Ka Taimaki Kanka Da Wasu Ta Wajen Yin Amfani Da Kalmar Allah
“Dukan dokokinka a kan kowane zance, ni kan maishe su daidai ne.”—ZAB. 119:128.
1. Me ya sa za mu amince da Kalmar Allah sosai?
SA’AD DA dattawa suke nema su tsai da shawara ko ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya ƙware ya soma wa’azi, suna tambayar kansu, ‘Shin furucin ɗalibin ya nuna ya gaskata cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki?’a Ya kamata dukanmu mu nuna ta ayyukanmu da kuma furucinmu cewa mun amince da Littafi Mai Tsarki. Idan muka amince da Littafi Mai Tsarki da kuma yi amfani da shi sosai a hidimarmu, za mu taimaka wa mutane su san Jehobah kuma su samu rai madawwami.
2. Me ya sa za mu ‘lizima kai a cikin al’amuran da muka koya’?
2 Manzo Bulus ya nanata muhimmancin Kalmar Allah sa’ad da ya rubuta wa Timotawus cewa: “Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo.” “Al’amuran” da Bulus ya ambata su ne koyarwar Littafi Mai Tsarki da suka motsa Timotawus ya gaskata da bisharar. Waɗannan koyarwar suna taimaka mana a yau, kuma za su ci gaba da ‘hikimantar da mu zuwa ceto.’ (2 Tim. 3:14, 15) Abin da Bulus ya faɗa a gaba ya nuna cewa Allah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki. Amma, mene ne kuma za mu iya koya daga 2 Timotawus 3:16? (Karanta.) Bari mu bincika wannan ayar dalla-dalla, don yin hakan zai sa mu amince cewa dukan koyarwar Jehobah “daidai ne.”—Zab. 119:128.
‘MAI AMFANI GA KOYARWA’
3-5. (a) Me ya faru bayan da Bitrus ya ba da jawabi ga taro mai girma a ranar Fentakos, kuma me ya sa? (b) Me ya sa mutane da yawa a Tasalonika suka soma bauta wa Jehobah? (c) Mene ne zai iya burge mutane a yau game da hidimarmu?
3 Yesu ya gaya wa al’ummar Isra’ila: “Ina aika maku annabawa, da masu-hikima, da marubuta.” (Mat. 23:34) Yesu yana magana game da almajiransa da ya koya wa yadda za su yi amfani da Nassosi a hidimarsu. Manzo Bitrus yana cikin waɗannan “marubuta,” kuma a ranar Fentakos ta shekara ta 33, ya ba da jawabi ga taro mai girma a Urushalima kuma ya yi ƙaulin ayoyi da yawa daga Nassosin Ibrananci. Sa’ad da mutanen suka ji yadda ya bayyana waɗannan ayoyin, sai da yawa a cikinsu “suka soku cikin zuciyarsu.” Sun tuba daga zunubansu. A ranar, mutane kusan dubu uku suka roƙi Allah ya gafarta musu kuma suka zama Kiristoci.—A. M. 2:37-41.
4 Za mu iya koyon wani abu daga manzo Bulus da ya yi wa’azi a wasu wurare, ba a Urushalima kaɗai ba. Alal misali, ya yi wa Yahudawa da ke bauta a majalisa wa’azi a birnin Makidoniya da ke Tasalonika. A kowace assabbaci, har mako uku Bulus yana “mahawara da su daga cikin littattafai, yana buɗewa, yana ƙarfafawa, wajib ne ga Kristi ya sha wahala, ya tashi kuma daga matattu.” Mene ne sakamakon? “Waɗansu [Yahudawa] a cikinsu suka rinjayu,” kamar yadda taro mai yawa na “Helenawa masu-ibada kuma” suka yi.—A. M. 17:1-4.
5 Yadda bayin Allah a yau suke amfani da Littafi Mai Tsarki yana burge mutane da yawa. Sa’ad da wani a ƙasar Siwizalan ya saurari yadda wata ’yar’uwa ta karanta wani nassi, sai ya tambaye ta: “Wane coci kike zuwa?” Ta ce: “Ni da ’yar’uwata Shaidun Jehobah ne.” Sai ya ce: “Ai na sani! Shaidun Jehobah ne kaɗai suke zuwa gidajen mutane kuma su karanta musu Littafi Mai Tsarki.”
6, 7. (a) Ta yaya waɗanda suke koyarwa a cikin ikilisiya za su yi amfani da Littafi Mai Tsarki yadda ya dace? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki yadda ya dace sa’ad da muke nazari da wani?
6 Ta yaya za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki yadda ya dace a koyarwarmu? Idan aka ba ka jawabi a ikilisiya, ka yi amfani da ainihin nassosi da suka goyi bayan koyarwarka. Maimakon ka gaya wa mutane abin da nassin ya ce ko kuma ka karanta daga cikin takarda, ka buɗe Littafi Mai Tsarki kuma ka karanta, ka ƙarfafa masu sauraro su yi hakan. Ka bayyana ma’anar ayoyin da kuma yadda za su taimaka musu su ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Maimakon yin amfani da misalai da suke da wuyan fahimta ko kuma labarai da za su sa mutane dariya, ka yi amfani da lokacin wajen bayyana Kalmar Allah.
7 Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke koyar da ɗalibanmu? Yayin da muke nazari da mutum, ya kamata mu karanta nassosi da aka rubuta amma ba a yi ƙaulinsu ba. Ya kamata mu ƙarfafa ɗalibin ya karanta su kuma mu taimaka masa ya fahimci ma’anarsu. Ta yaya za ka yi hakan? Bai kamata mu yi dogon bayani ba kamar muna lacca, amma ya kamata mu bar ɗalibin ya faɗi ra’ayinsa. Maimakon ka gaya masa abin da zai yi imani da shi ko kuma matakin da zai ɗauka, kana iya yi masa tambayoyi da za su sa ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.b
‘MAI AMFANI GA TSAUTAWA’
8. Wace kokawa ce Bulus ya yi?
8 Dattawa ne suke da hakkin ‘tsauta’ ko kuma yi wa waɗanda suka yi zunubi horo. (1 Tim. 5:20; Tit. 1:13) Amma, yana da muhimmanci mu tsauta wa kanmu. Bulus Kirista ne mai kan gado kuma yana da lamiri mai kyau. (2 Tim. 1:3) Duk da haka ya ce: “Ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubi.” Za mu tattauna abin da Bulus ya yi don ya shawo kan kasawarsa.—Karanta Romawa 7:21-25.
9, 10. (a) Waɗanne kasawa ne Bulus ya yi fama da su? (b) Ta yaya Bulus wataƙila ya shawo kan kasawarsa?
9 Waɗanne kasawa ne Bulus ya yi ƙoƙari ya shawo kansu? Ko da yake bai lissafa su ba, amma ya rubuta wa Timotawus cewa a dā shi “mai-ɓatanci” ne. (1 Tim. 1:13) Kafin ya zama Kirista, Bulus ya wulakanta Kiristoci. Ya ce “Na fai hauka saboda su.” (A. M. 26:11) Bulus ya koyi ya kame kansa, amma yin hakan bai kasance masa da sauƙi ba don a wasu lokatai, yakan ƙoƙarta sosai ya kame kansa da furucinsa. (A. M. 15:36-39) Mene ne ya taimake shi ya yi nasara?
10 Bulus ya bayyana abin da ya yi don ya tsauta wa kansa a cikin wasiƙa da ya rubuta wa Kiristoci da ke Koranti. (Karanta 1 Korintiyawa 9:26, 27.) Ya ƙoƙarta sosai don ya shawo kan kasawarsa. Babu shakka, ya nemi shawara a cikin Nassosi, ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya bi shawarar, kuma ya yi iya ƙoƙarinsa ya yi hakan.c Ya kafa mana misali mai kyau domin mu ma muna fama mu shawo kan kasawarmu.
11. Ta yaya za mu ci gaba da “gwada” kanmu ko muna bin hanya ta gaskiya?
11 Bai kamata mu yi tunani cewa za mu iya daina fama da kasawarmu ba. Muna bukatar mu ci gaba da “gwada” kanmu don mu tabbata cewa muna bin hanyar gaskiya. (2 Kor. 13:5) Sa’ad da muke karanta nassosi kamar Kolosiyawa 3:5-10, muna iya tambayar kanmu: ‘Ina yin ƙoƙari sosai don in shawo kan kasawata? Ko kuma na soma son abin da Jehobah ya tsana? Alal misali, idan dandalin da ake lalata ya bayyana farat ɗaya, ina rufe dandalin nan da nan ko kuma ina nemansu ne?’ Idan muka bi shawarar da ke cikin Kalmar Allah a wannan hanyar, hakan zai taimaka mana mu “yi zamanmu ba barci ba maye.”—1 Tas. 5:6-8.
‘MAI AMFANI GA KWAƁEWA’
12, 13. (a) Mece ce kalmar nan ‘kwaɓewa’ take nufi, kuma ta yaya za mu bi misalin Yesu a yin hakan? (b) Wane irin furuci ne za mu guji yi?
12 Kalmar nan ‘kwaɓewa’ da aka fassara daga Helenanci gana nufin “daidaita wani abu ko kuma a yi masa gyara.” A wasu lokatai, muna bukatar mu sasanta da wanda abin da muka faɗa ko kuma yi ya ɓata masa rai. Alal misali, shugabanan Yahudawa sun ce Yesu yana ci da sha da “masu-karɓan haraji da masu-zunubi.” Yesu ya ce: “Lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo. Amma ku tafi ku koya azancin wannan, ni, jinƙai ni ke so, ba hadaya ba.” (Mat. 9:11-13) Yesu ya kuma daidaita ra’ayin mutane game da Allah. Ya koya wa mutane cikin haƙuri da kuma kirki cewa Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fit. 34:6) A sakamako, mutane da yawa masu tawali’u suka ba da gaskiya ga bisharar.
13 Ya kamata mu yi koyi da Yesu sa’ad da muke ƙoƙari mu taimaka wa mutane. Gargaɗin da ke 2 Timotawus 3:16, ba ya nufin mu yi wa mutane baƙar magana sa’ad da muke sasantawa da su. Nassi bai ba mu damar yi wa mutane magana ba tare da yin la’akari da yadda za su ji ba. Idan muka yi magana da garaje, kalaminmu yana iya zama kamar “sussukan takobi.” Za mu sa mutum baƙin ciki kuma ba za mu taimaka masa ba.—Mis. 12:18.
14-16. (a) Ta yaya dattawa za su iya ‘kwaɓe’ waɗanda suke bukatar taimako don su magance matsalolinsu? (b) Me ya sa yake da kyau iyaye su yi amfani da Nassi wajen ‘kwaɓe’ ’ya’yansu?
14 Ta yaya za mu yi haƙuri da kuma kirki sa’ad da muke amfani da Littafi Mai Tsarki don mu sasanta da wani? A ce ma’aurata da suke yawan jayayya sun gaya wa dattijo ya taimaka musu su daina yin hakan. Mene ne dattijon zai yi? Ba zai goyi bayan kowa ba, kuma ba zai faɗi ra’ayinsa ba game da matsalolinsu. Maimakon haka, zai yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don ya taimaka musu su fahimci yadda za su daina jayayyar. Yana iya yin amfani da ƙa’idodi da ke cikin babi 3 na littafin nan Asirin Farinciki na Iyali. Yayin da suke tattaunawa, ma’auratan za su fahimci cewa suna bukatar yin wasu canje-canje. Daga baya, dattijon zai iya tambayar ma’auratan ko matsalarsu ta ragu, kuma zai ba su ƙarin taimako idan da bukata.
15 Ta yaya iyaye za su kwaɓi yaransu a hanyar da za ta taimaka musu su ci gaba da bauta wa Jehobah? A ce ’yarka ta samu sabuwar ƙawa, amma kana ganin cewa ba ƙawar kirki ba ce. Da farko, ka nemi ƙarin bayani game da ƙawar. Bayan haka, idan har ila ka damu da ’yarka, kana iya tattaunawa da ita ta wajen yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da ke cikin littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 2. Ka tabbata ka daɗa tattauna kuma da ita a wani lokaci. Kana iya lura da yadda take yi idan ta fita wa’azi da kuma sa’ad da kuke shakatawa tare a matsayin iyali. Idan ka bi da ita cikin haƙuri da kuma kirki, za ta san cewa kana ƙaunarta kuma ka damu da ita. Hakan zai sa ta bi shawararka game da abokantaka, kuma ta guji yin zaɓi marar kyau a rayuwarta.
16 Hakanan ma, za mu iya taimaka wa waɗanda suke damuwa saboda rashin lafiya ko rashin aiki ko kuma waɗanda ba su fahimci wata koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Muna bukatar mu yi hakan cikin haƙuri da kuma kirki. Muna amfana sosai idan muka yi amfani da Kalmar Allah don “kwaɓewa.”
‘MAI AMFANI GA HORO DA KE CIKIN ADALCI’
17. Me ya sa ya kamata mu yi godiya sa’ad da aka mana horo?
17 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, . . . amma daga baya ya kan bada amfani mai salama watau na adalci ke nan ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.” (Ibran. 12:11) Yawancin Kiristoci da suka manyanta yanzu, sun yarda cewa horon da iyayensu suka yi musu ne ya taimaka musu. Kuma idan muka karɓi horo da Jehobah yake ba mu ta wajen dattawa, ba za mu ratse daga hanyar rai ba.—Mis. 10:17.
18, 19. (a) Me ya sa gargaɗin da ke Misalai 18:13 ke da muhimmanci ga dattawa don su ba da horo “cikin adalci”? (b) Mene ne zai faru idan dattawa suka ba da horo cikin tawali’u da kuma ƙauna?
18 Ta yaya dattawa da kuma iyaye za su koyi ba da horo da kyau? Jehobah ya gaya wa Kiristoci cewa su ba da horo “cikin adalci.” (2 Tim. 3:16) Hakan yana nufin cewa mu yi amfani da ƙa’idodin Littafin Mai Tsarki don ba da horo. Wata ƙa’ida mai muhimmanci ita ce wadda ke cikin Misalai 18:13 da ta ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gareshi da kunya.” Saboda haka, ya kamata dattawa su samu cikakken bayani game da wanda ake zarginsa da yin wani laifi mai tsanani kafin su ba da horo. (K. Sha 13:14) Hakan zai sa su ba da horon “cikin adalci.”
19 Ƙari ga haka, Kalmar Allah ta gargaɗi dattawa su riƙa ba da horo “cikin tawali’u.” (Karanta 2 Timotawus 2:24-26.) Babu shakka cewa idan mutum ya yi zunubi, zai iya sa a zargi Jehobah ko kuma ya jawo wa mutane lahani. Duk da haka, dattijo ba zai taimaki mutumin ba idan yana tsauta masa cikin fushi. Amma, mai zunubin zai so ya tuba idan dattawa suka yi koyi da “alherin Allah” sa’ad da suke taimaka masa.—Rom. 2:4.
20. Waɗanne ƙa’idoji ne iyaye suke bukatar su bi sa’ad da suke yi wa ’ya’yansu horo?
20 Wajibi ne iyaye ma su yi amfani da ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki don su raini ’ya’yansu “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Alal misali, mene ne ya kamata uba ya yi idan wani ya kawo karan ɗansa a wurinsa? Uban ya tabbatar da abin da aka gaya masa kafin ya hori ɗan. Kuma bai kamata halin cin zali ya kasance cikin iyalin Kirista ba. Jehobah Allah ne mai ‘cike da tausayi, mai-jinƙai kuma.’ Iyaye suna bukatar su bi misalinsa sa’ad da suke yi wa ’ya’yansu horo.—Yaƙ. 5:11.
BAIWA CE MAI TAMANI DAGA JEHOBAH
21, 22. Waɗanne kalamai ne da suke cikin Zabura 119:97-104, suka kwatanta yadda kake ɗaukan Kalmar Jehobah?
21 Wani bawan Jehobah ya faɗi abin da ya sa yake son dokar Jehobah. (Karanta Zabura 119:97-104.) Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ya sami hikima da fahimi da kuma ganewa. Sa’ad da ya bi gargaɗin da ke cikinsa, ya guji yin kuskuren da mutane da yawa suka yi. Ya ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki sosai, kuma ya amfana daga bin ƙa’idodinsa. Ya ƙudurta cewa ba zai daina bin dokar Jehobah ba.
22 Kana daraja “kowane nassi” kuwa? Zai iya taimaka maka ka kasance da bangaskiya sosai cewa Allah zai cika nufinsa.Gargaɗin da ke cikinsa yana taimaka maka ka guji yin zunubi da kuma sakamakonsa, wato mutuwa. Idan ka yi amfani da Nassi da kyau, za ka taimaki mutane su samu hanyar rai kuma su ci gaba da tafiya a cikinta. Bari mu ci gaba da yi amfani da “kowane nassi” a waɗannan hanyoyin yayin da muke bauta wa Jehobah, Allah mai ƙauna da kuma hikima.
a Ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafi na 79.
b Sau da yawa, Yesu yakan tambayi wasu sa’ad da yake koyarwa: “Me kuke tsammani?” Sai ya jira su amsa.—Mat. 18:12; 21:28; 22:42.
c Wasiƙun da Bulus ya rubuta sun ƙarfafa mu mu shawo kan kasawarmu. (Rom. 6:12; Gal. 5:16-18) Ya dace mu kammala cewa shi ma ya yi amfani da gargaɗin da ya ba wasu.—Rom. 2:21.