Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Janairu pp. 8-13
  • Jehobah Zai Iya Taimaka Maka Idan Ka Yi Sanyin Gwiwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Zai Iya Taimaka Maka Idan Ka Yi Sanyin Gwiwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABUBUWAN DA SUKA SA BULUS SANYIN GWIWA
  • MENE NE BULUS YA YI A LOKACIN DA YA YI SANYIN GWIWA?
  • ABUBUWAN DA ZA MU IYA YI IDAN MUKA YI SANYIN GWIWA
  • MUNA DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MANA KUMA ZAI ALBARKACE MU
  • Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Janairu pp. 8-13

9-15 GA MARIS 2026

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani A Kai

Jehobah Zai Iya Taimaka Maka Idan Ka Yi Sanyin Gwiwa

“Kaitona!”—ROM. 7:24.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da za mu iya yi idan muka yi sanyin gwiwa.

1-2. Yaya manzo Bulus ya ji a wasu lokuta, kuma ta yaya yadda ya ji ya yi kama da yadda muke ji a yau? (Romawa 7:​21-24)

A YAWANCI lokuta, idan muka yi tunani game da manzo Bulus mukan tuna cewa ya yi waꞌazi da ƙwazo a ƙasashe da yawa, ya rubuta littattafai dabam-dabam a Littafi Mai Tsarki, kuma shi malami ne da ya iya koyarwa sosai. Babu shakka, shi mutum mai aminci da kuma ƙarfin zuciya ne. Duk da haka, a wasu lokuta ya yi sanyin gwiwa da kuma baƙin ciki.

2 Karanta Romawa 7:​21-24. A wasiƙar da Bulus ya rubuta zuwa ga Romawa, ya bayyana wasu abubuwan da ke damunsa. Da yawa daga cikinmu a yau muna fama da irin waɗannan abubuwan. Ko da yake Bulus Kirista ne mai aminci kuma yana son ya riƙa yin abubuwan da Jehobah yake so, ya yi fama da ajizanci. Kuma hakan ya sa ya yi masa wuya ya yi abin da Jehobah yake so. Ban da haka ma, Bulus yakan yi baƙin ciki sosai idan ya yi tunani a kan abubuwan da ya yi kafin ya zama Kirista. Kuma a wasu lokuta, yakan yi baƙin ciki sosai don wata matsala a rayuwarsa da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

3 Ko da yake a wasu lokuta Bulus ya yi sanyin gwiwa, ya yi ƙoƙari sosai don kada ya riƙa mai da hankali a kan abubuwan da suke sa shi baƙin ciki ko damuwa.a A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyin nan: Waɗanne abubuwa ne suka sa manzo Bulus sanyin gwiwa? Me ya taimaka wa Bulus kada ya ci-gaba da yin tunani a kan abubuwan da suke sa shi sanyin gwiwa? Kuma me za mu iya yi idan muka yi sanyin gwiwa?

ABUBUWAN DA SUKA SA BULUS SANYIN GWIWA

4. Waɗanne abubuwa ne suka sa Bulus sanyin gwiwa?

4 Abubuwan da ya yi a dā. Kafin Bulus ya zama Kirista, ya yi munanan abubuwa da yawa. Alal misali, da goyon bayansa ne aka kashe Istifanus. (A. M. 7:58; 8:1) Ƙari ga haka, ya tsananta kuma ya wulaƙanta Kiristoci da yawa.—A. M. 8:3; 26:​9-11.

5. Yaya Bulus ya ji don abubuwan da ya yi a dā?

5 Bayan da Bulus ya zama Kirista, abubuwan da ya yi a dā sun ci-gaba da sa shi baƙin ciki. Duk da cewa da shigewar lokaci ya zama Kiristan da ya manyanta, abubuwan nan sun ci-gaba da sa shi baƙin ciki. Alal misali, saꞌad da ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korintiyawa a wajen shekara ta 55 bayan haihuwar Yesu, ya ce: “Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikilisiyar Allah.” (1 Kor. 15:9) Wajen shekaru biyar bayan haka, saꞌad da ya rubuta wasiƙa zuwa ga Afisawa, ya ce shi ne mafi “ƙanƙanta cikin tsarkaka.” (Afis. 3:8) Kuma a wasiƙar da ya rubuta wa Timoti ya ce: “Ni mai saɓon Allah ne” kuma ina tsananta da wulaƙanta bayinsa. (1 Tim. 1:13) Babu shakka, Bulus zai yi baƙin ciki sosai, saꞌad da ya haɗu da ꞌyanꞌuwan da ya tsananta musu a dā ko kuma iyalansu.

