SASHE NA 9
Addini na Gaskiya Zai Amfane Ka Har Abada!
1. Menene zai faru idan muka “kusato ga Allah”?
JEHOBAH yana ƙaunar waɗanda suke bauta masa. Idan kana bauta wa Jehobah, zai albarkace ka a yanzu da kuma a nan gaba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.”—Yaƙub 4:8.
2. Ta yaya za mu kusaci Allah, kuma ta yaya zai shafi addu’armu?
2 Domin ka kusaci Allah, dole ne ka yi nazari kuma ka yi amfani da Kalmarsa. Idan ka yi addu’a da ta jitu da nufinsa, Jehobah zai saurari addu’arka kuma ya amsa. Manzo Yohanna Kirista ya rubuta: “Gaba gaɗi ke nan da mu ke yi a gaban [Allah], idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu: kuma idan mun sani yana jinmu, kome muke roƙo, mun sani muna samun abin da mun roƙa a gare shi.”—1 Yohanna 5:14, 15.
3-7. Ta yaya za mu samu hikima ta ibada, kuma ta yaya za ta taimake mu?
3 Bugu da ƙari, yayin da ka kusaci Allah, shi kuma zai ba ka hikima da za ka bi da al’amura na yau da kullum. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah.”—Yaƙub 1:5.
4 Ta yaya hikima ta ibada za ta taimake ka? Abu ɗaya shi ne, za ta taimake ka ka san abubuwa da suke ɓata wa Jehobah rai. Za ka kuma koyi abin da ya sa waɗannan abubuwa ba su da kyau, da kuma abin da za ka yi ka guje wa ayyukan. Irin wannan ilimin zai kāre ka daga yawancin matsaloli da suke damun galibin mutane. Alal misali, biyayya ga gargaɗin Allah mu kasance da ɗabi’a mai kyau yana taimaka wajen kāre mutanen Allah daga ɗaukan cikin shige, cututtuka da ake ɗauka ta jima’i, da kuma aure marar farin ciki ko kuma kashe aure.
5 Menene kuma hikima da Allah ya bayar za ta yi maka? Za ta taimake ka ka amfana ƙwarai daga rayuwa. Za ta taimake ka ka yanke shawara mai hikima a al’amura, kamar su bi da dukiyarka. Za ka iya bin buri masu kyau ka bar buri da ba su da amfani mai jimawa.
6 Hikima ta ibada za ta taimake ka wajen dangantakarka da wasu. Za ka kasance da iyali mai farin ciki. Za ka ƙulla abokantaka mai kyau da wasu, kuma a ba ka daraja, har daga wajen waɗanda ba sa bauta wa Allah.
7 Ƙari ga haka, kasancewarka da hikima ta ibada za ta gyara yadda kake ɗaukar rayuwa. Za ta taimaka maka ka jure wa matsalolin rayuwa da kuma ɓacin rai. Kuma za ka kasance da daidaitaccen bege mai kyau a nan gaba. Bege mai kyau, kuma zai daɗa ga lafiyarka ta jiki da ta hankali.—Misalai 14:30; Ishaya 48:17.
8. Idan kana bauta wa Allah, menene ba za ka ji tsoronsu ba?
8 Idan kana bauta wa Allah na gaskiya, za ka samu ’yanci daga tsoro da yake matsa wa waɗanda ba sa bauta masa. Domin ka sani cewa matattu ba su da rai a cikin kabari, ba za ka ji tsoron waɗanda suka mutu ba. Domin ka dogara bisa alkawarin Allah cewa zai ta da matattu, ba za ka ji tsoron mutuwa ba. Kuma domin ka sani cewa Allah ya fi kome iko, ba za ka ji tsoron maita ba ko duba.—Yohanna 8:32.
Masu Tawali’u Za Su Gāji Duniya
9-11. Su waye za su rayu cikin Aljanna, kuma su waye ba za su rayu ba?
9 Idan ka kusaci Allah, ba za ka ji tsoron abin da ke zuwa nan gaba ba. Kamar yadda muka gani, Littafi Mai Tsarki ya faɗi yawancin matsalolin da muke gani a duniya a yau. Jehobah ya gaya mana cewa waɗannan abubuwa na ɗan lokaci ne kawai; Mulkin Allah ba da daɗewa ba zai mai da duniya aljanna.—Luka 21:10, 11, 31; 23:43.
10 Waɗanda suka kusaci Jehobah, suka kuma bauta masa ne kawai za su yi rayuwa a cikin Aljanna. Littafi Mai Tsarki ya ce: “In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:10, 11.
11 Waɗanda da gangan suka ƙi su yi biyayya ga dokokin Allah masu adalci za su rasa rayukansu har abada. (2 Tasalonikawa 1:8, 9) Ba za su kasance ba. Za su haɗu da Shaiɗan da aljannunsa a mutuwa ta har abada. (Ru’ya ta Yohanna 20:10, 14) Amma waɗanda suka koyi game da Jehobah kuma suka bauta masa za su faranta zuciyarsu cikin Aljanna a duniya.
Abin da Ke Zuwa a Nan Gaba Mai Ban Sha’awa!
12. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da abin da ke zuwa a nan gaba?
12 Jehobah ya ajiye abubuwa masu ban sha’awa ga waɗanda suke ƙaunarsa! Ga abin da Kalmarsa ta ce game da rayuwa a Aljanna a duniya:
Yalwar abinci da za a ci: “Za a yi albarkar hatsi [ko, abinci] a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.”—Zabura 72:16.
Gidaje masu kyau: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki.”—Ishaya 65:21.
Aiki da za a ji daɗinsa: “Za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu. Ba za su yi aiki a banza ba.”—Ishaya 65:22, 23.
Babu ciwo: “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24.
Babu Naƙasa: “Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe. Sa’annan gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa, harshen bebe kuma za ya rera waƙa.”—Ishaya 35:5, 6.
Babu azaba, baƙin ciki, da mutuwa: “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.
Babu yaƙi: “[Allah] ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.”—Zabura 46:9.
Rai madawwami: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29.
13. Waye ne kawai zai iya mayar da duniyar nan aljanna, kuma me ya sa?
13 ’Yan Adam ba za su taɓa kawo irin waɗannan abubuwa ba, amma Jehobah yana da ikon ya yi dukan abin da ya ce zai yi. Babu abin da zai hana shi yin abin da yake so ya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.”—Luka 1:37.
14. Ta yaya za ka samu hanyar zuwa rai madawwami?
14 Ta wajen Shaidunsa, Jehobah yana bai wa mutane a ko’ina zarafin su “shiga ta wurin ƙunƙuntar ƙofa” kuma su yi tafiya bisa hanyar da take kai wa zuwa rai madawwami. Ka kasance tsakanin mutane masu farin ciki da suka karɓi wannan gayyatar. Ka yi addini na gaskiya kuma ka more albarkar Jehobah har abada abadin!—Matta 7:13, 14.