙarewar “zamanin ƙarshe” ne da muke ciki yanzu.—2 Timoti 3:1.
Lokacin ‘hukunci’ albishir ne ga masu ƙaunar adalci. Lokaci ne da Allah zai kawo sauƙi wa bayinsa da suke shan wahala cikin mugun zamanin nan cike da mugunta, marar ƙauna.
Yanzu kafin ‘lokacin hukunci’ ya ƙare, za a halaka mugun zamanin nan, an aririce mu: ‘Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi.’ Kana yin haka kuwa? Wannan ya wuci kawai a ce, “na gaskata da Allah.” (Matiyu 7:21-23; Yakubu 2:19, 20) Tsoron da ya dace ga Allah ya kamata ya sa mu ɗaukaka shi. Ya kamata ya sa mu bar mugunta. (Karin Magana 8:13) Ya kamata ya taimake mu mu ƙaunaci nagarta kuma mu ƙi mugunta. (Amos 5:14, 15) Idan muna girmama Allah, za mu saurare shi da ladabi ƙwarai. Ba za mu taƙure da wasu abubuwa mu kasa karatun Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki a kai a kai ba. Za mu dogara gare shi kullum mu yi hakan da zuciya ɗaya. (Zabura 62:8; Karin Magana 3:5, 6) Waɗanda suke girmama shi da gaske sun fahimci shi Mahaliccin sama ne da duniya, Mai Ikon Mallakar Dukan Sararin Halitta, kuma suna yi masa biyayya domin shi ne wanda yake da Iko a kan rayukanmu. Idan muka fahimci cewa muna bukatar mu daɗa mai da hankali ga waɗannan batu, bari mu yi hakan babu ɓata lokaci.
Lokacin zartar da hukunci da mala’ikan ya yi maganarsa “ranar Ubangiji” ce. “Ranar” nan ta zo kan Urushalima a shekara ta 607 K.Z., saboda mazaunanta ba su saurari gargaɗin Jehovah ta wurin annabawansa ba. Domin a zukatansu sun ce ranar Jehovah tana nan gaba tukuna, sun daɗa sa rayukansu cikin haɗari. Jehovah ya faɗakar da su: “Ta gabato, tana gabatowa da sauri.” (Zafaniya 1:14) Wata “ranar Ubangiji” kuma ta zo kan Babila ta dā a shekara ta 539 K.Z. (Ishaya 13:1, 6) Domin sun dogara ga garun birnin da kuma allolinsu, Babiloniyawa suka yi banza da gargaɗin da annabawan Jehovah suka bayar. Amma a dare ɗaya Babila Babba ta fāɗa hannun Mediya da Farisa.
Menene muke fuskanta a yau? Wata “ranar Ubangiji” ce mai girma. (2 Bitrus 3:11-14) An sanar da hukuncin Allah a kan “Babila Babba.” A Wahayin Yahaya 14:8, wani mala’ika ya sanar: “Babila mai girma ta fāɗi.” Wannan ya riga ya faru. Ba ta da ikon da za ta tsare masu bauta wa Jehovah ba. An fallasa ɓatancinta sosai, da kuma sa hannunta cikin yaƙi. Ga shi halaka ta ƙarshe a kanta ta yi kusa. Domin wannan, Littafi Mai Tsarki ya aririce mutane a ko’ina cewa: “Ku fito daga cikinta [Babila mai girma], . . . Kada zunubanta su shafe ku, kada bala’inta ya taɓa ku. Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama, Allah kuwa ya tuna da laifofinta.”—Wahayin Yahaya 18:4, 5.
Mecece Babila Mai Girma? Tsarin addini ne na dukan duniya da yake da irin halayen Babila ta dā. (Wahayin Yahaya, surori 17, 18) Ka yi la’akari da wasu kamanninta:
• Firistocin Babila ta dā sun shaƙu sarai da harkokin siyasa ta al’ummar. Yadda yake ke nan da yawancin addinai a yau.
• Firistocin Babila ne suke gabatar da yaƙe-yaƙen al’ummar. Sau da yawa addinai na zamani ne suke ja-gora a amince da sojoji sa’ad da za su yi yaƙi.
• Koyarwa da kuma ayyuka na Babila ta dā ne ya sa al’ummar take mugun lalata. Sa’ad da shugabannin addinai a yau suka yi banza da mizanan Littafi Mai Tsarki, ana ganin lalata sosai tsakanin limamai da kuma ’yan zauna ku ji. Abin lura kuma shi ne cewa Babila Mai Girma tana karuwanci da duniya da kuma tsarinta na siyasa, yadda Wahayin Yahaya ya nuna ita karuwa ce.
• Littafi Mai Tsarki kuma ya ce Babila Babba tana “almubazzaranci.” A Babila ta dā, ƙungiya ta haikali suna da filaye sosai, kuma firistocin ne suke kasuwanci sosai da filayen. Ban da wuraren sujada, Babila Babba tana da filaye masu yawa na kasuwanci. Koyarwarta da kuma ranakun hutu da take da su suna kawo mata arziki kuma wasu ma suna samun arziki a tsarin kasuwancinta.
• Ana amfani da sifofi, dabo, da maita a Babila ta dā yadda yake a wurare da yawa a yau. Ana ɗaukan mutuwa cewa tafiya ce zuwa wata rayuwa. Babila tana cike da haikalai da ƙungiyoyi na ɗaukaka allolinta, amma mutanen Babila suna adawa da masu bauta wa Jehovah. Waɗannan imani da ayyuka ne a yau suke nuna wadda Babila Babba take.
A zamanin dā, Jehovah ya sa al’ummai masu girma na siyasa da suke da sojoji su yi wa waɗanda suka ci gaba da rena shi da kuma nufinsa horo. Saboda haka, Assuriyawa suka halaka Samariya a shekara ta 740 K.Z. Mutanen Babila suka halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., kuma Romawa suka halaka ta a shekara ta 70 A.Z. Sai kuma ’yan Mediya da Farisa suka halaka Babila a shekara ta 539 K.Z. Littafi Mai Tsarki ya annabta game da zamaninmu cewa gwamnati ta siyasa, kamar dabba, za ta kai wa “karuwan” farmaki kuma za ta mai da ita tsirara, ta fallasa ainihin halinta. Za ta halaka ta sarai sarai.—Wahayin Yahaya 17:16.
Gwamnatin duniya za ta yi haka da gaske? Littafi Mai Tsarki ya ce ‘Allah ya nufe su su yi nufinsa.’ (Wahayin Yahaya 17:17) Zai kasance farat ɗaya ne, na ban mamaki, na ban girgiza, da ba za a ga shirinsa ba ko kuma ba a hankali ba ne.
Me kake bukatar ka yi? Ka tambayi kanka: ‘Ina manne wa ƙungiyar addini da koyarwarta da kuma ayyuka da suke nuna ta sashen Babila Babba ne?’ Ko idan ba ka cikinsu, kana iya tambayar kanka: ‘Na yarda tasirinta ya rinjaye ni ne?’ Wane irin tasiri ke nan? Tasirin amince da rashin ɗabi’a, son abin duniya da annashuwa maimakon ƙauna ga Allah, ko kuwa reni da gangan (har ma a abubuwan da kamar ƙanana ne) na Kalmar Jehovah. Ka yi tunanin amsarka.
Domin mu sami amincewar Jehovah, yana da muhimmanci mu nuna ta wurin ayyukanmu da burin zuciyarmu cewa da gaske mu ba na Babila Babba ba ne. Lokaci ya ƙure. Da Littafi Mai Tsarki yake yi mana gargaɗi cewa ƙarshen zai zo farat ɗaya ne, ya ce: “Za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.”—Wahayin Yahaya 18:21.
Amma bai ƙare ba. Wani fasalin ‘lokacin hukuncin’ kuma shi ne cewa Jehovah Allah zai shar’anta tsarin siyasa na duniya, masu sarautarta, da kuma dukan waɗanda suka yi banza da ikonsa na sarauta ta wurin Mulkinsa na samaniya a hannun Yesu Kristi. (Wahayin Yahaya 13:1, 2; 19:19-21) Wahayin da aka rubuta a Daniyel 2:20-45 ya nuna sarautar siyasa daga lokacin Babila ta dā zuwa yanzu da sifar zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, da kuma yumɓu ke wakiltawa. Annabcin ya ce game da zamaninmu: “Allah na Sama zai kafa wani Mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada.” Game da abin da wannan Mulkin zai yi har ila cikin ‘lokacin hukuncin’ Jehovah, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki [na mutane], ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.”—Daniyel 2:44.
Littafi Mai Tsarki ya yi wa masu bauta ta gaskiya gargaɗi kada su ƙaunaci “abin da ke cikin [duniya],” watau, yayin rayuwa da duniya wadda take a ware daga Allah na gaskiya take gabatar da shi. (1 Yahaya 2:15-17) Shawarwarinka da ayyukanka suna nuna kana goyon bayan Mulkin Allah sarai kuwa? Ka sa shi farko a rayuwarka kuwa?—Matiyu 6:33; Yahaya 17:16, 17.
