TARIHI
Jehobah Ya Albarkace Ni Sosai don Na Yi Masa Biyayya
Mahaifina ya ce: “Hakika mun koyi darasi mai kyau daga wurin Nuhu! Ya yi biyayya ga Jehobah kuma ya ƙaunaci iyalinsa. Hakan ya sa suka tsira daga Rigyawa domin dukan iyalin ta shiga cikin jirgi.”
WANNAN ɗaya ne cikin abubuwan da zan iya tunawa game da mahaifina. Shi mutumin kirki ne kuma yana da ƙwazo sosai. Yana son yin adalci sosai, saboda haka, ya so saƙon Littafi Mai Tsarki nan da nan da aka yi masa wa’azi a shekara ta 1953. Tun daga lokacin sai ya yi iya ƙoƙarinsa don ya koya mana abin da ya koya. Da farko, mahaifiyata ta yi jinkirin barin al’adun cocin Katolika. Amma daga baya, sai ta gaskata da koyarwar Littafi Mai Tsarki.
Yana da wuya iyayenmu su yi nazari da mu, domin mahaifiyarmu ba ta iya karatu da rubutu ba sosai kuma mahaifinmu yana aiki sosai a gona. A wasu lokatai yakan gaji tikis har ya riƙa barci sa’ad da muke nazari. Ƙoƙarce-ƙoƙarcensa ya taimaka mana sosai. Ni ce ’ya ta fari, kuma na taimaka wajen koyar da ƙanwata da kuma ƙannena maza biyu. Sau da yawa mahaifina yakan ce, Nuhu ya nuna cewa yana yin biyayya ga Allah ta yadda ya ƙaunaci iyalinsa. Ina son labarin Nuhu sosai! Ba da daɗewa ba, sai muka soma halartar taro a wata Majami’ar Mulki da ke birnin Roseto degli Abruzzi a gaɓar tekun Adriatic na ƙasar Italiya.
A shekara ta 1955 sa’ad da nake ’yar shekara 11, ni da mahaifiyata mun haye wani tudu zuwa yammacin garin don mu halarci taron gundumarmu na farko a ƙasar Roma. Tun daga lokacin, ina ɗaukan wannan babban taron a matsayin ɗaya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci a rayuwar Kirista.
A shekara ta gaba, na yi baftisma kuma ba da daɗewa ba na soma yin hidima ta cikakken lokaci. Sa’ad da nake ’yar shekara 17, na soma yin hidimar majagaba na musamman a birnin Latina da ke kudancin Roma, kuma yana da nisan mil 190 daga garinmu. Sabon birni ne, saboda haka, kowa yana ta-kai ta-kai. Ni da abokiyar hidimata mun yi farin ciki don rarraba littattafai masu bayyana Littafi Mai Tsarki da yawa, kuma da yake ni ƙaramar yarinya ce, na yi kewar gida sosai! Duk da haka, na so in bi ja-gorar da aka yi mini.
Daga baya aka tura ni hidima a birnin Milan don in taimaka a shirye-shiryen Taron Ƙasashe mai jigo “Everlasting Good News” (“Bishara ta Har Abada”) a shekara ta 1963. A lokacin taron, ni da ’yan’uwa da yawa mun ba da kanmu don yin aiki, har da ɗan’uwa Paolo Piccioli da ya zo daga birnin Florence. A rana ta biyu na taron gundumar, ya ba da wani jawabi mai daɗaɗawa game da zama marar aure. Sai na yi tunani cewa, ‘Wannan ɗan’uwan ba zai taɓa yin aure ba.’ Amma, sai muka soma rubuta wa juna wasiƙa kuma mun fahimci cewa muna da maƙasudi iri ɗaya. Ni da Paolo mun yi aure a shekara ta 1965.
TATTAUNAWA DA LIMAMAI
Na yi shekara goma ina hidimar majagaba na kullum a birnin Florence. Na yi farin ciki ganin yadda ikilisiyoyin suke ƙaruwa da kuma yadda matasa ma suke samun ci gaba. Ni da maigidana mun ji daɗin tattaunawa game da bauta tare da su, kuma muna wasu wasanni tare amma maigidana ya fi son buga ƙwallon ƙafa. Ko da yake, ina jin daɗin kasancewa da maigidana, amma na fahimci cewa yana bukatar ya ba da lokaci wajen taimaka wa matasa da kuma iyalai da ke ikilisiyarmu.
Ina farin ciki sa’ad da na tuna da mutane da yawa da muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su a dā. Adriana tana cikin waɗanda muka yi nazari da su, kuma ta tattauna abin da take koya da iyalai biyu. Sun keɓe lokaci don su tattauna da limamai game da koyarwar allah-uku-cikin ɗaya da kuma kurwa marar mutuwa. Manyan limamai uku ne suka halarci taron. Limaman sai kumbiya-kumbiya suke ta yi. Da zarar ɗalibanmu suka ji abin da suke faɗa, sai suka ga cewa ya yi dabam da gaskiyar da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. Hakika, wannan taron ya sa mutane da yawa suka soma bauta wa Jehobah. Da shigewar lokaci, mutane 15 daga waɗannan iyalai biyu suka zama Shaidu.
Amma, yadda muke yin wa’azi a yau ya canja. A lokacin, maigidana ya gwanince wajen tattauna da limamai, kuma ya sha yin hakan da su. Na tuna da wata tattaunawar da muka yi da su a gaban jama’a da ba Shaidu ba. Mun fahimci cewa ’yan adawar sun riga sun gaya wa wasu cikin jama’ar su riƙa yin tambayoyi da ba su da kai. Amma, mutanen ba su yi hakan ba. Wani ya yi tambaya ko ya dace coci su riƙa saka hannu a siyasa, kamar yadda suka jima suna yi. A lokacin, limaman sun fahimci cewa turi ya kai bango. Sai farat ɗaya, aka ɗauke wuta, kuma kowa ya watse. Bayan wasu shekaru, muka gane cewa ashe sun shirya a kashe wutar idan tattaunawar ba ta kasance yadda suke so ba.
HIDIMOMIN DA MUKA YI
Shekara goma bayan aurenmu, sai aka tura mu yin hidima a matsayin masu kula da da’ira. A lokacin, maigidana yana yin aiki da ake biyansa albashi mai tsoka sosai, saboda haka, yin murabus da aikin bai yi sauƙi ba sam. Amma, bayan mun saka batun a addu’a, sai muka amince mu yi hidimar. Mun ji daɗin zama da iyalai da muka sauka a gidajensu. Mukan yi nazari da yamma tare, bayan haka, sai maigidana ya taya yaran yin aikin da aka ba su a makaranta, musamman lissafi. Ƙari ga haka, yana jin daɗin karanta littattafanmu kuma yana tattauna abin da ya karanta da mutane. Muna yawan zuwa yin wa’azi a ranar Litinin a garurrukan da babu Shaidu, kuma mu gayyaci mutane zuwa jawabin da za a yi da yamma.
Bayan mun yi hidimar masu kula da da’ira na shekara biyu, sai aka gayyace mu hidima a Bethel na ƙasar Roma. Maigidana ya yi hidima a matsayin lauya, ni kuma na yi hidima a Sashen Mujallu. Barin hidima a yanki zuwa Bethel bai kasance mana da sauƙi ba, amma muna son mu yi biyayya. Ganin yadda aka faɗaɗa reshen da kuma yadda ’yan’uwa suke ƙaruwa a Italiya ya faranta mana rai sosai. A wannan lokacin, hukumar ƙasar ta amince da ayyukan Shaidun Jehobah. Mun ji daɗin yin hidima a Bethel sosai.
Sa’ad da muke hidima a Bethel, wani abu ya faru da ya sa duk ƙasar Italiya ta san da cewa Shaidun Jehobah ba sa karɓan ƙarin jini. Hakan ya faru ne tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1985. An yi wa wasu Shaidu ma’aurata zargin haddasa mutuwar ’yarsu, ko da yake ta mutu ne sanadiyyar wata cutar jini da ke yaɗuwa a ƙasashen yankin Bahar Rum. ’Yan’uwa daga Bethel sun taimaka wa alƙalan da suke wakiltar iyayen yarinyar. Wata warƙa da kuma fitowa ta musamman ta mujallar Awake! sun taimaki mutane da yawa su fahimci abin da Kalmar Allah ta ce game da jini. A waɗannan watannin, maigidana yakan yi aiki ba tsayawa har sa’o’i 16 a rana. Kuma na ƙoƙarta na taimaka masa a waɗannan ayyukan.
WANI CANJI A SALON RAYUWARMU
Shekara 20 bayan aurenmu, wani abu ya faru da mu da ya kawo wani canji na musamman a rayuwarmu. A lokacin, ina ’yar shekara 41 kuma Paolo na ɗan shekara 49. Na gaya masa cewa ina da juna biyu. Na ga abin da ya rubuta a cikin ɗan littafinsa cewa: “Addu’a: Idan gaskiya ne, ka taimake mu mu ci gaba da yin hidima ta cikakken lokaci, kada mu yi sanyi gwiwa, kuma ka sa mu zama iyayen kirki. Ka taimake ni in aikata aƙalla kashi ɗaya bisa ɗari na abubuwan da na koyar tun shekara 30 da ta shige.” Abubuwan da suka faru daga baya sun nuna cewa Jehobah ya amsa addu’armu.
Sa’ad da muka haifi ’yarmu Ilaria, abubuwa sun ɗan canja a rayuwarmu. A gaskiya, mun yi sanyi gwiwa a wasu lokatai, kamar yadda littafin Misalai 24:10 ya ambata cewa: “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne.” Amma, mun tallafa da kuma ƙarfafa juna.
Ilaria ta faɗi yadda ta yi farin ciki ganin cewa iyayenta Shaidu ne kuma suna yin hidima ta cikakken lokaci. Ba ta taɓa ji kamar ba ma kula da ita ba, ta yi girma ne a iyali mai kyau. Da rana ina kula da ita, amma da yamma sa’ad da mahaifinta ya dawo gida, yana wasa da ita kuma ya taimaka mata da aikin da aka ba ta a makaranta, ko da yake yana da wasu ayyuka da ya kamata ya yi. Yana yin hakan ko da ya san cewa ba zai yi barci ba har ƙarfe biyu ko uku na asuba domin ya kammala aikinsa. Ilaria takan ce, “Baba ne aminina.”
Taimaka wa Ilaria ta ci gaba da bauta wa Jehobah ba wasan yara ba ne, hakan yana bukatar ƙoƙari sosai. Na tuna lokacin da ta yi abin da bai dace ba, sa’ad da take wasa da ƙawarta. Mun yi amfani da Littafi Mai Tsarki don mu nuna mata abin da ya sa bai kamata ta yi hakan ba. Kuma mun sa ta ba ƙawarta haƙuri a gabanmu.
Ilaria ta ce tana yaba wa iyayenta don yadda suke son yin hidima. Yanzu da ta yi aure, ta fi fahimtar muhimmancin yin biyayya ga Jehobah da kuma bin ja-gorarsa.
YIN BIYAYYA HAR A LOKACIN BAƘIN CIKI
A shekara ta 2008, sai maigidana ya kamu da ciwon daji. Da farko, kamar zai warke, kuma ya ƙarfafa ni sosai. Ƙari ga neman shawara a kan jinyar da za a yi masa, ni da Ilaria muka riƙa yi wa Jehobah addu’a don ya taimaka mana. Duk da haka, da sannu sannu na ga wannan ƙaƙarfan mutumi yana raunanawa. Mun yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya rasu a shekara ta 2010. Amma, abubuwan da muka cim ma shekaru 45 da suka shige da muke tare sun ta’azantar da ni. Mun yi iya ƙoƙarinmu mu bauta wa Jehobah. Kuma na san cewa aikin da muka yi zai ci gaba da taimaka wa mutane. Ina ɗokin ganin an ta da maigidana daga matattu, kamar yadda Yesu ya ambata a littafin Yohanna 5:28, 29.
“Har ila, ina son labarin Nuhu kamar yadda na yi sa’ad da nake ƙarama. Kuma, ban canja makasudina ba”
Har ila, ina son labarin Nuhu kamar yadda na yi sa’ad da nake ƙaramar yarinya. Kuma, ban canja maƙasudina ba. Ina son in yi biyayya ga Jehobah, ko da mene ne yake so in yi. Na san cewa yawan albarkar da Jehobah zai yi mini ya fi duk wani tangarɗa da kuma rashi. Na shaida hakan, kuma ina tabbatar muku cewa na yi dace sosai.