Ina Rayuwarka Ta Nufa?
•Harkokin yau da kullum sun kwashe hankalin mutane da yawa a yau, kuma ba sa tunanin inda suke nufa ba.
• Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da aukuwa masu ban mamaki da suke zuwa a nan gaba. Ya kuma faɗakar da mu game da canji na farat ɗaya da ƙungiyoyin mutane za su yi. Domin mu amfana kuma mu kauce wa masifa, muna bukatar mu ɗauki mataki da gaggawa.
• Da akwai wasu mutane da suka san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kuma suke ƙoƙarin su yi amfani da shi amma suka ƙyale alhinin rai ya tura shi gefe ɗaya.
• Kana son inda rayuwarka ta nufa? Sa’ad da kake shirin wasu abubuwan yi kana lura ka ga yadda waɗannan za su iya shafan makasudanka masu daɗewa a rayuwa?
[Akwati/Hotuna a shafi na 9]
Me Ya Fi Muhimmanci a Gare Ka?
Yaya za ka jera waɗannan abubuwa? Ka jera su bisa adadinsu.
Da yawa cikinsu suna da wajen da ya dace a rayuwa, amma idan za ka yi zaɓe, me za ka sa farko? na biyu? da kuma sauransu?
․․․ Liyafa/nishaɗi
․․․ Aikina ko makasudina
․․․ Lafiyar jikina
․․․ Farin cikina
․․․ Abokiyar aureta
․․․ Iyayena
․․․ Yarana
․․․ Gida mai kyau, riguna masu kyau
․․․ Gwaninta a duk abin da nake yi
․․․ Bauta wa Allah
[Akwati a shafi na 10 da 11]
Zaɓen da Kake Yi Yana Kai Ka Inda Ka Nufa Kuwa?
KA BINCIKA WAƊANNAN TAMBAYOYI
LIYAFA/NISHAƊI: Ina samun wartsakewa a cikin nishaɗi da nake yi kuwa? Da akwai wasu abubuwa a ciki da za su iya zama mini haɗari ko su gurguntar da ni? “Moriya” ce da take motsawa na ’yan sa’o’i amma tana da ban ciwo mai daɗewa? Ko idan liyafa da na zaɓa mai kyau ce, ina ba da lokaci ainun gare ta da zai hana wasu abubuwa mafi muhimmanci?
AIKINA KO MAKASUDINA: Abin da zai taimake ni ne ko zai sa in zama bawansa ne? Yana bukatar abin da zai lalace lafiya ta ce? Zan fi son na ƙara lokacin aiki ko kuwa na kasance tare da abokiyar aureta ko yarana? Idan shugaban aikina ya bukaci na yi aikin da zai dami lamirina ko kuma yakan dami sha’anin ruhaniyata, zan yi wannan aikin ne domin kada a kore ni?
LAFIYAR JIKINA: Ba na damuwa da lafiyar jikina ko kuma ina lura da ita ainun ne? Ita kawai nake taɗinta? Yadda nake bi da shi ina damuwa da iyalina kuwa?
FARIN CIKINA: Abin da ya fi muhimmanci ke nan a gare ni? Ina damuwa da shi fiye da farin ciki na abokiyar aureta ko iyalita? Yadda nake biɗan farin ciki daidai ne da yadda ya kamata mai bauta wa Allah na gaskiya ya yi?
ABOKIYAR AURETA: Idan kawai zan amfana ne zan yarda cewa abokiyar aureta abokiyata ce? Ina bi da abokiyar aureta da daraja, cewa ta cancanci haka? Imanina ga Allah yana shafan yadda nake ɗaukan abokiyar aureta kuwa?
IYAYENA: Idan kai yaro ne, yaya biyayyata take ga iyayena—ina amsa musu da ladabi, ina yin aikin da suka ba ni, ina dawowa gida lokacin da suka ce, ina kauce wa tarayya da ayyuka da suka ƙi? Idan ka kai mutum, ina sauraron iyayena da ladabi, ina taimaka musu yadda ya kamata? Yadda nake bi da su yadda nake so ne ko abin da Kalmar Allah ta ce ne?
