Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 2 Yohanna 1:1-3:18
  • 2 Bitrus

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2 Bitrus
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
2 Bitrus

WASIƘAR BITRUS TA BIYU

1 Daga Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kristi, zuwa ga waɗanda suka samu imani mai daraja kamar yadda mu ma muka samu ta wurin adalcin Allahnmu, da kuma Yesu Kristi Mai Ceto:

2 Bari alheri da salamar da Allah yake ba ku su ƙaru, ta wurin cikakken ilimi game da Allah da kuma Yesu Ubangijinmu. 3 Allah cikin ikonsa ya ba mu dukan abubuwan da muke bukata don mu rayu kuma mu yi ibada da dukan zuciyarmu ta wurin cikakken ilimi game da Wanda ya kira mu da ɗaukakarsa da kuma halin kirkinsa. 4 Ta wurin waɗannan abubuwan ne ya yi mana alkawarin manyan abubuwa da suke da daraja sosai, kuma ta wurin abubuwan nan za ku samu rabo a cikin ɗaukakar Allah, da yake kun guje wa lalacin da ke duniya wanda mugayen shaꞌawoyi suke jawowa.

5 Saboda haka, ku yi iya ƙoƙarinku ku ƙara wa bangaskiyarku halin kirki, ku ƙara wa halin kirkinku ilimi, 6 ku ƙara wa iliminku kamun kai, ku ƙara wa kamun kanku jimrewa, ku ƙara wa jimrewarku ibada da dukan zuciyarku, 7 ku ƙara wa ibada da dukan zuciyarku son ꞌyanꞌuwa, ku ƙara wa son ꞌyanꞌuwanku ƙauna. 8 Gama idan halayen nan sun kasance a cikinku kuma suka yalwata, za su sa ku yi amfani da cikakken ilimi game da Ubangijinmu Yesu Kristi da kyau, kuma ba za ku yi zaman banza ko ku zama marasa ba da amfani ba.

9 Gama duk wanda ba ya yin abubuwan nan shi makaho ne kuma ba ya so ya ga haske, kuma ya manta da yadda aka tsabtace shi daga zunubansa na dā. 10 Saboda haka ꞌyanꞌuwa, ku ci-gaba da yin iya ƙoƙarinku don ku tabbatar da kiran ku da kuma zaɓan ku da aka yi, gama idan kun ci-gaba da yin abubuwan nan, ba za ku taɓa faɗuwa ko kaɗan ba. 11 Hakika, ta yin hakan, za a ba ku babbar dama don ku shiga Mulki na har abada na Ubangijinmu da Mai Ceto Yesu Kristi.

12 Saboda haka, a kullum ina so in riƙa tuna muku da abubuwan nan ko da yake kun san su kuma kun kafu sosai a cikin gaskiyar da kuke da ita. 13 Amma a ganina ya dace, muddin ina cikin tentin nan* in riƙa tuna muku abubuwan nan, 14 yayin da nake hakan, na san an kusa a cire tentina kamar yadda Ubangijinmu Yesu Kristi ma ya bayyana mini hakan dalla-dalla. 15 A koyaushe, zan ci-gaba da yin iya ƙoƙarina domin bayan na bar duniya, za ku iya tuna da abubuwan nan da kanku.

16 Saꞌad da muka ba ku labarin yadda Ubangijinmu Yesu Kristi ya bayyana da iko, ba tatsuniyoyi da aka ƙirƙiro da wayo ne muka bi ba, a maimakon haka, da idanunmu muka shaida ɗaukakarsa. 17 Gama daga wurin Allah Uba ne ya karɓi daraja da ɗaukaka, kuma wannan ya faru ne saꞌad da Allah wanda ya ba shi ɗaukaka ya ce: “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna, wanda ni da kaina na amince da shi.” 18 Hakika, mun ji kalmomin nan suna fitowa daga sama saꞌad da muke tare da shi a tudu mai tsarki.

19 Wannan ya sa mun ƙara kasancewa da tabbaci cewa annabce-annabce da aka yi za su cika, ya dace da kuke mai da hankali ga annabce-annabcen nan da suke kamar fitila da ke haskakawa a cikin duhu, wato a cikin zukatanku har sai gari ya waye kuma tauraron safe ya fito. 20 Da farko, ku sani cewa babu wani annabci da ke cikin nassi da ya fito daga raꞌayin mutane. 21 Gama ba a taɓa yin annabci da ya samo tushensa daga nufin mutum ba, amma ruhu mai tsarki ne ya ja-goranci mutane su faɗi abin da Allah yake so su faɗa.

2 Amma, kamar yadda a lokacin an sami annabawan ƙarya a cikin mutanen Israꞌila, haka ma za a sami malaman ƙarya a cikinku. A hankali, mutanen nan za su kafa ƙungiyoyin tawaye da za su ɓata bangaskiyarku kuma su yi mūsun wanda ya saye su, ta hakan za su jawo wa kansu hallaka da sauri. 2 Ƙari ga haka, mutane da yawa za su bi halinsu na rashin kunya,* kuma saboda su, za a riƙa yin maganganu marasa kyau a kan hanyar gaskiya. 3 Ƙari ga haka, za su cuce ku ta wurin maganganun ƙarya saboda haɗamarsu. Amma hukuncin da aka riga aka yanke musu tun da daɗewa, yana zuwa da sauri, kuma ba shakka Allah zai hallaka su.

4 Hakika, Allah bai fasa hukunta malaꞌikun da suka yi zunubi ba, amma ya jefa su cikin kurkuku da ake kira Tataros,* ya ɗaura su da sarƙoƙi kuma ya saka su a cikin tsananin duhu, har sai lokacin da za a yanke musu hukunci. 5 Kuma bai fasa hukunta duniya ta dā ba, amma ya ceci Nuhu mai waꞌazin adalci, tare da wasu mutane bakwai saꞌad da ya kawo ambaliyar ruwa a kan duniyar da take cike da marasa tsoron Allah. 6 Kuma ya mai da biranen Sodom da Gomorra toka, ya hukunta su, ta hakan ya mai da su misali na abin da zai yi wa marasa tsoron Allah. 7 Amma ya ceci Lutu mai aminci, wanda a dā yake baƙin ciki saboda halin rashin kunya* na mugayen mutanen​—⁠ 8 domin saꞌad da wannan mutum mai adalci yake zama a cikinsu, ya yi baƙin ciki* sosai a kowace rana domin mugayen ayyuka da suke yi da yake gani kuma yake ji. 9 Don haka, Jehobah* ya san yadda zai ceci mutanen da suke masa ibada da dukan zuciyarsu daga matsaloli, ya kuma san yadda zai ajiye marasa adalci don ya hallaka su a ranar shariꞌa, 10 musamman ma masu bin shaꞌawar jikinsu kuma suke ƙoƙarin lalata wasu, da waɗanda suke rena hukuma.

Ba sa jin tsoro, suna da taurin kai kuma suna zagin waɗanda aka ɗaukaka. 11 Ko da yake malaꞌiku sun fi su ƙarfi da kuma iko, malaꞌikun ba sa kawo zargi a kansu ta wurin amfani da zagi, domin suna daraja Jehobah.* 12 Amma mutanen nan ba sa tunani, suna yin abin da jikinsu ya gaya musu ne kawai, kamar dabbobi waɗanda aka haifa ne don a kama a kashe, suna zagi a kan abubuwan da ba su sani ba. Abubuwa marasa kyau da suke yi zai jawo musu hallaka, 13 ladan da za su samu ke nan don abubuwa marasa kyau da suka yi.

A ganinsu, jin daɗi ne idan mutum ya yi duk abin da jikinsa yake so, ko da ya yi hakan da rana ne. Sun zama tabo da kuma abin zargi a gare ku saꞌad da suke liyafa tare da ku, suna jin daɗin yaudarar mutane da koyarwar ƙarya. 14 Idanunsu suna cike da zina kuma ba sa iya guje wa yin zunubi, suna kuma rinjayar marasa ƙarfi. Zukatansu a cike suke da haɗama. Su laꞌanannun yara ne. 15 An ruɗe su, kuma suka daina bin hanya mai kyau. Sun bi hanyar Balam ɗan Beyor, wanda yake son ladan aikin mugunta, 16 amma an tsawata masa domin ya ƙi yin abin da ya dace. Jaki da ba ya yin magana ya yi magana da muryar mutum don ya hana annabin yin abin da bai dace ba.

17 Suna kama da maɓuɓɓugar ruwa waɗanda babu ruwa a ciki, kamar hazo da iska mai ƙarfi yake jujjuyawa, kuma an shirya musu wuri mai duhu sosai a matsayin wurin zama. 18 Suna yin maganganu masu daɗin ji amma marasa amfani. Ta wurin bin shaꞌawoyin jikinsu, da kuma yin ayyukan rashin kunya,* suna ruɗin waɗanda ba su daɗe da kuɓucewa daga mutanen da suke yin rayuwar zunubi ba. 19 Malaman ƙaryan suna yi musu alkawarin ꞌyanci, amma su da kansu bayi ne na zunubi; domin duk wanda ya shawo kan wani mutum, mutumin ya zama bawansa* ke nan. 20 Hakika, idan mutane sun iya kuɓuce ma ayyukan ƙazanta na duniya ta wurin cikakken ilimi game da Ubangiji da Mai Cetonmu Yesu Kristi, amma suka sake komawa ga abubuwan nan, kuma suka bar abubuwan su sha kansu, hakan yana nufin cewa yanayinsu na ƙarshe ya fi na farko muni. 21 Da zai fi musu kyau idan ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, maimakon a ce bayan sun sani su juya baya ga dokoki masu tsarki da aka ba su. 22 Abin da suka yi ya yi daidai da karin maganar nan cewa: “Kare ya koma ya lashe amansa, kuma aladen da aka masa wanka ya koma birgima a cikin taɓo.”

3 Ya ku ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙata ta biyu zuwa gare ku, kuma kamar yadda na yi a wasiƙata ta farko, ina tuna muku da abubuwan da kuka riga kuka sani domin su taimaka muku ku yi tunanin da ya dace, 2 kuma ku tuna da abubuwan da annabawa masu tsarki suka faɗa a dā da dokokin da Ubangiji da Mai Cetonmu ya ba ku ta wurin manzanninku. 3 Da farko dai, ku sani cewa a kwanakin ƙarshe masu baꞌa za su zo su yi baꞌa, kuma za su yi abubuwa yadda suka ga dama 4 suna cewa: “Ba ya yi alkawari cewa zai dawo ba, to, ina yake? Domin tun lokacin da kakanninmu suka mutu, abubuwa sun ci-gaba da kasancewa daidai yadda suke tun lokacin da Allah ya fara halitta.”

5 Gama, da gangan ne suka yi watsi da wannan gaskiyar cewa sama ta kasance tun da daɗewa, kuma ta wurin kalmar Allah ce aka yi duniya daga cikin ruwa, duniyar kuwa ta kafu sosai a cikin ruwa; 6 kuma da ruwan ne aka hallaka duniya ta wancan lokaci saꞌad da ruwan ya mamaye ta. 7 Amma ta wurin kalmar nan, sama da ƙasa da suke nan a yanzu suna jira a hallaka su da wuta, kuma an ajiye su har zuwa ranar shariꞌa da kuma ranar da za a hallaka mutane marasa tsoron Allah.

8 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku manta da wannan, cewa rana ɗaya a wurin Jehobah* kamar shekaru dubu ne a wurinmu, shekaru dubu kuma, kamar rana ɗaya ce a wurin sa. 9 Jehobah* ba ya ɓata lokaci wajen cika alkawarinsa, kamar yadda wasu suke tsammani, amma yana haƙuri da ku ne domin ba ya so wani ya hallaka, sai dai yana so kowa ya tuba. 10 Amma ranar Jehobah* za ta zo kamar ɓarawo, a ranar, sammai za su shuɗe da ƙara mai ƙarfi, abubuwan da suke cikin sama da duniya za su narke saboda tsananin zafi kuma duniya da abubuwan da ke cikinta za su bayyana.*

11 Tun da yake dukan abubuwan nan za su narke haka, ku yi tunanin irin mutanen da ya kamata ku zama da zai nuna cewa kuna da halaye masu tsarki kuma kuna yin ibada da dukan zuciyarku, 12 yayin da kuke jira kuma kuke marmarin zuwan ranar Jehobah,* domin a ranar ce za a hallaka sama da wuta, kuma abubuwan da suke cikin sama da duniya za su narke saboda tsananin zafi! 13 Amma akwai sababbin sammai da sabuwar duniya da muke jira waɗanda Allah ya yi mana alkawarin su, kuma za a riƙa yin adalci a cikinsu.

14 Saboda haka, ƙaunatattuna, tun da yake kuna jiran abubuwan nan, ku yi iya ƙoƙarinku domin a ƙarshe ya same ku a matsayin marasa tabo, marasa laifi, kuma cikin salama. 15 Ƙari ga haka, ku ɗauki haƙurin da Ubangijinmu yake yi a matsayin ceto, kamar yadda ƙaunataccen ɗanꞌuwanmu Bulus ma ya rubuta muku bisa ga hikimar da aka ba shi, 16 ya yi magana a kan abubuwan nan a cikin dukan wasiƙunsa. Amma, wasu abubuwa a cikinsu suna da wuyar fahimta, kuma abubuwan nan ne marasa ganewa da marasa ƙarfi cikin bangaskiya suke juya maꞌanarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, kuma hakan zai kai su ga hallaka.

17 Saboda haka, ƙaunatattuna, da yake kun san abubuwan nan kafin su faru, sai ku lura don kada koyarwar ƙarya ta masu mugunta ta sa ku bijire kuma ku bar hanya mai kyau. 18 A maimakon haka, ku ci-gaba da girma cikin alheri da ilimin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kristi. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi yanzu da kuma har abada. Amin.

Wato, jikinsa.

Ko kuma “halayensu na rashin kunya.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ko kuma “halayensu na rashin kunya.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ko kuma “ransa ya yi baƙin ciki.” A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “halayen rashin kunya.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ko kuma “duk wanda wani abu ya sha kansa ya zama bawan abin.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Maꞌana “Ba za su samu kāriya daga wuta ba.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba