TARIHI
Mun Yi Hidima Shekara Hamsin Kusa da Yankin Arctic Circle
Mun ce wa wata ƙawarmu, “Soma hidimar majagaba ba zai yi miki wuya ba, domin iyayenki Shaidu ne kuma za su goyi bayanki.” Sai ta ce: “Dukanmu Ubanmu ɗaya ne.” Amsarta ta tuna mana wani abu mai muhimmanci, wato, Ubanmu na sama yana kula da bayinsa kuma yana ƙarfafa su. Hakika, tarihinmu ya ba da tabbaci cewa hakan gaskiya ne.
IYALINMU manoma ne a yankin Ostrobothnia da ke Gabashin ƙasar Finland, kuma mu ’ya’ya goma ne. Mu ƙanana ne sa’ad da aka yi Yaƙin Duniya na Biyu. Ko da yake yaƙin bai isa wajenmu ba, amma ya jawo wahala sosai. A daren da aka jefa bama-bamai a garin Oulu da kuma Kalajoki, wutan da ke ci ya sa sarari ya yi ja. Iyayenmu sun gaya mana mu riƙa ɓuya duk sa’ad da muka ga jiragen yaƙi a sama. Sa’ad da yayanmu Tauno ya gaya mana cewa babu wanda zai sha wahala a aljanna, mun so mu ƙara koya game da aljannar.
Sa’ad da Tauno yake ɗan shekara goma sha huɗu, ya koyi gaskiya ta wajen karanta littattafan da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka wallafa. A lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, ya ƙi shiga soja domin abin da ya koya daga cikin Littafi Mai Tsarki. Sai aka kai shi fursuna, kuma aka gana masa azaba. Amma, hakan ya inganta ƙudurinsa na bauta wa Jehobah. Bayan da aka fitar da shi daga fursunan, sai ya daɗa ƙwazo a hidima. Misalinsa mai kyau ya sa mu halarci taron da Shaidu suke yi a wani ƙauye da ke kusa. Mun yi ajiyar kuɗi domin mu halarci taron gunduma, ko da yake yin hakan ba cin tuwo ba ne. Mun yi noman albasa, mun tsinka ’ya’yan itace kuma mun yi ɗinki. Dukanmu ba ma halartar taron gunduma tare, domin akwai aiki da yawa a gonarmu.
Abubuwan da muka koya game da Jehobah da kuma nufe-nufensa sun sa mu ƙaunace shi sosai, har muka keɓe kanmu kuma muka yi baftisma a shekara ta 1947. Annikki tana ’yar shekara 15 a lokacin, Aili kuma tana ’yar shekara 17. ’Yar’uwarmu Saimi ma ta yi baftisma a wannan shekarar. Mun kuma yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ’yar’uwarmu Linnea, kuma tana da aure a lokacin. Iyalinta baki ɗaya sun zama Shaidun Jehobah. Bayan da muka yi baftisma, sai muka ƙudurta cewa za mu riƙa yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a kai a kai.
MUN SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
A shekara ta 1955, mun koma birnin Kemi da ke arewa. Ko da yake muna aiki na cikakken lokaci, mun so mu soma hidimar majagaba. Amma, mun yi tunani cewa hakan zai sa mu soma aiki na ɗan lokaci kawai, kuma ba za mu samu isashen kuɗin biyan bukatunmu ba. Sai muka tattauna hakan da ’yar’uwa majagaba da aka ambata ɗazu. Bayan tattaunawar, muka fahimci cewa idan muna son mu yi hidima ta cikakken lokaci, ya kamata mu dogara ga Jehobah don biyan bukatunmu, ba ga kanmu ko kuma iyalinmu ba.
A lokacin, mun yi ajiyar kuɗin da muke bukata don yin hidimar majagaba na wata biyu. A watan Mayu na 1957, sai muka soma hidimar majagaba na wata biyu a garin Pello da ke yankin Lapland. Bayan wata biyu, ba mu kashe kuɗin da muka tara ba. Sai muka sake yin hidimar majagaba na wata biyu. Bayan wata biyu kuma, ba abin da ya sami kuɗin. Yanzu ba ma shakkar cewa Jehobah zai kula da mu. Mun yi hidimar majagaba na shekara 50, amma ba mu kashe wannan kuɗin ba! Muna ji kamar Jehobah ya riƙe hannunmu, kuma ya ce mana: “Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Isha. 41:13.
Mun yi hidimar majagaba na shekara 50, amma ba mu kashe wannan kuɗin ba!
A shekara ta 1958, mai kula da da’irarmu ya tambaye mu ko za mu iya zama majagaba na musamman, kuma mu soma hidima a garin Sodankylä da ke arewancin yankin Lapland. A lokacin ’yar’uwa ɗaya ce kawai ke zama a garin. Ta koyi gaskiya a hanya mai ban sha’awa sosai. Ɗanta da ’yan ajinsu sun tafi birnin Helsinki, wanda shi ne babban birnin ƙasar Finland. Sa’ad da suke yawo a cikin birnin, sai wata ’yar’uwa tsohuwa ta ba ɗanta mujallar Hasumiyar Tsaro, kuma ta ce ya ba mahaifiyarsa. Da ɗan ya isa gida, sai ya idar da saƙon. Mahaifiyarsa ta karanta, kuma ta ga cewa mujallar tana koyar da gaskiya.
Mun kama ɗakin haya a saman wata ma’aikatar katako. Kuma a wurin ne muke yin taro. Da farko, mu biyu da ’yar’uwan nan da kuma ’yarta ne kaɗai ke halartar taron. Mukan karanta littafin da ake tattaunawa kowane mako. Daga baya, wani mutumin da Shaidu suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ya zo aiki a wannan ma’aikatar. Sai shi da matarsa suka soma zuwa taro, har suka yi baftisma. Wannan ɗan’uwan ne ya ci gaba da gudanar da taro. Wasu maza da ke aiki a wannan ma’aikatar ma sun soma halartar taro, kuma suka yi baftisma. Bayan ’yan shekaru, rukuninmu ya zama ikilisiya.
ƘALUBALE A YANKIN
Wuraren da muke zuwa wa’azi suna da nisa sosai. Da damina, mukan taka, mu tuka keke kuma mu hau kwalekwale don mu isa inda mutane suke. Kekunanmu sun taimaka mana sosai. Mukan tuka su idan za mu je taron gunduma da kuma ziyarar iyayenmu da ke da ɗan nisa daga yankinmu. Da ɗari kuma, mukan bi bas da sassafe zuwa ƙauye, sa’an nan mu bi gida gida da kafa. Idan muka gama wa’azi a ƙauye guda, sai mu soma a wani kuma. Ƙanƙara takan taru sosai a kan hanya. A yawancin lokaci, mukan bi sawun karusar da ta wuce a kan ƙanƙarar. Amma idan an sake yin ƙanƙara, sai sawun ya ɓace. Bayan lokacin ɗari, sai ƙanƙara ta soma narkewa, kuma hakan yana sa tafiya da kafa ta yi wuya.
Mun koyi saka rigunan sanyi a lokacin ɗari. Mukan sanya safa masu kauri sosai, ko kuma mu haɗa guda biyu ko uku, da kuma manyan takalma. Duk da haka, sai ƙanƙara ta cika takalman sa’ad da muke tafiya. Sa’ad da muka isa bakin kofa, sai mu cire takalmanmu kuma mu kakkaɓe ƙanƙarar. Ƙanƙara takan jika shafin rigunan sanyi da muka sanya, kuma ta sa su daskare. Wata uwargida ta ce, ‘Lallai imaninku babu na biyunsa, tun da har kun iya fita a irin wannan yanayin.’ Mun yi takun mil 7 kafin muka isa wannan gidan.
Sau da yawa mukan kwana a gidan mutanen ƙauyen, da yake mun fito daga wuri mai nisa. Idan yamma ta yi, sai mu tambayi mutanen ko za mu iya kwana a gidansu. Suna da gidaje masu ɗan kyau, kuma suna da kirki da kuma fara’a. Ban da wurin kwanciya, sun kuma ciyar da mu. A yawancin lokatai, mukan kwanta a kan tabarma da aka yi da fatar dabba. Amma wasun su suna da masauki don baƙi. Alal misali, wata mace mai babban gida ta kai mu ɗakin baƙi da ke bene. An shirya gado da kuma shimfiɗa mai kyau a ɗakin. Sau da yawa mun tattauna Littafi Mai Tsarki har tsakar dare da masu gidan. A wani wuri, mu da ma’auratan mun kwanta a ɗaki ɗaya. Sun kwanta a gefe guda, mu kuma a ɗayan gefen. Mun tattauna da su, kuma mun amsa tambayoyinsu har asuba.
MUN SAMU ALBARKA A HIDIMARMU
Yankin Lapland yana da kyau sosai. Amma mutanen da suka koya game da Jehobah sun fi yankin kyau. Wasu mutanen da muka yi wa wa’azi maza ne da suka ƙaura zuwa yankin don su yanka itatuwa. A wasu lokatai, mukan shiga cikin ma’aikatar kuma mu ga mutane da yawa suna kwana a ciki. Waɗannan mazajen suna jin daɗin koyo game da Littafi Mai Tsarki da kuma karanta littattafanmu.
Muna da labarai masu ban dariya. Wata rana agogon da ke wata tashar mota ya makara da minti biyar, hakan ya sa bas da ya kamata mu shiga ya bar mu. Sai muka bi wani bas zuwa wani ƙauye dabam. Ba mu taɓa wa’azi a wannan ƙauyen ba. Amma da muka shiga gida na farko, sai wata mata ta ce, “Allah ya kawo ku, dā ma ina jiranku.” Ashe muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ’yar’uwarta, kuma ta ce ta gaya mana mu soma nazari da ita ma. Amma, ’yar’uwarta ba ta gaya mana ba. Mun soma nazari da ita da kuma danginta da ke kusa. Jim kaɗan sai muka soma nazari da su goma sha biyu tare. Tun daga lokacin, ’yan iyalin da yawa sun zama Shaidun Jehobah.
A shekara ta 1965, an tura mu ikilisiyar da ke Kuusamo. A lokacin masu shela ƙalilan ne kawai a ikilisiyar. Da farko, yin wa’azi a wannan yankin bai da sauƙi. Mutanen suna sha’anin addini sosai kuma ba sa son saƙonmu. Duk da haka, akwai waɗanda suke daraja Littafi Mai Tsarki. Da sannu-sannu muka san ra’ayoyinsu. Kuma bayan shekara biyu, sai soma nazari da su ya zama kamar cin tuwo.
HAR ILA MUNA HIDIMA DA ƘWAZO
Ko da yake yanzu ba ma iya yin wa’azi daga safe har yamma, amma muna fita kusan kowace rana. Yanzu wa’azi a babban yankinmu yana da sauƙi sosai domin Aili ta iya tuƙa mota. Ɗan wanmu ne ya ƙarfafa ta ta koyi tuƙi, kuma ta karɓi lasisin tuƙi a shekara ta 1987. A lokacin ta kai shekara 56 da haihuwa. Sa’ad da aka gina mana Majami’ar Mulki, sai muka soma zama a ɗakin da aka gina don mai kula da majami’ar.
Muna farin ciki sosai domin mutane da yawa sun soma bauta wa Jehobah a arewancin ƙasar Finland. Sa’ad da muka soma hidima a wurin, babu masu shela sosai. Amma yanzu akwai ikilisiyoyi da yawa da kuma da’ira guda. Mutane sun sha zuwa wurinmu a manyan taro, su gabatar da kansu kuma su tambaye mu ko mun tuna da su. Wasu sukan tuna mana cewa mun yi nazari da su sa’ad da suke yara. Allah ya sa wannan iri da muka shuka shekaru da yawa da suka shige ya tsira.—1 Kor. 3:6.
Mun cika shekara 50 da hidima a matsayin majagaba na musamman a shekara ta 2008. Mun gode wa Jehobah cewa mun samu ƙarfafa daga juna don mu ci gaba da bauta masa. Mun kasance da salon rayuwa mai sauƙi, amma ba mu rasa kome ba. (Zab. 23:1) Yanzu mun ga cewa bai dace da muka yi jinkiri ba da farko. Abin farin ciki shi ne, a cikin duk waɗannan shekarun, Jehobah ya cika alkawarin da ya yi a cikin Ishaya 41:10, cewa: Zan “ƙarfafa ka: ni taimake ka, i, ni riƙe ka da hannun dama na adalcina.”