Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w19 Fabrairu pp. 26-30
  • Yadda Aka Rene Ni Ya Sa In Sami Ci Gaba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Aka Rene Ni Ya Sa In Sami Ci Gaba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IYAYENMU SUNA ƘAUNARMU
  • SA’AD DA MUKE GIRMA
  • HIDIMA MAI ƘAYATARWA A NAJERIYA
  • MUN SOMA WATA HIDIMA
  • Jehobah Ya Kiyaye Ni don Na Dogara Gare Shi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
w19 Fabrairu pp. 26-30
Woodworth Mills

TARIHI

Yadda Aka Rene Ni Ya Sa In Sami Ci Gaba

Woodworth Mills ne ya ba da labarin

MUN kai gaɓar Kogin Niger da tsakar dare, kogin na da girma sosai kuma faɗinsa ya kusan mil ɗaya. A lokacin ana Yaƙin Basasa a Najeriya, saboda haka, haye kogin yana da haɗari sosai. Duk da haka, mun haye kogin sau da yawa. Yaya na sami kaina cikin wannan yanayin? Bari in gaya muku abin da ya faru kafin a haife ni.

Mahaifina John Mills ya yi baftisma yana ɗan shekara 25, a birnin New York a shekara ta 1913. Ɗan’uwa Russell ne ya yi jawabin baftismarsa. Jim kaɗan bayan haka, mahaifina ya koma ƙasar Trinidad. A wurin ne, ya auri Constance Farmer, wata Ɗalibar Littafi Mai Tsarki mai ƙwazo sosai. Mahaifina ya taimaka wa abokinsa William R. Brown ya nuna fim ɗin nan “Photo-Drama of Creation.” Sun yi hakan har sai lokacin da aka tura Ɗan’uwa Brown da iyalinsa zuwa Yammacin Afirka a 1923. Amma, mahaifina da mahaifiyata da suke da begen zuwa sama sun ci gaba da hidima a ƙasar Trinidad.

IYAYENMU SUNA ƘAUNARMU

Iyayenmu suna da yara tara, sunan ɗan fari Rutherford ne, an ba yayana sunan nan domin a lokacin, Ɗan’uwa Rutherford ne shugaban Watch Tower Bible and Tract Society. Da aka haife ni a ranar 30 ga Disamba, 1922, an ba ni suna Woodworth domin Ɗan’uwa Clayton J. Woodworth ne editan The Golden Age da ake kira Awake! a yau. Iyayenmu sun tura mu makaranta, amma sun ƙarfafa mu mu kafa maƙasudai a hidimar Jehobah. Mahaifiyata ta iya bayyana Nassosi sosai. Mahaifina yakan gaya mana labaran Littafi Mai Tsarki, kuma yakan yi kwaikwayon mutanen da muke karanta labarinsu.

Allah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcensu sosai don maza uku cikin yara tara sun je Makarantar Gilead. Ƙari ga haka, ’yan’uwanmu mata uku sun yi hidimar majagaba shekaru da yawa a ƙasar Trinidad and Tobago. Koyar da mu sosai da kuma kafa mana misali mai kyau, ya taimaka mana mu kasance a “gidan Yahweh.” Yadda iyayenmu suka ƙarfafa mu ya taimaka mana mu ci gaba da hidima kuma mu sami ci gaba “a cikin gidan Allahnmu.”​—Zab. 92:13.

Ana taron fita wa’azi a gidanmu. Majagaba sukan taru a wurin kuma sau da yawa suna magana game da Ɗan’uwa George Young, wani ɗan Kanada mai wa’azi a ƙasar waje da ya ziyarci ƙasar Trinidad. Iyayenmu suna farin ciki sa’ad da suke magana game da abokan hidimarsu a dā wato iyalin Brown waɗanda a lokacin suna hidima a Yammacin Afirka. Hakan ya ƙarfafa ni in soma wa’azi sa’ad da nake ɗan shekara goma.

SA’AD DA MUKE GIRMA

A lokacin, ana yawan fallasa addinin ƙarya da ’yan talla masu hadama da kuma ’yan siyasa masu cin hanci a littattafanmu. Saboda haka a shekara a 1936, limamai sun sa shugaban Trinidad ya hana mu rarraba littattafanmu. Mun ɓoye littattafanmu kuma muka ci gaba da yin amfani da su har suka ƙare. Mukan rataye fosta a wuya yayin da muke tuƙa kekuna ko kuma takawa a kan titi muna rarraba warƙoƙi. Da mu da wani rukuni da ke garin Tunapuna, mukan yi amfani da mota mai lasifika don mu yi wa’azi har a wurare masu nisa a ƙasar Trinidad. Mun ji daɗin wannan wa’azin sosai! Kuma hakan ya ƙarfafa ni in yi baftisma sa’ad da nake ɗan shekara 16.

’Yan’uwa a Tunapuna kusa da mota mai lasifika

’Yan’uwa a Tunapuna kusa da mota mai lasifika

Yadda iyalinmu suka sa bautar Allah a gaba da kuma wa’azi da muka yi a wasu wurare ya sa in soma sha’awar yin wa’azi a ƙasar waje. Shi ya sa na je tsibirin Aruba a 1944 don yin hidima tare da Ɗan’uwa Edmund W. Cummings. Mun yi farin ciki sa’ad da mutane goma suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a 1945. An kafa ikilisiya ta farko a tsibirin a 1946.

Oris da Woodworth Mills a lokacin da suke matasa

Ni da matata Oris mun ji daɗin zama tare

Jim kaɗan bayan haka, sai na yi wa’azi ga wata abokiyar aikina mai suna Oris Williams. Oris ta nemi ta kāre imaninta, amma yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa ta koyi gaskiya kuma ta yi baftisma a ranar 5 ga Janairu 1947. Da shigewar lokaci, muka soma fita zance kuma muka yi aure. Ta soma hidimar majagaba a watan Nuwamba 1950. Na soma jin daɗin rayuwa a wata hanya sa’ad da na aure ta.

HIDIMA MAI ƘAYATARWA A NAJERIYA

An gayyace mu mu je Makarantar Gilead a 1955. Don mu je wannan makarantar, ni da matata muka yi murabus daga aikinmu, muka sayar da gidanmu da kayayyakinmu kuma muka bar tsibirin Aruba. Mun sauke karatu a aji na 27 a ranar 29 ga Yuli a 1956, kuma aka tura mu hidima a Najeriya.

Woodworth da Oris Mills tare da iyalin Bethel a Legas, Nigeria, a 1957

Tare da iyalin Bethel a Legas, Najeriya, a 1957

Matata Oris ta ce: “Ruhun Jehobah yana taimaka wa mutum ya jimre da matsaloli da ke tattare da yin hidima a wata ƙasa. Mijina yana son yin hidima a wata ƙasa, amma ni ba na so. Na fi so mu gina gida kuma mu haifi yara, amma na canja ra’ayina sa’ad da na ga cewa ana bukatar a yi wa’azi da gaggawa. Na ƙuduri niyyar yin hidima a wata ƙasa sa’ad da muka sauke karatu daga Gilead. Sa’ad da muka shiga jirgin ruwa mai suna Queen Mary, sai Ɗan’uwa Worth Thornton da ke aiki a ofishin Ɗan’uwa Knorr ya yi mana ban-kwana. Ƙari ga haka, ya gaya mana cewa za mu yi hidima a Bethel. Ba na son yin hidima a Bethel, amma na canja ra’ayina kuma na ji daɗin yin hidima dabam-dabam a Bethel. Na fi jin daɗin yin aiki a wurin da ake marabtar baƙi. Ina son mutane, kuma wannan aikin ya sa na san ’yan’uwa a Najeriya sosai. ’Yan’uwa da yawa sukan isa Bethel a gajiye, suna jin ƙishirwa da yunwa. Na yi farin cikin ba su abinci da kuma biyan bukatunsu. Yin hakan hidima ce ga Jehobah, kuma ya sa na sami gamsuwa da farin ciki.” Hakika, kowace hidima tana sa mu sami ci gaba.

Sa’ad da iyalinmu suka yi wata liyafa a Trinidad a 1961, Ɗan’uwa Brown ya ba da labarai masu ƙayatarwa game da Afirka. Ni kuma na faɗa yadda muke samun ƙaruwa sosai a Najeriya. Sai Ɗan’uwa Brown ya ɗora hannu a kafaɗa na kuma ya gaya wa mahaifina: “Johnny ba ka taɓa zuwa Afirka ba, amma Woodworth ya je!” Mahaifina kuma ya ce: “Ka ci gaba ɗana! Ka ci gaba da ƙoƙari!” Irin wannan ƙarfafa daga ’yan’uwa da suka daɗe suna bauta wa Jehobah ya sa na ƙara yin ƙwazo a hidimata.

Woodworth Mills da Antonia Brown da William “Bible” Brown da kuma Oris Mills

William “Bible” Brown da matarsa Antonia, sun ƙarfafa mu sosai

A 1962, na sami gatar samun ƙarin horarwa na wata goma a aji na 37 a makarantar Gilead. Ɗan’uwa Wilfred Gooch da ke kula da ofishin Shaidun Jehobah a Najeriya ya je aji na 38 kuma aka tura shi hidima a Ingila. Hakan ya sa na sami gatar kula da ofishinmu da ke Najeriya. Na bi misalin Ɗan’uwa Brown kuma na yi tafiye-tafiye sosai a Najeriya, hakan ya sa na san ’yan’uwa sosai a Najeriya kuma na ƙaunace su. ’Yan’uwan suna farin ciki sosai duk da cewa ba su da kayan zamani da mutane da suke ƙasashen da suka bunƙasa suke da shi. Hakan ya nuna cewa mutum zai iya yin farin ciki a rayuwa ko da ba shi da kuɗi ko abin duniya. Duk da yanayinsu, sukan zo taro sanye da kaya masu tsabta. Sa’ad da dukansu suka zo taron yanki, mutane da yawa cikinsu sukan shiga manyan motoci da bas da ake kira bolekajas.a Sau da yawa akan rubuta abubuwa dabam-dabam a waɗannan motocin. A wani bas an rubuta: “Little drops of water make a mighty ocean,” wato da yayyafi kogi kan cika.

Abin da aka rubuta a wannan bas gaskiya ne! Aikin da ni da matata muka yi, haɗe da na ’yan’uwanmu a Najeriya ya taimaka sosai. A 1974, Najeriya ta zama ƙasa ta biyu da ta sami masu shela 100,000. Amirka ce ƙasa ta farko. Hakika an sami ci gaba!

Ko da yake an yi Yaƙin Basasa a Najeriya daga 1967 zuwa 1970, an sami ƙaruwa sosai a lokacin. Watanni da yawa, ’yan’uwanmu da suke gefen Biafra da ke ketaren Kogin Niger ba su iya cuɗanya da ’yan’uwa da ke ofishinmu ba. Saboda haka, muna da hakkin kai musu littattafai da kuma yi musu ja-goranci. Kamar yadda na ambata ɗazu, Jehobah ya taimaka mana mu haye kogin sau da yawa.

Na tuna tafiye-tafiye masu haɗari da muka yi sa’ad da muke ƙetare kogin Niger, mun fuskanci sojoji masu saurin harbi da cututtuka da dai sauransu. Yana da wuya sosai mu ƙetare yankin da akwai sojojin gwamnati, amma ya fi ban-tsoro mu ƙetare gefen ’yan Biafra. Akwai lokacin da na haye Kogin Niger da ruwan ke gudu sosai da kwalekwale daga garin Asaba zuwa birnin Anaca kuma muka wuce zuwa Enugu don mu ƙarfafa dattawan da suke wurin. Akwai wata tafiya da muka yi don mu ƙarfafa dattawan da ke Aba kuma a birnin an haramta kunna wuta daddare don kada sojojin gwamnati su gan su. A birnin Fatākwal, mun hanzarta rufe wani taro da addu’a sa’ad da sojojin gwamnati suka shigo ɓangaren ’yan Biafra ƙarfi-da-yaji.

Yana da muhimmanci a yi waɗannan taron a wannan lokacin don a tabbatar wa ’yan’uwanmu cewa Jehobah yana ƙaunarsu. Ban da haka, an gargaɗe su kada su saka hannu a yaƙi amma su kasance da haɗin kai. ’Yan’uwa a Najeriya sun yi nasara da suka jimre da wannan yanayin. Sun ƙaunaci juna sosai duk da cewa sun fito daga ƙabilu dabam-dabam kuma sun kasance da haɗin kai. Mun yi farin ciki kasancewa tare da su a wannan mawuyacin lokaci!

A 1969, Ɗan’uwa Milton G. Henschel ne mai kujerar taron ƙasashe da aka yi a filin wasan Yankee da ke New York. Jigon taron shi ne “Peace on Earth,” wato Salama a Duniya kuma ni ne mataimakinsa. Na sami wannan horarwa a lokacin da ya dace don mun yi taron ƙasashe a birnin Legas da ke Najeriya a 1970. Jigon taron shi ne “Men of Goodwill,” wato Mutane masu Nagarta. Jehobah ne ya taimaka mana muka yi nasarar yin wannan taron da yake ba a daɗe da gama yin yaƙin basasa ba. Taro ne mai ban al’ajabi domin an yi shi cikin harsuna 17 kuma mutane 121,128 ne suka halarta. Ɗan’uwa Knorr da Henschel da kuma wasu baƙi sun yi hayar jirgin sama da suka zo taron da shi daga Amirka da kuma Ingila. Sun ga mutane 3,775 da suka yi baftisma kuma wannan adadi ne mafi yawa tun lokacin Fentakos! Na shagala da aiki sosai sa’ad da muka shirya wannan taron. Adadin masu shela ya bunƙasa sosai fiye da sauran ƙasashe!

Taron kasashe mai jigo “Men of Goodwill,” da aka yi a Legas, Nigeria, a 1970

Mutane 121,128 ne suka halarci taron ƙasashe mai jigo “Men of Goodwill,” kuma an yi taron a yaruka 17 har a yaren Ibo

Mun yi hidima a Najeriya fiye da shekara 30, kuma na ji daɗin yin hidimar mai kula mai ziyara a wasu lokuta da kuma hidimar mai ziyarar ofishin Shaidun Jehobah a Yammacin Afirka. Masu hidima a ƙasashen sun yi farin ciki cewa ana ƙarfafa su kuma ana kula da su. Ƙari ga haka, sun yi murna da aka tabbatar musu da cewa ba a manta da su ba. Wannan aikin ya koya mini cewa nuna wa mutane ka damu da su zai taimaka musu su sami ci gaba. Bugu da ƙari, zai sa ’yan’uwa a ƙungiyar Jehobah su kasance da haɗin kai.

Jehobah ne ya taimaka mana mu jimre da yaƙin da kuma rashin lafiya. Mun ga cewa Jehobah yana yi mana albarka a kowane lokaci. Oris ta ce:

“Mun yi zazzaɓin cizon sauro sau da yawa. Akwai lokacin da mijina ya sume kuma aka kai shi asibiti a Legas. Sai aka gaya mini cewa wataƙila ba zai farfaɗo ba, amma mun yi farin ciki cewa ya sami lafiya! Sa’ad da ya farfaɗo, sai ya yi wa nas da ke kula da shi wa’azi game da Mulkin Allah. Daga baya, ni da mijina muka kai wa wannan nas mai suna Mista Nwambiwe ziyara don ya nuna yana son saƙon Littafi Mai Tsarki. Ya soma bauta wa Jehobah kuma daga baya ya zama dattijo a birnin Aba. Ni ma na yi nasarar taimaka wa mutane da yawa har da Musulmai su soma bauta wa Jehobah. Muna farin ciki sosai cewa mun san ’yan’uwanmu da ke Najeriya da al’adunsu da kuma yarensu.”

Na koyi wani darassi: Don mu yi farin ciki a hidimarmu a wata ƙasa, wajibi ne mu ƙaunaci ’yan’uwanmu ko da al’adarsu dabam ne da tamu.

MUN SOMA WATA HIDIMA

Bayan mun yi hidima shekaru da yawa a Bethel da ke Najeriya, an tura mu yin wa’azi a tsibirin St. Lucia a Karibiya a shekara ta 1987. Mun ji daɗin hidima a wurin amma mun fuskanci wani ƙalubale. A Afirka maza sukan auri mata da yawa, amma a nan St. Lucia, matsalar ita ce namiji da ta mace sukan yi zaman daduro. Kalmar Allah ta taimaka wa ɗalibanmu da yawa su yi canje-canje a rayuwarsu.

Woodworth da Oris Mills

Ina bala’in ƙaunar matata Oris a dukan shekaru 68 da muka zauna tare

Da yake mun soma tsufa, ba mu da ƙarfi kamar dā. Don haka a shekara ta 2005, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ce mu koma hidima a hedkwatarmu da ke Brooklyn a jihar New York, Amirka. A kowace rana, ina gode wa Jehobah don matata Oris. A shekara ta 2015 matata ta rasu kuma har yanzu ina baƙin ciki sosai. Matata tana da halaye masu kyau. Ina bala’in ƙaunar ta a dukan shekaru 68 da muka zauna tare. Mun fahimci cewa abin da ke kawo farin ciki a aure da kuma a ikilisiya shi ne daraja waɗanda ke ja-goranci da gafartawa da nuna tawali’u da kuma kasance da halayen da ruhu mai tsarki ke haifarwa.

A duk lokacin da muka karaya, muna dogara ga Jehobah ya taimaka mana mu ci gaba da bauta masa. Da muka ci gaba da yin canje-canje a rayuwa, hakan ya taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali, kuma a nan gaba za mu more rayuwa!​—Isha. 60:17; 2 Kor. 13:11.

Jehobah ya albarkaci aikin da iyayena da kuma wasu ’yan’uwa suka yi a ƙasar Trinidad and Tobago. Rahoto da aka ba da kwanan nan ya nuna cewa mutane 9,892 sun soma bauta wa Jehobah a ƙasar. A tsibirin Aruba kuma, ’yan’uwa da yawa sun yi ƙoƙari don su ci gaba da tallafa wa ikilisiya ta farko a wurin. Yanzu akwai ikilisiyoyi guda 14 a tsibirin. A Najeriya kuma, adadin masu shela ya ƙaru sosai, kuma yanzu mutane 381,398 ne suke bauta wa Jehobah. A tsibirin St. Lucia mutane 783 ne ke goyon bayan Mulkin Allah.

A yau, na wuce shekaru 90. Littafin Zabura 92:14 ya yi magana game da waɗanda suke bauta wa Jehobah cewa: “A tsufarsu za su yi ta ba da ’ya’ya, kullum ɗanye suke, cike da ruwa.” Ina farin ciki sosai don hidimar da na yi wa Jehobah. Yadda iyayena suka rene ni ya taimaka mini in bauta masa. Da yake Jehobah mai aminci ne, ya sa na sami ci gaba a ‘cikin Gidansa.’​—Zab. 92:13.

a Ka duba Awake! na 8 ga Maris, 1972, shafuffuka na 24-26.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba