KA SANI?
Majami’a a Ƙarni na Farko: A wannan hoton, an nuna wasu abubuwan da ke majami’a ta ƙarni na farko a birnin Gamla mai nisan mil shida daga arewa maso gabashin Kogin Galili. Hoton ya nuna yadda majami’u suke a zamanin dā
Ta yaya aka soma amfani da majami’a?
A HELENANCI, kalmar nan “majami’a” tana nufin “taro.” Sunan ya dace domin tun zamanin dā, Yahudawa suna yin taro a majami’unsu don ibada da kuma ilimantarwa. Ba a ambata majami’u a Nassosin Ibrananci ba, amma bayanan da muka gani a Nassosin Helenanci sun nuna cewa an daɗe ana amfani da su kafin ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu.
Yawancin marubuta sun gaskata cewa an soma amfani da majami’u a lokacin da aka kai Yahudawa zaman bauta a Babila. An ambata a littafin nan Encyclopædia Judaica cewa: “Da yake Yahudawa ba su da Haikali a Babila kuma suna bukatar ƙarfafa don ƙuncin da suke ciki, sai suka soma yin taro a kai a kai, mai yiwuwa a ranar Assabaci don su karanta Nassosi.” Babu shakka, bayan da suka koma ƙasarsu, sun ci gaba da yin taro don su yi addu’a tare kuma su karanta Nassosi. Yahudawa sun ci gaba da kafa majami’u a duk inda suke zama.
A ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu, majami’u sun riga sun zama tushen addinin Yahudawa da kuma abin da Yahudawa da ke kewaye da Bahar Maliya da Gabas ta Tsakiya da kuma Isra’ila suke amfani da shi. Wani Farfesan tarihin Yahudawa mai suna Lee Levine ya ce Yahudawa suna amfani da wuraren nan don yin nazari da cin abinci da yin shari’a da ajiyar kuɗi da taron siyasa da na zaman jama’a. Ya ƙara da cewa: “Abu na musamman da ake yi a wuraren nan shi ne ibada.” Shi ya sa Yesu yake yawan halartan taro a majami’a a zamaninsa. (Mar. 1:21; 6:2; Luk. 4:16) A nan ne yake koyar da mutane, ya umurce su kuma ya ƙarfafa su. Bayan da aka kafa ikilisiyar Kirista, manzo Bulus ma ya yi wa’azi sau da yawa a majami’u. Mutanen da suke so su ƙulla dangantaka da Allah suna yawan zuwa majami’a. Shi ya sa a duk lokacin da manzo Bulus ya shiga wani birni, wurin da yake fara zuwa yin wa’azi shi ne majami’a.—A. M. 17:1, 2; 18:4.