Sabuwar Duniya Bisa Ga Alkawarin Allah
RUBUTACCIYAR Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ta ba mu bege sa’ad da ta ce: “Bisa ga alkawarinsa, muna jiran sababbin sammai da sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zamansa.”—2 Bitrus 3:13.
Menene “sababbin sammai”? Littafi Mai Tsarki ya yi zancen sammai tare da sarauta. (Ayyukan Manzanni 7:49) “Sababbin sammai” sabuwar gwamnati ce da za ta yi sarauta bisa duniya. Sabuwa ce domin za ta ɗauki matsayin tsarin sarauta na zamanin nan; sabuwar aba ce a cika ƙudurin Allah. Mulki ne wanda Yesu ya koya mana yadda za mu yi addu’a dominsa. (Matiyu 6:10) Da yake Allah ne Tushensa kuma wurin zamansa sama ne ya sa aka kira shi “Mulkin Sama.”—Matiyu 7:21.
Mecece “sabuwar ƙasa”? Ba sabon kwallon duniya ba ne domin Littafi Mai Tsarki ya faɗa sarai cewa za a zauna a duniya har abada. “Sabuwar ƙasa” sabuwar jam’iyyar mutane ce. Sabuwa ce domin za a datse miyagu daga cikinta. (Karin Magana 2:21, 22) Dukan waɗanda suke rayuwa a lokacin za su ɗaukaka kuma su yi biyayya da Mahalicci kuma su yi rayuwa da ta jitu da farillansa. (Zabura 22:27) Ana gayyatar mutane yanzu daga dukan al’ummai su koyi waɗannan farillai kuma su yi rayuwa da ta jitu da su. Kana yin haka kuwa?
A cikin sabuwar duniya ta Allah, kowa zai yi biyayya da Sarautarsa. Ƙauna ga Allah yana motsa ka ka yi biyayya gare shi? (1 Yahaya 5:3) Wannan haka yake a gidanka? a wurin aikinka ko a makaranta? haka kake rayuwarka?
A cikin wannan sabuwar duniyar, mutane za su haɗa kai wajen bauta wa Allah na gaskiya. Kana bauta wa Mahaliccin sama da duniya kuwa? Bauta da kake yi tana haɗa ka da ’yan’uwa masu bauta daga dukan al’ummai, dukan ƙabilai, da kuma harsuna?—Zabura 86:9, 10; Ishaya 2:2-4; Zafaniya 3:9.
[Akwati a shafi na 17]
Allahn da Ya Yi Alkawarin Waɗannan Abubuwa
Shi ne Mahaliccin sammai da Duniya na zahiri. Shi ne wanda Yesu Kristi ya kira “Allah Makaɗaici na gaskiya.”—Yahaya 17:3.
Yawancin mutane suna ɗaukaka allahn da su suke yi ne. Miliyoyi suna bauta wa wasu sifofi. Wasu suna ɗaukaka ƙungiyoyin mutane, abin duniya, ussan ilimi, ko burin kansu. Har waɗanda suke da’awar suna amfani da Littafi Mai Tsarki ma ba sa ɗaukaka sunan wannan da ake ce da shi ‘Allah na gaskiya.’—Maimaitawar Shari’a 4:35.
Littafi Mai Tsarki ya ce game da Mahalicci: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne.” (Zabura 83:18, Litafi Mai-Tsarki.) Wannan sunan ya bayana fiye da sau 7,000 cikin Littafi Mai Tsarki cikin harsunansa na asali. Yesu Kristi ya koya wa mabiyansa su yi addu’a haka: “Ya Ubanmu wanda ke cikin Sama, a kiyaye sunanka da tsarki.”—Matiyu 6:9.
Waɗanne ne halayen Allah na gaskiya? Ya bayyana kansa “mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya” kuma wanda ba ya ƙin yin horo ga waɗanda suka taka dokokinsa da gangan ba. (Fitowa 34:6, 7) Tarihin yadda ya bi da mutane yana tabbatar da wannan kwatanci.
Ya kamata a tsarkake sunan da mai sunan ko a bi da su da tsarki. Da yake shi Mahalicci ne kuma Mamallakin Sararin Samaniya ne, ya cancanci mu yi masa biyayya mu yi masa sujada. Kai kana yin haka gare shi kuwa?
[Akwati/Hoto a shafi na 18]
Waɗanne Canje-Canje Za Su Auku Domin “Sababbin Sammai da Sabuwar Ƙasa”?
Duniya ta zama Aljanna Luka 23:43
Mutane daga dukan al’ummai, Yahaya 13:35;
dukan ƙabilu, da dukan harsuna suna Yahaya 7:9, 10
haɗa kai cikin ƙauna Wahayin
Salama ta dukan duniya, kwanciyar Zabura 37:10, 11;
rai ta gaske ga kowa Mika 4:3, 4
Aiki mai gamsarwa, yalwan abinci Ishaya 25:6; 65:17, 21-23
Za a kawar da ciwo, baƙin ciki, Ishaya 25:8;
da mutuwa Wahayin Yahaya 21:1, 4
Duniya da take haɗa kai a bauta wa Wahayin Yahaya 15:3, 4
Allah na gaskiya
[Akwati/Hotuna a shafi na 19]
Za Ka Amfana Kuwa?
Allah ba ya ƙarya!—Titus 1:2.
Jehovah ya ce: “Maganar da na faɗa . . . ba ta kāsa cika abin da na shirya mata, za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.”—Ishaya 55:11.
Jehovah ya riga ya soma halittar “sababbin sammai da sabuwar ƙasa.” Gwamnati ta samaniya ta riga ta fara aiki. An riga an kafa tushen “sabuwar ƙasa.”
Bayan ya ambata wasu manyan abubuwan da “sababbin sammai da sabuwar ƙasa” za ta kawo wa mutane, Wahayin Yahaya ya ɗauko abin da Allah kansa ya faɗa, shi Mamallakin Dukan Sararin Samaniya, cewa: “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce: “Rubuta wannan, domin maganan nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.”—Wahayin Yahaya 21:1, 5.
Muhimmiyar tambaya ita ce, Kowannenmu yana yin gyara da ta dace don mu cancanci mu kasance cikin “sabuwar ƙasa” ƙarƙashin “sababbin sammai”?