[Akwati a shafi na 14]
Yaushe Ƙarshen Zai Zo?
“A lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”—Matiyu 24:44.
“Sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa’ar.”—Matiyu 25:13.
“Ba zai makara ba.”—Habakuk 2:3.
[Akwati a shafi na 14]
Idan Ka San Ranar Ayyukanka Za Su Bambanta Ne?
Idan ka sani cewa hukuncin Allah mai zuwa ba zai zo ba nan da ’yan shekaru, wannan zai canja yadda kake rayuwarka ne? Idan ƙarshen wannan tsohon zamani ya daɗe fiye da yadda kake tsammani, za ka ƙyale wannan ya sa ka rage gaggawarka cikin hidimar Jehovah?—Ibraniyawa 10:36-38.
Yadda ba mu san ranar ba yana ba mu zarafin nuna cewa muna bauta wa Allah da buri mai kyau. Waɗanda suka san Jehovah sun sani cewa kasancewa da himma ta farat ɗaya kafin ƙarshe ba za ta burge Allah ba, shi da ya san zuciya.—Irmiya 17:10; Ibraniyawa 4:13.
Waɗanda suke ƙaunar Jehovah da gaske suna sa shi farko a rayuwarsu. Yadda sauran mutane suke, Kiristoci na gaskiya su ma suna aikin albashi. Amma ba domin su yi arziki ba ne ko su samu isashen abin duniya da kuma ɗan ƙari da za su rarraba ba. (Afisawa 4:28; 1 Timoti 6:7-12) Su ma suna morar nishatsi mai kyau da yin wani abu dabam, amma dalilin wannan domin su sami wartsakewa ne ba kawai su yi abin da wasu suke yi ba. (Markus 6:31; Romawa 12:2) Suna farin ciki su yi nufin Allah yadda Yesu Kristi ya yi.—Zabura 37:4; 40:8.
Kiristoci na gaskiya suna son su rayu kuma su bauta wa Jehovah har abada. Begen da suke da shi yana da muhimmanci domin za su jira wata albarka fiye da yadda wasu suke tsammani.
[Akwati/Hoto a shafi na 15]
Batun Ikon Mallaka
Domin mu fahimci abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala haka, muna bukatar mu fahimci batun ikon mallaka. Menene ikon mallaka? Fificin iko ne.
Saboda Jehovah shi ne Mahalicci, yana da ikon ya yi sarautar duniya da dukan abin da ke cikinta. Amma, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa da farko cikin tarihin ’yan Adam, an zargi ikon mallaka na Jehovah. Shaiɗan Iblis ya yi da’awar cewa Jehovah matsananci ne, cewa Ya yi wa iyayenmu na farko ƙarya game da abin da zai faru idan suka yi banza da dokar Allah kuma su yi abubuwa yadda suke so, kuma cewa zai fi musu albarka idan suka mallaki kansu suka ƙyale Allah.—Farawa, surori 2, 3.
Da Allah ya halakar da waɗannan ’yan tawayen nan da nan zai nuna ikonsa, amma ba zai warware batun da aka tayar ba. Maimakon ya halakar da ’yan tawayen nan da nan, Jehovah ya ƙyale dukan halittu masu basira su ga sakamakon tawaye. Ko da yake wannan ya haɗa da wahala, ya ba da zarafin a haife mu.
Bugu da ƙari, ya kasance da zafi ƙwarai gare shi, Jehovah cikin ƙauna ya yi tanadin da mutanen da suka yi masa biyayya kuma suke da bangaskiya a hadayar fansar Ɗansa za su iya samun ’yanci daga zunubi da sakamakonsa kuma su rayu a Aljanna. Idan bukata ta kama, zai zama ta wurin tashin matattu.
Yadda aka ba da lokaci don a warware batun ya ba bayin Allah zarafin su nuna cewa sun yarda da ƙaunar Allah kuma suna nuna amincinsu ga Jehovah a kowane irin yanayi. Warware batun ikon mallaka na Allah, tare da wasu batun amincin mutane yana da muhimmanci don a yi ladabi da ya dace da doka cikin dukan sararin samaniya. Idan ba haka ba, ba za a taɓa samun salama ta gaskiya ba.a
[Hasiya]
a An tattauna waɗannan batutuwa da nufinsu sosai cikin littafin nan Ka Kusaci Jehovah, da Shaidun Jehovah suka buga.
[Hoto]
Tsarin siyasa na sarautar duniya zai kai ƙarshensa