Ina Wannan Duniya Ta Nufa?
Matsaloli masu tsanani da aukuwa na ban tsoro sun zama ruwan dare gama gari a duniya! Menene wannan yake nufi?
KWANCIYAR RAI: Bomabomai sun fashe babu zato babu tsammani a kasuwa. An harbe malamai da ɗalibai a makarantu. An sace yara daga iyayensu a ɗan lokaci da ba su saka musu ido ba. Da rana tsaka an yi wa tsofaffi maza da mata fashi.
YANAYIN ADDINI: Coci sun goyi bayan yaƙi. An kama limami da alhakin kisan ƙare dangi. Firistoci suna zalunta yara ƙanana; coci sun goyi bayan mugunta. Raguwa a yawan masu zuwan coci; an sayar da majami’u.
MAHALLI: An yaye daji domin kasuwanci. An sassare itatuwa ba ji ba gani domin neman fetur. Ruwa bai shawuwa domin gurɓacewa. An cika kogi da datti da kuma irin salon kamun kifi na zamani da yake karkashe kifaye. Gubar iska ya shaƙe mutane.
NEMAN ABINCI: A wasu wuraren Afirka kuɗin da ake samu a shekara kaɗan ne kawai. Haɗama ta manyan ’yan kasuwa tana jawo karyewar jari, ya bar dubbai babu aiki. Zamba tana sa masu zuba jari su yi hasarar ajiyar da suka yi da daɗewa.
ƘARANCIN ABINCI: Mutane wajen 800,000,000 kullum ba sa samun abincin yini.
YAƘI: Mutane fiye da miliyan 100 suka rasa rayukansu a yaƙe-yaƙe na ƙarni na 20. Da akwai isassun makaman nukiliya da zai iya halaka dukan mutane sau da yawa. Yaƙe-yaƙen basasa. Ta’addanci ya shafi dukan duniya.
ANNOBA DA WASU CUTUTTUKA: Somawa a shekara ta 1918 cutar massassara ta kashe mutane 21,000,000. Yanzu ƙanjamau ne wanda “ya fi halakarwa a duk tarihin ’yan Adam.” Ciwon daji, da kuma ciwon zuciya sun jawo baƙin ciki da yawa a duk faɗin duniya.
Kada ka mai da hankalinka waje ɗaya kawai. Abubuwa da suke aukuwa a waje ɗaya kawai? Ko kuma sun tattara ne cikin aukuwa ta duniya da ke da muhimmanci?
[Akwati/Hoto a shafi na 5]
Allah Yana Kula Kuwa?
Domin aukuwa masu razanarwa ko kuma hasarar da ake yi, mutane da yawa sun damu cewa me ya sa Allah bai sa hannu ya hana waɗannan abubuwa ba.
Allah yana kula. Yana tanadin kāriya mai kyau da kuma sauƙaƙawa a yanzu. (Matiyu 11:28-30; 2 Timoti 3:16, 17) Ya riga ya kafa abin da zai kawo ƙarshen nuna ƙarfi, ciwo, da kuma mutuwa. Tanadinsa ya nuna cewa yana kula ba kawai da mutanen al’umma ɗaya ba amma da mutane daga dukan al’ummai, ƙabilu, da harsuna.—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
Ta yaya muke damuwa da ƙudurin Allah? Ka san Mahaliccin sama da duniya? Menene sunansa? Menene ƙudurinsa? Ya amsa waɗannan tambayoyin cikin Littafi Mai Tsarki. A nan, ya gaya mana matakai da ya ɗauka don ya kawo ƙarshen nuna ƙarfi da ciwo da kuma mutuwa. Don mu amfana, me ake bukata a gare mu? Muna bukatar mu koya game da shi da kuma ƙudurinsa. Ta yaya za mu yi tsammanin za mu amfana daga tanadinsa idan ba mu yi imani da shi ba? (Yahaya 3:16; Ibraniyawa 11:6) Ya dace mu yi biyayya da farillansa. (1 Yahaya 5:3) Ka damu ka yi hakan kuwa?
Don a fahimci dalilin yanayi na yanzu da Allah ya ƙyale, dole ne mu fahimci wani batu mai muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya bayyana shi. An yi bayani a kan wannan batu a shafi 15 na wannan mujallar.