6. Wane abu ne kuma ya sa Bulus damuwa sosai? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

6 Wani abin da ya sa shi damuwa sosai. Bulus ya ce ya yi fama da wani abin da ya zama masa kamar “ƙaya a jiki.” (2 Kor. 12:7) Bulus bai ambata ainihin abin da ke damunsa ba, mai yiwuwa wata cuta ce ko kuma wata matsala ce dabam.b

7. Me ya sa yin abubuwa masu kyau ya yi wa Bulus wuya? (Romawa 7:​18, 19)

7 Ajizancinsa. Bulus ya yi kurakurai da yawa. Babu shakka, hakan ya sa shi sanyin gwiwa. Amma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ci-gaba da yin abubuwan da suka dace. (Karanta Romawa 7:​18, 19.) Duk da cewa yana iya ƙoƙarinsa don ya yi abubuwa masu kyau, a wasu lokuta yana yin abubuwan da ba ya so ya yi. Ya ce, a kowane lokaci yana ƙoƙari don kada ya yi abin da zuciyarsa take so ya yi. (1 Kor. 9:27) Duk da haka, ya yi kurakurai. Wannan ba ƙaramin baƙin ciki zai sa Bulus ya yi ba.

MENE NE BULUS YA YI A LOKACIN DA YA YI SANYIN GWIWA?

8. Waɗanne abubuwa ne Bulus ya yi da suka taimaka masa ya kasance da halayen kirki?

8 Daga wasiƙun da Bulus ya rubuta, mun gano cewa Bulus ya yi tunani mai zurfi a kan yadda ruhun Allah zai taimaka wa shi da ꞌyanꞌuwansa Kiristoci su daina tunanin da ba su dace ba, kuma su kasance da halayen kirki. (Rom. 8:13; Gal. 5:​16, 17) Bulus ya ambata halaye da ayyuka da Kiristoci suke bukata su guje wa don su faranta wa Allah rai. (Gal. 5:​19-21, 26) Abubuwan da Bulus ya rubuta sun nuna cewa ya yi tunani a kan abubuwan da yake bukata ya canja a rayuwarsa. Ya yi nazarin Kalmar Allah don ya san abin da zai yi da kuma yadda zai iya yin hakan. Babu shakka, Bulus da kansa ya bi shawarwarin da ya bayar.

9-10. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wa Bulus saꞌad da ya yi sanyin gwiwa? (Afisawa 1:7) (Ka kuma duba hoton.)

9 Ko da yake a wasu lokuta Bulus ya yi sanyin gwiwa, akwai abubuwa da yawa da suka sa shi farin ciki. Alal misali, labarai masu kyau game da ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyoyi dabam-dabam sun sa shi farin ciki. (2 Kor. 7:​6, 7) Wani abu kuma da ya sa shi farin ciki shi ne yin tarayya da ꞌyanꞌuwa. (2 Tim. 1:4) Ƙari ga haka, ya yi farin ciki don dangantaka da ya ƙulla da Jehobah da kuma sanin cewa Jehobah yana amincewa da shi. (2 Tim. 1:3) Har a lokacin da aka sa Bulus a kurkuku a Roma, ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa maza da mata cewa, “Ku yi farin ciki cikin Ubangiji kullum.” (Filib. 4:4) Abubuwan da Bulus ya faɗa sun nuna cewa, bai mai da hankali a kan matsalolinsa ko kurakuransa ba. Da zarar ya soma tunani a kan abubuwan da suke sa shi sanyin gwiwa, yakan kawar da su nan da nan kuma ya mai da hankali a kan abubuwan da suke sa shi farin ciki.

10 Wani abu kuma da ya taimaka wa Bulus ya kasance da farin ciki shi ne fansar Yesu. Ya tuna cewa Jehobah yana ƙaunar sa ne shi ya sa ya ba da fansar. (Gal. 2:20; karanta Afisawa 1:7.) Hakan ya sa ya kasance da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta masa zunubansa kuma zai ci-gaba da gafarta masa. (Rom. 7:​24, 25) Dukan waɗannan abubuwan sun taimaka wa Bulus ya ci-gaba da “bauta” wa Jehobah da farin ciki.—Ibran. 9:​12-14.

Hotuna: Na 1. Manzo Bulus yana tunani. Na 2. Ya tuna wani abin da ya faru shekarun baya, lokacin da ya sa aka jawo wani Kirista daga gidansa. Na 3. Yana tunani game da yadda aka kashe Yesu a kan gungume.

Ko da yake Bulus ya yi baƙin ciki sosai don abubuwan da ya yi a dā, yin tunani game da fansar Yesu ya taimaka masa (Ka duba sakin layi na 9-10)


11. Ta yaya labarin Bulus zai ƙarfafa mu?

11 Kamar Bulus, za mu iya ga kamar ba ya yi mana sauƙi mu yi tunani ko faɗa, ko kuma mu yi abin da Jehobah yake so. Hakan zai iya sa mu ga kamar ba za mu taɓa iya faranta wa Jehobah rai ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai shekaru 26 mai suna Elizac ta ce: “Yin tunanin a kan labarin manzo Bulus yana ƙarfafa ni. Ina farin cikin sanin cewa manzo Bulus ma ya yi wasu canje-canje a rayuwarsa kamar yadda ni ma nake bukatar yi. Wani abu kuma da labarinsa yake tuna mini shi ne, Jehobah ya san ƙasawa da bayinsa suke fama da su.” Kamar Bulus, me za mu iya yi don mu faranta wa Jehobah rai kuma mu kasance da farin ciki ko da mun yi sanyin gwiwa a wasu lokuta?

ABUBUWAN DA ZA MU IYA YI IDAN MUKA YI SANYIN GWIWA

12. Waɗanne abubuwan ne muke bukatar mu yi don mu ci-gaba da yin farin ciki?

12 Mu ci-gaba da yin abubuwan da za su sa mu kusaci Jehobah. Idan muna cin abinci masu gina jiki, muna motsa jiki kullum, kuma muna samun isasshen barci, hakan zai inganta lafiyar jikinmu. Haka ma, idan muna karanta Kalmar Allah kowace rana, da fita waꞌazi, da halartan taro, da yin shiri kafin mu halarci taro, da kuma yin kalami a taron, za mu riƙa mai da hankali a kan abubuwa masu kyau, maimakon a kan abubuwan da za su sa mu sanyin gwiwa. Kuma hakan zai sa mu farin ciki.—Rom. 12:​11, 12.

13-14. Ta yaya wasu ꞌyanꞌuwa suka amfana saꞌad da suka ci-gaba da yin abubuwan da za su sa su kusaci Jehobah?

13 Ka yi laꞌakari da labarin Ɗanꞌuwa John da aka gano cewa yana da ciwon kansa a lokacin da yake shekaru 39. Da farko ya ji tsoro kuma ya damu sosai. Ya yi mamaki da ya kamu da irin wannan cutar a lokacin a rayuwarsa. A lokacin, ɗansa yana shekara uku ne kawai. Mene ne ya taimaka wa John kada ya damu sosai? Ya ce, “Ciwon yana sa ni gajiya sosai, amma na yi iya ƙoƙarina wajen tabbata cewa dukanmu a iyali muna halartan taro, muna fita waꞌazi kuma muna yin ibada ta iyali kowane mako. Muna yin waɗannan abubuwan duk da cewa hakan bai da sauƙi.” Ɗanꞌuwa John ya ƙara da cewa, “Mai yiwuwa abu na farko da za mu yi idan muka ga kanmu a cikin yanayin mai wuya shi ne baƙin ciki. Amma na koyi cewa, bayan hakan Jehobah zai ba mu ƙarfin da muke bukata, kuma zai tabbatar mana cewa yana ƙaunarmu. Jehobah zai taimaka maka kamar yadda ya taimaka mini.”

