Menene Dukan Waɗannan Abubuwa Ke Nufi?
YESU KRISTI ya ce: Yaƙi, ƙarancin abinci, annoba, da kuma girgizar ƙasa ne za su nuna “ƙarewar zamani.”—Matiyu 24:1-8; Luka 21:10, 11.
Tun shekara ta 1914 yaƙe-yaƙe tsakanin al’ummai da ƙabilu, waɗanda sau da yawa limamai ’yan siyasa suke tura su, sun yi wa rayuwa lahani, yanzu kuma har da farmakin ’yan ta’adda.
Duk da ci gaba na kimiyya, miliyoyin mutane a kewayen duniya suna shan wuya domin mummunar ƙarancin abinci. Kowacce shekara, miliyoyin mutane suna mutuwa domin ƙarancin abinci.
Annoba ma tana cikin alamar da Yesu ya bayar. Bayan Yaƙin Duniya na I, cutar massassara ta lashe rayuka fiye da 21,000,000, ba kamar annoba da ta shafi wasu wurare ba kawai. Ta shafi al’ummai da yawa a duk duniya har tsibirai masu nisa. Yanzu ƙanjamau yana share dukan duniya, da kuma wasu annoba kamar su tarin fuka, zazzabin ciwon sauro, da kuma ciwon barci da suke gaba gaba sosai a ƙasashe masu tasowa.
An ba da rahoton cewa dubban girgizan ƙasa suna aukuwa kowacce shekara da tsananinsu ya bambanta. Duk da yawan kayayyakin aiki da kuma yadda an kyautata hanyoyin ba da labarai, bala’in da aka shaida a inda jama’a suke da yawa saboda girgizar ƙasa sune suka zama labarai.
Littafi Mai Tsarki ma ya annabta: “Amma ka fahimta a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai. Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zage-zage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka, da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta, da maciya amana, da masu annashuwa, fiye da son Allah, suna riƙe da siffofin ibada, amma suna saɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.”—2 Timoti 3:1-5.
Ba ka yarda ba ne cewa muna zama cikin zamani da da ake ‘shan wuya ƙwarai’?
Ka kuwa lura cewa mutane sun zama masu sonkai sosai, masu son kuɗi, kuma masu girmankai?
Wa zai yi musun cewa duniya ta cika da mutane masu biɗa amma masu butulci, masu riƙo a zuci, kuma marasa tsarkaka?
Ka kuwa lura da cewa rashin bin iyaye tare da rashin ƙauna tana kan ƙaruwa, ba a wurare kaɗan kawai ba amma a dukan duniya?
Babu shakka ka lura cewa muna zama cikin duniya wadda ta shaƙu da son annashuwa amma tana rashin nagarta. Yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta halaye da za su mallaki “zamanin ƙarshe” ke nan.
Muna bukatar wani abu ne kuma don mu san irin lokaci da muke ciki? Yesu ya kuma annabta cewa a wannan lokaci ne ma za a yi bisharar Mulkin Allah a dukan duniya. (Matiyu 24:14) Ana yin haka kuwa?
Hasumiyar Tsaro, jaridar da take daga Littafi Mai Tsarki da aka keɓe ta domin shelar bisharar Mulkin Jehovah, ana buga ta a kai a kai cikin harsuna fiye da yadda ake buga wasu jaridun labarai.
Kowacce shekara, Shaidun Jehovah suna keɓe sa’o’i fiye da biliyan suna yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah.
Suna buga wasu littattafai masu tushe daga Littafi Mai Tsarki da sun kai cikin harsuna 400, har ma harsuna da suke nesa da jama’ar kalilan ne. Shaidun Jehovah sun kai dukan al’ummai da bisharar; sun kuma yi wa’azi a tsibirai da yankuna ƙanana da ba su kai a yi zancensu a duniya ba. A yawancin ƙasashe, suna gabatar da tsarin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki a kai a kai.
Hakika, ana wa’azin wannan bishara ta Mulkin Allah a dukan duniya, ba domin duniya duka su tuba ba, amma domin shaida. Ana ba wa mutane a ko’ina zarafin su nuna ko sun damu da wanda ya halicci sammai da duniya kuma su nuna ko za su yi biyayya ga dokokinsa kuma su nuna ƙauna ga maƙwabtansu.—Luka 10:25-27; Wahayin Yahaya 4:11.
Ba da daɗewa ba Mulkin Allah za ya kawar da dukan mugunta daga duniya kuma ya mai da ita aljanna.—Luka 23:43.
[Akwati a shafi na 6]
Kwanakin Ƙarshe na Menene?
Ba kwanakin ƙarshe na mutane ba. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da begen rayuwa ta har abada domin waɗanda suke yin nufin Allah.—Yahaya 3:16, 36; 1 Yahaya 2:17.
Ba kwanakin ƙarshe na duniya ba ne. Kalmar Allah ta yi alkawarin cewa duniya mazauni za ta kasance har abada.—Zabura 37:29; 104:5; Ishaya 45:18.
Maimako, waɗannan ne kwanaki na ƙarshe na wannan zamani marar ƙauna kuma na waɗanda suke bin hanyoyinsa.—Karin Magana 2:21, 22.
[Hoto a shafi na 7]
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah Ce Kuwa?
Sau da sau, annabawan Littafi Mai Tsarki sun rubuta: “Ubangiji ya ce.” (Ishaya 43:14; Irmiya 2:2) Yesu Kristi ma, wanda Ɗan Allah ne, ya nanata cewa ‘ba domin kansa yake faɗa ba.’ (Yahaya 14:10) A bayyane Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane Nassi hurare na Allah ne.”—2 Timoti 3:16.
Babu wani littafin da aka buga cikin harsuna da yawa haka—har fiye da 2,200 bisa rahoton Ƙungiyar Buga Littafi Mai Tsarki. Babu wani littafi da yake da yawa haka—da yanzu an rarraba fiye da biliyan huɗu. Ba abin da kake tsammanin zai faru ne da saƙo wanda yake daga Allah domin dukan mutane ba?
Domin ƙarin bayani game da cewa Littafi Mai Tsarki hurare ne daga Allah, dubi mujallar nan Littafi Don Dukan Mutane, wadda Shaidun Jehovah suka buga.
Idan ka karanta Littafi Mai Tsarki da imanin cewa Kalmar Allah ce da gaske, za ka amfana ƙwarai.
[Akwati/Hotuna a shafi na 8]
Menene Mulkin Allah?
Gwamnati ce ta musamman ta samaniya da Jehovah Allah na gaskiya, Mahaliccin sama da duniya ya kafa. —Irmiya 10:10, 12.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu Kristi ne Allah ya ba wa ikon sarautar nan. (Wahayin Yahaya 11:15) Sa’ad da yake duniya, ya nuna cewa yana da wannan iko daga wurin Allah—ikon da ya yi amfani da shi wurin sarauta bisa halitta, ya warkar da kowacce irin cuta, har kuma ya ta da matattu. (Matiyu 9:2-8; Markus 4:37-41; Yahaya 11:11-44) Hurarren annabcin Littafi Mai Tsarki ma ya annabta cewa Allah zai kuma ba shi “ɗaukaka, da sarauta, domin dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna, su bauta [yi hidima] masa.” (Daniyel 7:13, 14) Ana kiran gwamnatin nan Mulki na samaniya; daga sama ne ikon Yesu Kristi yake bayyanuwa.
[Hotuna a shafi na 7]
Wa’azin bishara na dukan duniya