YARANA: Ina ɗaukan cewa hakkina ne na koya wa yarana ɗabi’ar kirki, ko kuma ina ƙyalewa a koya musu a makaranta ne? Ina ɓatar da lokaci tare da yarana, ko kuma ina ƙyale abin wasa, telibijin, ko kuma na’ura ta koya musu? Ina yi wa yara horo sa’ad da sun yi banza da tunasarwar Allah, ko kuma kawai idan na ji haushi ne?
GIDA MAI KYAU, RIGUNA MASU KYAU: Menene ke sarrafa yadda nake yin ado kuma menene ke mallakata—yadda nake son maƙwabtana su ɗauke ni ne? lafiyar iyalina ne? ko kuma domin cewa ni mai bauta wa Allah ne?
GWANINTA A DUK ABIN DA NAKE YI: Ina ganin muhimmancin yin abu da kyau? Ina ƙoƙari na zama gwani ne koyaushe? Ba na jin daɗi idan wani ya fi ṇi yin wani abu da kyau?
BAUTA WA ALLAH: Samun amincewar Allah ya fi muhimmanci gare ni fiye da samun amincewar abokiyar aureta, yarana, iyayena, ko kuma shugaban aikina? Zan so ne na sa bauta wa Allah ta zama na biyu a rayuwata domin na yi rayuwa mai gamsarwa?
KA BINCIKA GARGAƊIN LITTAFI MAI TSARKI DA KYAU
Wane wuri Allah yake da shi a rayuwarka?
Mai Hadishi 12:13: “Ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum.”
KA TAMBAYI KANKA: Rayuwata tana nuna haka nake ɗaukan abubuwa? Yin biyayya da dokokin Allah yana nuna cewa ina cika hakkina a gida, a wurin aiki, ko kuma a makaranta kuwa? Ko kuwa wasu abubuwa ko kuma matsi na rayuwa suna sa na yi tunanin ko zan keɓe lokaci domin Allah?
Wace irin dangantaka kake da ita da Allah?
Karin Magana 3:5, 6: “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da ke daidai.”
Matiyu 4:10: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujjada, shi kaɗai za ka bauta wa.”
KA TAMBAYI KANKA: Yadda nake ji ke nan ne game da Allah? Aikina na kullum, da yadda nake bi da matsala suna nuna irin dogara da keɓe kai da nake da shi?
Yaya karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki suke da muhimmanci gare ka?
Yahaya 17:3: “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.”
KA TAMBAYI KANKA: Muhimmanci da nake ba wa karatun Kalmar Allah da kuma yin tunani sosai a kanta ya nuna na gaskata da ita kuwa?
Yaya halartan taro na ikilisiyar Kirista yake da muhimmanci a gare ka?
Ibraniyawa 10:24, 25: “Mu kuma riƙa kula da juna, ta yadda za mu ta da juna a tsimi mu yi ƙauna da aiki nagari. Kada mu bar yin taronmu . . . Tun ba ma da kuka ga ranan nan tana kusatowa ba.”
Zabura 122:1: “Na yi murna sa’ad da suka ce mini, ‘Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!’ ”
KA TAMBAYI KANKA: Hanyar rayuwata tana nuna godiyata ga ja-gorar da ke cikin Kalmar Allah kuwa? A cikin watanni da suka shige, ban je taro ba ne domin wani ɗan abu kawai?
Kana da himma wajen yi wa mutane magana game da Allah da ƙudurinsa?
Matiyu 24:14: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida . . . Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”
Matiyu 28:19, 20: “Ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku.”
Zabura 96:2: “Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi! Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa, Ya cece mu!”
KA TAMBAYI KANKA: Wannan aikin yana matsayin da ya cancanta a rayuwata? Yadda nake sa hannu yana nuna na tabbata da irin yanayin da muke ciki?