14 ꞌYarꞌuwa Eliza da aka ambata ɗazu ta ce: “Halartan taro da yin nazarin Littafi Mai Tsarki suna tuna mini cewa Jehobah yana ƙauna ta kuma yana sauraro na, kuma hakan yana sa ni farin ciki.” Wani mai kula da daꞌira a Afirka mai suna Nolan, ya bayyana abin da yake taimaka wa shi da matarsa mai suna Diane. Ya ce, “Muna yin adduꞌa, da nazarin Littafi Mai Tsarki, da halartan taro, da kuma yin waꞌazi ko da mun yi sanyin gwiwa. Idan muka yi sanyin gwiwa, mukan tuna cewa Jehobah zai taimaka mana, kuma zai albarkace mu. Ko da yake ba mu san yadda zai yi hakan ba, muna da tabbaci cewa zai taimaka mana.”

15. Idan mun ci-gaba da yin sanyin gwiwa, waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu yi? Ka ba da misali.

15 Akwai wasu abubuwan da muke bukatar mu yi idan mun ci-gaba da yin sanyin gwiwa. Alal misali, a ce kana fama da ciwon baya, kana bukatar ka tashi ka ɗan zagaya kowace rana. Amma don bayanka ya daina maka ciwo kwata-kwata, kana bukatar ka gane abin da ya jawo ciwon bayan. Mai yiwuwa ka yi bincike kuma ka je wurin likita. Haka ma, idan mun ci-gaba da yin sanyin gwiwa, muna bukatar mu yi bincike a Littafi Mai Tsarki da littattafanmu, ko kuma mu nemi shawara daga wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ta manyanta. Ga wasu abubuwa kuma da za su iya taimaka mana.

16. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi da za su taimaka mana saꞌad da muke yawan damuwa? (Zabura 139:​1-4, 23, 24)

16 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka san abin da kake bukata. Sarki Dauda ya san cewa Jehobah ya san shi ciki da waje. Saboda haka, Dauda ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya san dalilin da ya sa yake yawan damuwa. (Karanta Zabura 139:​1-4, 23, 24.) Kai ma za ka iya roƙan Jehobah ya taimaka maka ka san dalilin da ya sa kake yawan damuwa da kuma abin da za ka yi don ka sami kwanciyar hankali. Za mu iya yi wa kanmu wasu tambayoyi kamar: ‘Mene ne asalin abin yake sa ni damuwa? Akwai wani abin da ke faruwa da yake tayar mini da hankali har in soma damuwa? Ina yawan mai da hankali a kan abubuwan da suke sa ni sanyin gwiwa maimakon abubuwan da za su sa ni farin ciki?’

17. Waɗanne batutuwa ne za mu iya yin nazari a kai da za su taimaka mana mu mai da hankali a kan abubuwan da za su ƙarfafa mu? (Ka kuma duba hoton.)

17 Ka riƙa bincika batutuwan da za su taimaka maka. A wasu lokuta, yana da kyau mu yi nazari a kan wasu halayen Jehobah da za su ƙarfafa mu. Alal misali, manzo Bulus ya amfana sosai saꞌad da ya yi tunani game da fansar Yesu da kuma yadda Jehobah yake gafarta mana. Kai ma za ka iya yin hakan. Za ka iya yin amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah, ko kuma talifofi da ke jw.org wajen yin bincike a kan halayen Allah, kamar su jinƙai, da gafartawa, da kuma ƙauna marar canjawa. Idan ka samu talifofin da za su taimaka maka, ka rubuta su a wani wuri. Kuma ka ajiye a wurin da za ka iya gani. Za ka iya sake yin nazarin talifofin idan ka soma yin sanyin gwiwa. Ka yi ƙoƙari ka bi shawarwarin da ke abubuwan da ka karanta don hakan zai taimaka maka ka ji sauƙi.—Filib. 4:8.

Wani saurayi ya zauna yana nazari. A gabansa akwai Littafi Mai Tsarki, da takarda, da kuma babbar waya. Yana rubutu a Littafi Mai Tsarkin.

Ka riƙa yin nazari a kan batutuwan da za su ƙarfafa ka (Ka duba sakin layi na 17)


18. Waɗanne batutuwa ne wasu ꞌyanꞌuwa suka yi nazari a kai?

18 ꞌYarꞌuwa Eliza da aka ambata ɗazu, ta yi bincike a kan labarin Ayuba. Ta ce, “Na yi fama da matsaloli da dama a lokaci guda. Hakan ya sa na bincika labarin Ayuba. Na ga cewa ya yi fama da matsaloli da yawa kuma ya yi sanyin gwiwa. Ko da yake bai san dalilin da ya sa yake shan wahala ba, ya ci-gaba da dogara ga Jehobah.” (Ayu. 42:​1-6) ꞌYarꞌuwa Diane da aka ambata ɗazu ta ce, “Ni da maigidana muna nazari da littafin nan Ka Kusaci Jehobah. Muna godiya sosai sanin cewa Jehobah yana taimaka mana mu iya yin koyi da shi. Idan muka yi sanyin gwiwa don kurakuran da muka yi, muna tuna cewa Jehobah yana koyar da mu kuma yana taimaka mana mu zama mutanen kirki. Hakan yana sa mu ƙara kusantar sa.”—Isha. 64:8.

MUNA DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MANA KUMA ZAI ALBARKACE MU

19. Ko da mun bi dukan shawarwarin da aka bayar a wannan talifin, me zai iya faruwa, kuma wane tabbaci ne muke da shi?

19 Ko da mun bi dukan shawarwarin da aka bayar a wannan talifin, hakan ba zai hana mu yin baƙin ciki ko damuwa a wasu lokuta ba. A wasu lokuta ma, za mu iya yin sanyin gwiwa sosai. Amma da taimakon Jehobah za mu iya rage yin tunani a kan abubuwan da suke sa mu yin sanyin gwiwa. Muna da tabbaci cewa a yawancin lokuta za mu ji daɗin rayuwarmu kuma mu yi farin ciki. Me ya sa? Domin mun san cewa muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma yana alfahari da abin da muke yi.

20. Mene ne ka ƙudura niyyar yi?

20 Kada mu bar matsalolinmu, da abubuwan da suka faru a rayuwarmu a dā, da kuma kurakuranmu su hana mu jin daɗin rayuwarmu. Da taimakon Jehobah za mu iya daina yawan damuwa. (Zab. 143:10) Muna marmarin ganin lokacin da dukan abubuwan da muke tunani a kai za su riƙa sa mu farin ciki. A lokacin, babu wani abin da zai sa mu damuwa. Kowace rana za mu tashi muna bauta wa Jehobah Allahnmu da farin ciki!

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne abubuwa ne suka sa manzo Bulus sanyin gwiwa a wasu lokuta?

  • Me ya taimaka wa Bulus ya ci-gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki duk da cewa yana baƙin ciki a wasu lokuta?

  • Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi idan muna baƙin ciki ko damuwa?

WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci

a A wannan talifin, ana magana ne game da mutanen da suke baƙin ciki ko damuwa a wasu lokuta. Ba game da waɗanda suke fama da tsananin damuwa na dogon lokaci ba, ko kuma waɗanda suke bukatar su ga likita ba.

b Mai yiwuwa Bulus ya yi fama da ciwon ido ne, kuma wataƙila hakan ya sa ya yi masa wuya ya rubuta wasiƙu da kansa zuwa ikilisiyoyi, da yin tafiye-tafiye da kuma yin waꞌazi. (Gal. 4:15; 6:11) Wataƙila kuma Bulus ya damu ne don abin da wasu malaman ƙarya suke faɗa game da shi. (2 Kor. 10:10; 11:​5, 13) Ko da yake ba mu san ainihin abin da ya sa Bulus damuwa ba, mun san cewa abin ya sa Bulus baƙin ciki a wasu lokuta.

c An canja wasu sunayen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba