Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 3 Yohanna 1:1-5:21
  • 1 Yohanna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1 Yohanna
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
1 Yohanna

WASIƘAR YOHANNA TA FARKO

1 Muna rubuta muku game da wanda yake raye tun farko, wanda muka ji muryarsa, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka lura da shi kuma hannayenmu sun taɓa shi, wato kalmar rai, 2 (hakika, an bayyana mana wannan rai, mun kuwa gani, muna ba da shaida kuma muna gaya muku game da rai na har abadan nan wanda tun dā yake tare da Uba kuma aka bayyana mana shi), 3 shi wannan wanda muka gani muka kuma ji muryarsa, muna gaya muku game da shi, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Haka mu ma muke tarayya da Uba da kuma Ɗansa Yesu Kristi. 4 Kuma muna rubuta muku abubuwan nan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.

5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa kuma muna sanar muku da shi, cewa: Allah haske ne, kuma babu duhu ko kaɗan a cikinsa. 6 Idan muka faɗa cewa, “Muna yin tarayya da shi,” duk da haka mun ci-gaba da yin rayuwa cikin duhu, muna yin ƙarya kuma ba ma yin rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma idan muna yin rayuwa a cikin haske, kamar yadda shi ma yake cikin haske, muna tarayya da juna, kuma jinin Yesu Ɗansa ya wanke mu daga dukan zunubi.

8 Idan muka faɗa cewa, “Ba mu da zunubi,” muna ruɗin kanmu ne, kuma gaskiyar ba ta cikinmu. 9 Idan mun furta zunubanmu, shi mai aminci ne da adalci, kuma zai gafarta zunubanmu, ya kuma tsabtace mu daga dukan rashin adalci. 10 Idan muka faɗa cewa, “Ba mu yi zunubi ba,” muna mai da shi maƙaryaci ke nan, kuma kalmarsa ba ta cikinmu.

2 ꞌYan yarana, ina rubuta muku abubuwan nan ne don kada ku yi zunubi. Amma idan wani ya yi zunubi, muna da mai taimako wanda yake tare da Uba, wato Yesu Kristi, kuma shi mai adalci ne. 2 Shi ne hadaya na sasanta tsakaninmu da Allah, ba domin mu kaɗai ba amma domin dukan duniya. 3 Kuma idan mun ci-gaba da yin biyayya ga dokokin Allah, hakan zai nuna cewa mun san shi. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin biyayya ga dokokinsa, shi maƙaryaci ne, kuma gaskiya ba ta cikin mutumin nan. 5 Amma duk wanda ya yi biyayya ga kalmarsa, da gaske ƙaunar Allah ta zama cikakke a cikin mutumin. Ta haka ne muka san cewa muna da haɗin kai tare da shi. 6 Wanda ya ce yana da haɗin kai tare da shi dole ne ya ci-gaba da yin rayuwa daidai da yadda shi ma ya yi rayuwa.

7 Ƙaunatattuna, ba sabuwar doka ba ce nake rubuta muku, amma tsohuwar doka ce da kuka ji tun farko. Wannan tsohuwar dokar ita ce kalmar da kuka ji. 8 Ina sake rubuta muku game da wata sabuwar doka, wadda Yesu ya bi, da ku ma kuke bi, domin duhu yana shuɗewa kuma hasken gaske ya riga ya fara haskakawa.

9 Duk wanda ya ce yana cikin haske amma ya tsani ɗanꞌuwansa, har yanzu yana cikin duhu. 10 Wanda yake ƙaunar ɗanꞌuwansa yana cikin haske, kuma babu abin da zai sa shi tuntuɓe.* 11 Amma wanda ya tsani ɗanꞌuwansa yana cikin duhu, kuma yana rayuwa cikin duhu, bai san inda za shi ba, domin duhun ya makantar da shi.

12 Yara ƙanana, ina rubuta muku wannan wasiƙar domin an gafarta zunubanku saboda sunansa. 13 Ku ubanni, ina rubuta muku wannan wasiƙar domin kun zo ga sanin shi wanda yake nan tun daga farko. Ku samari, ina rubuta muku wannan wasiƙar domin kun yi nasara a kan mugun nan. Ku yara ƙanana, na rubuta muku wannan wasiƙar domin kun zo ga sanin Uban. 14 Ku ubanni, na rubuta muku wannan wasiƙar domin kun zo ga sanin shi wanda yake nan tun daga farko. Ku samari, na rubuta muku wannan wasiƙar domin kuna da ƙarfi kuma kalmar Allah tana cikinku kuma kun yi nasara a kan mugun nan.

15 Kada ku ƙaunaci duniya ko kuma abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yana ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uban; 16 domin dukan abubuwan da suke cikin duniya​—⁠kamar shaꞌawar jiki da shaꞌawar idanu da kuma yin taƙama da abin da mutum yake da shi⁠​—⁠⁠ba daga wurin Uba suka fito ba, amma sun fito ne daga duniya. 17 Ƙari ga haka, duniya da dukan abubuwan da mutanen duniya suke shaꞌawa suna wucewa, amma wanda yake yin nufin Allah zai rayu har abada.

18 Yara ƙanana, mun shiga awa ta ƙarshe, kuma kamar yadda kuka ji cewa maƙiyin Kristi yana zuwa, ko a yanzu ma maƙiyan Kristi da yawa sun bayyana, kuma hakan ya sa mun san cewa mun shiga awa ta ƙarshe. 19 A dā suna tare da mu, amma sun bar mu domin su ba namu ba ne; da a ce su namu ne, da sun ci-gaba da kasancewa tare da mu. Amma sun fita domin a san cewa ba kowa ba ne namu. 20 Allah mai tsarki ya shafe ku da ruhu mai tsarki, kuma dukanku kuna da ilimi. 21 Ba domin ba ku san gaskiya ba ne na rubuta muku wasiƙa, amma domin kun san gaskiya, kuma babu ƙarya da ta fito daga gaskiya.

22 Wane ne maƙaryaci, in ba wanda ya yi mūsun cewa Yesu ne Kristi ba? Wannan shi ne maƙiyin Kristi, wanda ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan. 23 Duk wanda ya yi mūsun Ɗan, ba shi da haɗin kai da Uban ma. Amma duk wanda ya yarda da Ɗan yana da haɗin kai da Uban ma. 24 Amma ku kam, dole ne ku riƙe abin da kuka ji tun daga farko. Idan kun ci-gaba da riƙe abin da kuka ji tun daga farko, za ku ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da Ɗan da kuma Uban. 25 Ƙari ga haka, abin da shi da kansa ya yi mana alkawarin sa shi ne rai na har abada.

26 Na rubuta muku abubuwan nan ne game da waɗanda suke ƙoƙari su yaudare ku. 27 Amma ku kam, Allah ya shafe ku da ruhunsa, ruhun nan yana tare da ku har yanzu, kuma ba kwa bukatar wani ya riƙa koyar da ku; amma Allah yana amfani da ruhun ya koya muku dukan abubuwa, kuma abin da ruhu yake koya muku gaskiya ne ba ƙarya ba. Kamar yadda ya koya muku, ku ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi. 28 Don haka, yara ƙanana, ku ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi, domin saꞌad da aka bayyana shi, za mu samu ꞌyancin yin magana, ba wai mu ɓoye a lokacin dawowarsa saboda kunya ba. 29 Idan kun san cewa shi mai adalci ne, hakan yana nufin kun san cewa duk mai yin adalci ɗansa ne.

3 Ku ga irin ƙauna da Uba ya nuna mana, da ya sa aka kira mu ꞌyaꞌyan Allah! Kuma haka muke. Shi ya sa duniya ba ta san mu ba, domin ba ta zo ga sanin sa ba. 2 Ƙaunatattuna, a yanzu mu ꞌyaꞌyan Allah ne, amma ba a bayyana mana abin da za mu zama ba tukuna. Mun dai san cewa saꞌad da aka bayyana shi, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi yadda yake. 3 Kuma duk wanda yake da wannan bege a kansa, ya tsabtace kansa kamar yadda shi yake da tsabta.

4 Duk wanda yake yin zunubi yana taka doka, kuma yin zunubi taka doka ne. 5 Kun kuma san cewa an bayyana shi ne domin ya ɗauke zunubanmu, kuma babu zunubi a cikinsa. 6 Duk wanda ya ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi ba ya yin zunubi; babu wanda ya ci-gaba da yin zunubi da ya taɓa ganin shi ko kuma ya zo ga sanin shi. 7 Yara ƙanana, kada wani ya ruɗe ku; wanda ya ci-gaba da yin adalci, shi mai adalci ne kamar yadda wancan* ma yake da adalci. 8 Wanda ya ci-gaba da yin zunubi ya fito daga wurin Ibilis ne, gama tun daga farko Ibilis yana yin zunubi, saboda wannan ne aka bayyana Ɗan Allah, domin ya rushe ayyukan Ibilis.

9 Duk wanda ya zama ɗan Allah, ba ya yin zunubi, gama iri na Allah yana cikin mutumin, kuma ba zai iya yin zunubi ba domin shi ɗan Allah ne. 10 Ta wannan ne ake gane ꞌyaꞌyan Allah da ꞌyaꞌyan Ibilis: Wanda ba ya yin adalci bai fito daga wurin Allah ba, haka ma yake da wanda ba ya ƙaunar ɗan­ꞌuwansa. 11 Gama wannan ne saƙon da muka ji tun daga farko, cewa mu ƙaunaci juna; 12 ba kamar Kayinu, wanda ya fito daga wurin mugun nan kuma ya kashe ɗanꞌuwansa ba. Kuma me ya sa ya kashe ɗanꞌuwansa? Domin ayyukansa na mugunta ne, amma ayyukan ɗanꞌuwansa kuma na adalci ne.

13 ꞌYanꞌuwa, kada ku yi mamaki domin duniya ta tsane ku. 14 Mun san cewa mun ƙetare daga mutuwa zuwa rai ne domin muna ƙaunar ꞌyanꞌuwa. Wanda ba ya ƙauna, har yanzu yana cikin mutuwa. 15 Duk wanda ya tsani ɗanꞌuwansa mai kisa ne, kuma kun san cewa babu mai kisa da zai sami rai na har abada. 16 Ta haka ne muka zo ga sanin ƙauna, domin shi ya ba da ransa* saboda mu, kuma ya zama mana dole mu ba da rayukanmu* saboda ꞌyanꞌuwanmu. 17 Amma duk wanda yake da abin duniya kuma ya ga ɗanꞌuwansa da ke da bukata, duk da haka ya ƙi ya ji tausayin sa, to, ta yaya mutumin zai ce yana ƙaunar Allah? 18 Yara ƙanana, mu nuna ƙauna ba da baki kawai ba, amma ta ayyuka da kuma gaskiya.

19 Ta haka ne za mu san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya sa zukatanmu su kasance da tabbaci a gabansa 20 a duk lokacin da zukatanmu sun sa mu ji kamar muna da laifi, domin Allah ya fi zukatanmu kuma ya san dukan abubuwa. 21 Ƙaunatattuna, idan zukatanmu ba su sa mun ji kamar mun yi laifi ba, muna da ꞌyancin yin magana a gaban Allah ke nan; 22 kuma yana ba mu duk abin da muka roƙa, domin muna bin dokokinsa kuma muna yin abin da yake da kyau a idanunsa. 23 Hakika, dokarsa ita ce: mu ba da gaskiya ga sunan Ɗansa Yesu Kristi kuma mu ƙaunaci juna, kamar yadda ya umurce mu. 24 Wanda yake bin dokokinsa zai ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi, kuma shi ma zai kasance da haɗin kai da irin mutumin nan. Kuma ta wurin ruhun da ya ba mu, mun san cewa har yanzu yana da haɗin kai da mu.

4 Ya ƙaunatattu, kada ku yarda da kowane saƙo da aka ce daga wurin Allah* ne, amma ku gwada saƙonnin ku ga ko sun fito daga wurin Allah da gaske, gama annabawan ƙarya da yawa sun fito a duniya.

2 Ga yadda za ku gane cewa saƙon ya fito daga wurin Allah: Duk wani saƙo da ya ce Yesu Kristi ya zo a cikin jiki, saƙon ya fito daga wurin Allah ne. 3 Amma duk saƙon da a ciki an yi mūsun cewa Yesu ya zo, saƙon bai fito daga wurin Allah ba. Ƙari ga haka, wannan saƙon daga maƙiyin Kristi ne da kuka ji cewa yana zuwa, kuma yanzu ya riga ya zo duniya.

4 Yara ƙanana, daga wurin Allah ne kuka fito, kuma kun yi nasara a kansu,* domin wanda yake da haɗin kai da ku ya fi wanda yake da haɗin kai da duniya. 5 Sun fito ne daga duniya; shi ya sa suke faɗan abubuwa da suka fito daga duniya, kuma duniya tana saurarar su. 6 Mun fito ne daga Allah. Kuma duk wanda ya zo ga sanin Allah yana saurarar mu; duk wanda bai fito daga wurin Allah ba ba ya saurarar mu. Ta haka ne muke bambanta tsakanin saƙo na gaskiya da kuma saƙo na ƙarya.

7 Ya ku ƙaunatattu, bari mu ci-gaba da ƙaunar juna, domin ƙauna daga wurin Allah ne, kuma duk wanda yake nuna ƙauna ɗan Allah ne kuma ya san Allah. 8 Duk wanda ba ya nuna ƙauna bai zo ga sanin Allah ba, domin Allah ƙauna ne. 9 Ta haka ne aka nuna ƙaunar Allah a gare mu, cewa Allah ya aiko Ɗansa makaɗaici cikin duniya don mu iya samun rai ta wurinsa. 10 Ga yadda ƙaunar take, ba wai mu ne muka ƙaunaci Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, kuma ya aiko Ɗansa a matsayin hadaya don sasanta tsakaninmu da Shi.

11 Ƙaunatattu, tun da haka ne Allah ya ƙaunace mu, dole ne mu ma mu ƙaunaci juna. 12 Babu wanda ya taɓa ganin Allah. Idan mun ci-gaba da ƙaunar juna, Allah zai ci-gaba da kasancewa a cikinmu kuma ƙaunarsa za ta zama cikakke a cikinmu. 13 Ta haka ne za mu san cewa muna ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi, kuma shi ma yana da haɗin kai da mu, domin ya riga ya ba mu ruhunsa. 14 Ƙari ga haka, mu da kanmu mun gani kuma muna ba da shaida cewa Uban ya aiko da Ɗansa a matsayin mai ceton duniya. 15 Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah zai ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da mutumin kuma mutumin zai kasance da haɗin kai da Allah. 16 Mun zo ga sanin ƙaunar da Allah yake nuna mana, kuma mun ba da gaskiya ga ƙaunar.

Allah ƙauna ne, kuma wanda ya ci-gaba da nuna ƙauna zai ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da Allah, kuma Allah zai ci-gaba da kasancewa da haɗin kai da shi. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakke a cikinmu, don mu iya kasancewa da ꞌyancin yin magana a ranar shariꞌa, gama kamar yadda wancan* yake, haka mu ma muke a duniyar nan. 18 A inda ƙauna take, babu tsoro, amma cikakkiyar ƙauna takan kawar da tsoro, domin tsoro yana hana mu yin abubuwa da yawa. Hakika, wanda yake jin tsoro ba shi da cikakkiyar ƙauna. 19 Muna nuna ƙauna domin shi ne ya fara nuna mana ƙauna.

20 Idan wani ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma ya tsani ɗanꞌuwansa, shi maƙaryaci ne. Gama wanda ba ya ƙaunar ɗanꞌuwansa wanda yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda bai taɓa gani ba. 21 Kuma ya ba mu wannan dokar cewa, duk wanda yake ƙaunar Allah, dole ne ya ƙaunaci ɗanꞌuwansa ma.

5 Duk wanda ya ba da gaskiya cewa Yesu shi ne Kristi, shi ɗan Allah ne, kuma duk wanda yake ƙaunar mahaifi, yana kuma ƙaunar ꞌyaꞌyan mahaifin. 2 Ta haka ne za mu san cewa muna ƙaunar ꞌyaꞌyan Allah, idan muna ƙaunar Allah kuma muna bin dokokinsa. 3 Gama ga abin da ƙaunar Allah take nufi, cewa mu bi dokokinsa; kuma dokokinsa ba su da wuyan bi,* 4 domin duk wanda shi ɗan Allah ne, ya yi nasara da duniya. Kuma bangaskiyarmu ce ta sa muka yi nasara da duniya.

5 Wane ne zai iya yin nasara da duniya? Shin ba wanda ya ba da gaskiya cewa Yesu ne Ɗan Allah ba? 6 Shi ne wanda ya zo ta wurin ruwa da kuma jini, wato Yesu Kristi, ba ta wurin ruwa kawai ba, amma ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhun kuma yana ba da shaida, domin ruhun gaskiya ne. 7 Gama akwai abubuwa uku da ke ba da shaida: 8 ruhun, da ruwan, da jinin; abubuwa ukun nan kuma manufarsu ɗaya ce.

9 Idan muka karɓi shaidar mutane, ai shaidar Allah ta fi girma. Domin wannan ita ce shaidar da Allah ya bayar, wato, shaidar da ya bayar game da Ɗansa. 10 Mutumin da yake ba da gaskiya ga Ɗan Allah yana da shaidar nan a zuciyarsa. Wanda ba ya ba da gaskiya ga Allah, ya mai da Allah maƙaryaci, domin bai ba da gaskiya ga shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. 11 Wannan ita ce shaidar, cewa Allah ya ba mu rai na har abada, kuma ta wurin Ɗansa ne yake ba da wannan rai. 12 Wanda yake da haɗin kai da Ɗan yana da wannan rai; amma duk wanda ba shi da haɗin kai da Ɗan Allah, ba shi da wannan rai.

13 Na rubuta muku abubuwan nan ne domin ku sani cewa kuna da rai na har abada, ku da kuka ba da gaskiya ga sunan Ɗan Allah. 14 Kuma muna da wannan tabbacin game da Allah, cewa ko da mene ne muka roƙa da ya yi daidai da nufinsa, yana saurarar mu. 15 Kuma idan mun san cewa zai saurare mu idan muka roƙe shi kowane abu, mun san cewa za mu samu abubuwan da muka roƙa, tun da yake mun roƙe shi abubuwan.

16 Idan wani ya ga ɗanꞌuwansa yana yin zunubi wanda ba zai kai ga mutuwa ba, zai yi masa adduꞌa kuma Allah zai ba shi rai, wato, ga waɗanda ba sa yin zunubin da zai kai ga mutuwa. Akwai zunubin da zai kai ga mutuwa. Ba irin wannan zunubin ne na ce masa ya yi adduꞌa a kai ba. 17 Dukan rashin adalci zunubi ne, duk da haka, akwai zunubin da ba ya kai ga mutuwa.

18 Mun san cewa duk wanda shi ɗan Allah ne ba ya ci-gaba da yin zunubi, amma wanda shi ɗan Allah* ne yana lura da shi, kuma mugun nan ba zai iya riƙe shi ba. 19 Mun san cewa mu na Allah ne, amma dukan duniya tana ƙarƙashin ikon mugun nan. 20 Ƙari ga haka, mun san cewa Ɗan Allah ya zo, kuma ya ba mu ganewa don mu iya sanin wanda shi ne gaskiya. Kuma muna da haɗin kai da wanda shi ne gaskiya, ta wurin Ɗansa Yesu Kristi. Wannan shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada. 21 Ya ku ƙananan yara, ku kiyaye kanku daga gumaka.

Yana kuma iya nufin, “ba ya sa mutane tuntuɓe.”

Wato, Yesu.

A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

A yaren Girka, “ruhu.”

Wato, annabawan ƙaryan.

Wato, Yesu Kristi.

A yaren Girka, “nauyi.”

Wato, Yesu Kristi Ɗan Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba