Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 12/15 pp. 3-5
  • Jehobah Ya Kāre Su a Cikin Inuwar Duwatsu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Kāre Su a Cikin Inuwar Duwatsu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • TA HANYOYIN ’YAN SUMOGA
  • “TAFIYAR SHAƘATAWA” MAI HAƊARI
  • DARASIN DA MUKA KOYA
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 12/15 pp. 3-5

Jehobah Ya Kāre Su A Cikin Inuwar Duwatsu

SA’AD DA wata mata ta fito waje da sassafe, sai ta ga wani ƙunshi a bakin ƙofarsu. Ta ɗauki ƙunshin kuma ta duba ta ga ba kowa a titin. Babu shakka, wani ne ya ajiye ƙunshin a wurin daddare. Da ta ɗan buɗe ƙunshin, sai ta koma cikin ɗakinta da wuri kuma ta rufe ƙofa. Littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da gwamnati ta hana amfani da su ne ke cikin ƙunshin. Da ta rungumi ƙunshin, sai ta yi addu’a a zuciyarta, ta gode wa Jehobah don waɗannan littattafai masu tamani.

Irin waɗannan yanayin sun faru ne a ƙasar Jamus a shekara ta 1930 zuwa 1939. A shekara ta 1933 da gwamnatin Nazi ta soma sarauta, an dakatar da ayyukan Shaidun Jehobah a yawancin ɓangarorin ƙasar. Wani ɗan’uwa mai suna Richard Rudolph da ya ba shekaru 100 baya yanzu,a ya ce: “Mun kasance da tabbaci cewa babu ɗan Adam da zai iya hana mu sanar da mutane game da Jehobah da kuma sunansa. Muna amfani da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki wajen yin nazari da kuma wa’azi. Amma, hanin da gwamnati ta yi ya sa mun yi ƙaranci waɗannan littattafan. Muna tunanin yadda aikin zai ci gaba.” Daga baya, Richard ya fahimci cewa zai iya taimakawa a wata hanya dabam, amma hakan zai yi wuya sosai. Me ya sa? Domin za a yi shi a cikin inuwar duwatsu.—Alƙa. 9:36.

TA HANYOYIN ’YAN SUMOGA

Idan ka taso daga inda kogin Elbe (ko Labe) ya soma, za ka iso Manyan Duwatsun Krkonoše. A nan ne iyakar da ke tsakanin Jamhuriyar Czech da Poland take. Duwatsun suna da tsawon wajen ƙafa 5,250, kuma an ce wurin ne ya fi sanyi a tsakiyar nahiyar Turai. Dusar ƙanƙarar mai kaurin kafa 10 takan rufe kan duwatsun har tsawon watanni shida. Waɗanda ba sa yin la’akari da yanayin wurin za su iya samun kansu a cikin mugun hazo da ke mamaye ƙololuwan duwatsun ba zato ba tsammani.

A ƙarnukan da suka wuce, waɗannan jerin duwatsun sun sa an sami iyaka tsakanin larduna da dauloli da kuma ƙasashe. Da yake hanyar ba ta da kyau, yana da wuya ’yan tsaro su bi wurin, saboda haka, ta duwatsun nan ne mutanen yankin suke shigar da kayayyaki a asirce a dā. A shekara ta 1930 zuwa ta 1939, sa’ad da Manyan Duwatsun suka raba ƙasar Czechoslovakia da Jamus, sai Shaidu suka soma yin amfani da hanyoyin ’yan sumogan. Me ya sa? Domin su kai wa ’yan’uwan da ke Jamus littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Matashi Richard yana cikin waɗannan Shaidun da suke bin wannan hanyar.

“TAFIYAR SHAƘATAWA” MAI HAƊARI

Richard ya ce: “A ƙarshen mako, mu ’yan’uwa matasa bakwai ko fiye a hakan mukan hau duwatsun kuma muna saka tufa kamar masu tafiyar shaƙatawa. Mun yi tafiyar wajen awa uku kafin muka ƙetare dutsen daga ɓangaren Jamus zuwa Špindlerův Mlýn,” wato wani wurin shaƙatawa da ke da nisan mil goma daga ɓangaren Czech. A lokacin, akwai Jamusawa da yawa a yankin. A cikinsu akwai wani manomi da ya ba ’yan’uwanmu haɗin kai. Yakan ɗauki akwatuna cike da littattafan a karusar da ake ɗaukan masu zuwa hutu, kuma yana yin hakan daga wani gari da ke kusa, inda jirgin ƙasar da ya zo daga birnin Prague ya sauƙar da littattafan. Bayan ya ɗauko akwatunan zuwa gonarsa, sai ya ɓoye su a ɗakin da ake ajiye busassun ciyayi, kuma ya jira sai waɗanda za su kai littattafan ɓangaren Jamus sun zo.

Richard ya daɗa da cewa: “Bayan da muka iso gonar, mun cika jakunkunarmu wadda aka yi musamman don ɗaukan kaya mai nauyi. Kowannenmu yana ɗaukan littattafan da ke da nauyin kilo 50.” Da yake ba sa so a gane, suna tafiya da daddare, wato daga faɗuwar rana kuma su isa gida kafin gari ya waye. Wani ɗan ƙasar Jamus, mai suna Ernst Wiesner ne mai kula da da’ira a lokacin, kuma ya kwatanta matakan da suka ɗauka don kada a kama su, ya ce: “’Yan’uwa biyu sukan wuce gaba, kuma idan suka haɗu da wani, sai nan da nan su ba da alama da hasken tocila. Wannan alamar tana nuna wa ’yan’uwan da ke ɗauke da littattafan nan masu nauyi da suke bin su a baya da ratar wajen mita ɗari su ɓuya a daji. Sa’an nan su jira waɗannan ’yan’uwa biyun a wurin har sai sun dawo kuma sun nuna musu wata alama dabam. Suna canja alamar kowane mako.” Amma, suna fuskantar haɗari daga wurin ’yan sandan Jamus masu kaki mai launin shuɗi da kuma wajen wasu mutane dabam.

Richard ya ce: “Akwai wata yammar da na yi aiki sosai, saboda haka, na tafi ɓangaren Czech kafin ’yan’uwa su isa wurin. Wurin da duhu kuma akwai hazo sosai, jikina na ta rawa sa’ad da nake tafiya cikin ruwan ƙanƙara. Na ɓata hanya a cikin jejin, kuma na yi awoyi da yawa kafin na iya fitowa. Masu tafiyar shaƙatawa da yawa suna yawan ɓacewa haka, kuma su mutu a sakamako. Sa’ad da ’yan’uwa suke dawowa da sassafe ne na haɗu da su.”

A cikin shekara uku, wannan rukunin ’yan’uwa masu gaba gaɗi suna zuwa duwatsun a kowane mako. A lokacin ɗari suna amfani da sanduna da kuma amalanken tafiya a kan dusar ƙanƙara da ake kira ski. A wasu lokatai, rukunin ’yan’uwan guda ashirin sukan ƙetare iyakar da rana, suna bin hanyoyin masu tafiyar shaƙatawa. Suna yin hakan ne don su nuna cewa su ’yan tafiyar shaƙatawa ne kuma ba sa ɓarna, suna tare da wasu ’yan’uwa mata ma. Wasunsu sukan wuce gaba, idan suka ga cewa akwai wata matsala sai su jefa hulunansu sama.

Shin mene ne ke faruwa sa’ad da waɗanda suke ɗauke da littattafan suka isa gida? Ana yin shirye-shirye don a tabbata cewa an rarraba wa ’yan’uwa littattafan da wuri. Ta yaya ake yin hakan? Ana ƙulla littattafan kamar ƙullin sabulu, sai a kai su tashan jirgin ƙasa a Hirschberg. Ana kai ƙunshin zuwa ɓangarori dabam-dabam a ƙasar Jamus, sai kuma ’yan’uwa su aika littattafan a ɓoye zuwa gidajen sauran ’yan’uwan kamar yadda aka ambata da farko. Idan aka gano wannan hanyar da suke bi, za su faɗa cikin babbar matsala. Hakika wata rana, sai aka gano su a inda ba su yi tsammani ba.

A shekara ta 1936, aka gano wasu littattafai a kusa da birnin Berlin. Akwai ƙunshi uku na littattafai a cikin abubuwan da suka gano. ’Yan sandan sun yi amfani da salon rubutu wajen gane ɗaya daga cikin ’yan’uwan kuma suka kama shi. Nan ba da daɗewa ba, sai aka kama Richard Rudolph da wani kuma. Da yake ’yan’uwan suna ba da kansu don yin dukan ayyukan, wasu sun ci gaba da yin wannan tafiyar mai haɗarin daga baya.

DARASIN DA MUKA KOYA

Ainihin hanyar da ake bi don a kawo wa Shaidun da ke Jamus littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, ita ce ta ɗaukan su a jakunkuna kuma bi ta Manyan Duwatsu. Amma, ba wannan hanyar kaɗai ake bi ba. Kafin rundunar Jamus su mallaki Czechoslovakia a shekara ta 1939, ’yan’uwan suna amfani da hanyar da ke iyakar wannan ƙasar. Shaidun Jehobah da ke ƙasashen da ke da iyaka da Jamus, kamar Faransa da Nedalan da Siwizalan da kuma Shaidu a Jamus sun yi kasada da ransu don su kai wa ’yan’uwansu littattafai.

Yawancinmu a yau muna samun littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da yawa kuma a nau’o’i da dama. Ko kana karɓan sabobin littattafai a Majami’ar Mulki ko kuma kana saukar da su a dandalin jw.org, zai dace ka yi la’akari da ƙwazon da ake yi don a iya tanadar maka da su. Wataƙila ba su yi kama da na waɗannan ’yan’uwa da suke bi ta duwatsu masu cike da dusar ƙanƙara daddare ba, amma suna aiki tuƙuru don su iya yi maka hidima da rashin son kai.

a Ya yi hidima a Ikilisiyar Hirschberg da ke lardin Silesia. A dā, ana kiran Jelenia Góra da ke kudu maso yammacin Poland Hirschberg.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba