Kana Daraja Gādonka Kuwa?
“Allah ya . . . ziyarci Al’ummai, domin shi ciro wata jama’a daga cikinsu domin sunansa.”—A. M. 15:14.
1, 2. (a) Mene ne “Mazaunin Dauda,” kuma ta yaya za a sake gina shi? (b) Su waye ne bayin Jehobah a yau?
A WANI taron da hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a Urushalima ta yi a shekara ta 49 a zamanin Yesu, Yaƙub ya ce: “Siman [Bitrus] ya ba da labari yadda Allah ya fara ziyarci Al’ummai, domin shi ciro wata jama’a daga cikinsu domin sunansa. Zantattukan annabawa fa suna muwafaka da wannan; kamar yadda na rubuta, bayan wannan zan komo, in sake gina mazaunin Dawuda, wanda ya rushe; in sake gina kufansa kuma, in tashe shi: Domin sauran mutanen duniya su nemi Ubangiji, da dukan Al’ummai, waɗanda an kira sunana a bisansu, in ji Ubangiji, wanda yana maida waɗannan abu sanannu tun daga farkon duniya.”—A. M. 15:13-18.
2 “Mazaunin Dauda” da aka ambata, yana nufin sarakunan da suka taso daga zuciyar Dauda. Mazaunin ya “rushe” sa’ad da aka cire Zedekiya wanda shi ne sarki na ƙarshe na Yahuda. (Amos 9:11) Amma, annabcin ya nuna cewa za a sake gina “mazaunin” kuma. Hakan yana nufin cewa wani sarki zai taso bayan Dauda, wato, Yesu. (Ezek. 21:27; A. M. 2:29-36) Yaƙub ya ce wannan annabcin ya nuna cewa za a shafe Yahudawa da ’Yan Al’ummai don su zama sarakuna tare da Yesu a sama. A yau, shafaffun da suka rage da miliyoyin “waɗansu tumaki,” suna yin wa’azi game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da haɗin kai.—Yoh. 10:16.
BAYIN JEHOBAH SUN FUSKANCI WANI ƘALUBALE
3, 4. Mene ne ya taimaki Yahudawa su kasance da aminci ga Jehobah a ƙasar Babila?
3 Sa’ad da aka kai Yahudawa bauta a ƙasar Babila, a bayyane yake cewa “mazaunin Dauda” ya rushe. Tun da Babiloniyawa suna bautar gumaka, ta yaya bayin Jehobah suka kasance da aminci a shekara 70 da suka yi a ƙasar? Sun kasance da aminci yadda mu ma muke kasancewa da aminci a duniyar Shaiɗan. (1 Yoh. 5:19) Bayin Jehobah suna da gādo mai tamani da ke taimaka musu su kasance da aminci.
4 A yau muna da cikakken Littafi Mai Tsarki, kuma wannan ɗaya cikin gādonmu ne. Yahudawa da aka kai bauta a ƙasar Babila ba su da cikakken Littafi Mai Tsarki. Amma duk da haka, sun san Dokar da aka ba da ta hannun Musa da kuma dokoki goma da ke cikinta. Sun san “waƙoƙin Sihiyona,” da hurarrun karin magana da kuma yadda wasu kakanninsu suka kasance da aminci ga Jehobah. Waɗannan Yahudawan sun yi kuka sosai domin suna son su koma ƙasarsu, kuma ba su manta da Jehobah ba. (Karanta Zabura 137:1-6.) Dukan waɗannan abubuwan sun taimaka musu su kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da suke ƙasar Babila, duk da yake wajen yana cike da bautar arna.
ALLAH-UKU-CIKIN-ƊAYA BA SABUWAR KOYARWA BA CE
5. Babiloniyawa da Masarawa sun yi imani da waɗanne ire-iren allah-uku-cikin-ɗaya?
5 A zamanin dā, mutane suna bauta wa allah-uku-cikin-ɗaya. Alal misali, Babiloniyawa suna bauta wa Sin, allahn-wata da Shamash, allahn-rana da kuma Ishtar, allahiyar ni’ima da yaƙi. Masarawa suna bauta wa wani allah da suka ce yana da mata da kuma ɗa. Ko da yake wannan allah-uku-cikin-ɗaya ne, amma sun ce ƙarfinsu ba ɗaya ba ne. Wani allah-uku-cikin-ɗaya na Masarawa shi ne Osiris da allahiya Isis da ɗansu Horus.
6. Mene ne Kiristendam suke koyar game da Allah, kuma yaya muka samu kāriya daga wannan koyarwar?
6 Kiristendom ma a yau sun gaskata da allah-uku-cikin-ɗaya. Sun ce Uba da Ɗa da kuma ruhu mai tsarki ɗaya ne. Amma, wannan koyarwar rashin kunya ce, tun da sun ce Allah yana kamar sashe ɗaya na abu guda da aka raba kashi uku. An kāre bayin Jehobah daga wannan koyarwar ƙarya. Mun koya cewa Jehobah “Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.” (K. Sha 6:4) Yesu ya maimaita waɗannan kalmomin, kuma Kiristoci na gaskiya suna gaskata da hakan.—Mar. 12:29.
7. Me ya kamata mutum ya gaskata game da Allah kafin ya yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah?
7 Koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ya saɓa wa umurnin da Yesu ya ba almajiransa cewa su ‘tafi fa, su almajirtar da dukan al’ummai, suna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.’ (Mat. 28:19) Hakan yana nufin cewa idan mutum yana son ya yi baftisma a matsayin Kirista na gaske da kuma Mashaidin Jehobah, dole ne ya amince cewa Uban, wato Jehobah ya fi Yesu iko. Kuma Yesu Ɗan Allah ne wanda ya zo duniya don ya fanshe mu. Ruhu mai tsarki kuma ikon da Allah yake ayyuka da shi ne, ba sashen Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba. (Far. 1:2) Idan mutum ya ci gaba da gaskata da wannan koyarwar, ba zai iya yin baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah ba. Muna matuƙar farin cikin sanin gaskiya cewa koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya yana ɓata wa Allah rai kuma wannan gaskiyar gādonmu ce.
SIHIRI
8. Mene ne Babiloniyawa suka gaskata game da alloli da kuma aljanu?
8 Babiloniyawa sun gaskata da allolinsu da aljanu da kuma sihiri. Wani littafin tarihi ya ce: “Babiloniyawa sun gaskata cewa aljanu suna iya sa mutum ciwo. Saboda haka, suna yin addu’a ga allolinsu cewa su kāre su daga aljanu.”
9. (a) Ta yaya Yahudawa da yawa suka koyi ƙarya game da aljanu? (b) Ta yaya muke samun kāriya daga yin cuɗanya da aljanu?
9 Sa’ad da Yahudawa suke bauta a ƙasar Babila, yawancinsu sun koyi koyarwar arna. Daga baya, Yahudawa da yawa suka yi imani da koyarwar Helenawa cewa aljanu suna iya yi wa mutum alheri. Amma, Allah ya gargaɗe mu cewa kada mu yi sihiri ko kuma yi cuɗanya da aljanu domin hakan yana da lahani sosai. Wannan koyarwar tana cikin gādonmu. (Isha. 47:1, 12-15) Mun yi tir da sihiri kamar yadda Jehobah ya ce mu yi, kuma hakan kāriya ce a gare mu.—Karanta Kubawar Shari’a 18:10-12; Ru’ya ta Yohanna 21:8.
10. Daga ina ne Babila Babba ta koyi al’adu da koyarwar ƙarya?
10 Ba Babiloniyawa kaɗai ba ne suka yi sihiri ba, amma duk da addinan da suke goyon bayansu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki yake kiran dukan addinan ƙarya a duniya Babila Babba. (R. Yoh. 18:21-24) Waɗannan addinan suna da alaƙa da Babila ta dā domin ita ce tushen koyarwar ƙarya a yau. Nan ba da daɗewa ba, za a halaka Babila Babba domin tana sihiri da bautar gumaka da dai wasu zunubai.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:1-5.
11. Waɗanne gargaɗi game da sihiri ne aka wallafa a cikin littattafanmu?
11 Jehobah ya ce: “Ba za ku yi maita ba.” (Lev. 19:26) Mutane da yawa sun saka hannu a sihiri tun shekara ta 1800. Saboda haka, Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta ce: “Koyarwa da gama gari ne cewa matattu suna ci gaba da rayuwa a wani wuri ba sabon abu ba ne. Ba yau aka soma wannan koyarwar ba, kuma ita ce tushen dukan koyarwar ƙarya.” Mujallar ta kuma ce aljanu suna yi kamar su matattu ne da ke yin magana da rayayyu. A sakamakon haka, aljanu sun samu damar yaudarar mutane da yawa. Mujallar nan What Say the Scriptures About Spiritism? da aka buga tun da daɗewa da kuma wasu littattafanmu na kwana-kwanan nan sun ba da irin wannan gargaɗin.
SHIN KURWAR MUTANE SUNA SHAN AZABA A JAHANNAMA?
12. Mene ne aka hure Sulemanu ya ce game da matattu?
12 “Dukan waɗanda sun san gaskiya” za su iya amsa wannan tambayar. (2 Yoh. 1) Sulemanu ya ce: “Kare mai-rai ya fi matacen zaki. Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba, . . . Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da ƙarfinka; gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” Kuma mun amince da waɗannan kalmomin.—M. Wa. 9:4, 5, 10.
13. Ta yaya al’ada da addinin Helenawa suka shafi na Yahudawa?
13 Jehobah ya gaya wa Yahudawa gaskiya game da matattu. Amma, sa’ad da sarakunan Hellas suka mamaye Yahuda da Siriya, sun tilasta musu su rungumi koyarwa da al’adarsu. A sakamako, Yahudawa suka soma gaskata cewa kurwa ba ta mutuwa kuma akwai wutar jahannama. Ba Helenawa ba ne suka soma gaskata cewa za a ƙona mutum cikin wutar jahannama ba. Littafin nan The Religion of Babylonia and Assyria ya ce, Babiloniyawa sun gaskata cewa akwai wani wuri inda alloli da aljanu masu ƙarfi sosai za su azabta mutane. A bayyane yake cewa sun gaskata cewa akwai sashen jikin mutum da ke rayuwa bayan mutuwa.
14. Mene ne Ayuba da Ibrahim suka sani game da mutuwa da kuma tashin matattu?
14 Ko da yake Ayuba bai da Littafi Mai Tsarki, amma ya san abin da ke faruwa da mutum sa’ad da ya mutu. Ya kuma san cewa Allah mai ƙauna yana ɗokin ya ta da shi daga matattu. (Ayu. 14:13-15) Ibrahim ma ya gaskata da tashiwar matattu. (Karanta Ibraniyawa 11:17-19.) Ba su gaskata cewa matattu suna rayuwa a wani wuri ba. Ba zai yiwu a ta da mutumin da ba zai iya mutuwa ba. Ruhu mai tsarki na Allah ya taimaki Ayuba da Ibrahim su gaskata da tashiwar matattu.Wannan gaskiyar ma gādonmu ne.
ME YA SA ‘FANSAR’ TAKE DA MUHIMMANCI?
15, 16. Ta yaya aka kuɓuce mu daga zunubi da mutuwa?
15 Muna matuƙar godiya domin Allah ya bayyana mana dalla-dalla yadda ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa da muka gāda daga Adamu. (Rom. 5:12) Mun san cewa Yesu ya zo duniya “ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu, shi ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” (Mar. 10:45) Yana da kyau sosai da muka san game da “barata a yalwace ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi.”—Rom. 3:22-24.
16 A ƙarni na farko, an bukaci mutane su tuba daga zunubansu kuma su yi imani da hadayar fansa ta Yesu idan suna son a gafarce su. Hakan ma yake da mu a yau. (Yoh. 3:16, 36) Idan mutum ya gaskata da koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya da kurwa marar mutuwa, kuma ya ci gaba da gaskata da su, ba zai iya amfana daga fansar Yesu ba. Amma, mu za mu iya amfana domin mun san gaskiya game da “Ɗa na ƙaunar [Allah]; wanda mu ke da fansarmu a cikinsa, watau gafarar zunubanmu.”—Kol. 1:13, 14.
KU DAGE A MATSAYIN MASU ƊAUKE DA SUNAN ALLAH
17, 18. Mene ne zai taimaka mana mu san tarihin Shaidun Jehobah, kuma yaya hakan zai amfane mu?
17 Gādonmu ya haɗa da abubuwan da Allah ya koya mana da wasu hanyoyin da ya taimaka mana da kuma albarkace mu. Littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses, ya bayyana yadda bayin Jehobah a faɗin duniya suke duƙufa da bauta masa. Za mu iya koya tarihin Shaidun Jehobah a bidiyon nan Jehobah’s Witnesses—Faith in Action, Sashe na 1 da na 2. Za mu kuma iya koya game da su a littattafai kamar su Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom. Sau da yawa kuma muna karanta labaran ’yan’uwanmu a ciki mujallu.
18 Isra’ilawa sun amfana sosai sa’ad da suka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimake su. Mu ma muna amfana sa’ad da muka yi nazarin tarihin Shaidun Jehobah. (Fit. 12:26, 27) Sa’ad da Musa ya tsufa, ya gaya wa Isra’ilawa: ‘Ku tuna da kwanakin dā, ku lura da shekarun tsara zuwa tsara; ku tambayi ubanku, su kuwa gwada muku; manyanku kuma, za su faɗa muku.’ (K. Sha 32:7) Dukanmu muna farin ciki don bauta wa Jehobah da kuma sanar wa mutane abubuwan da ya yi. (Zab. 79:13) Darussan da muka koya daga tarihinmu a matsayin bayin Jehobah za su taimaka mana mu ci gaba da bauta masa.
19. Me ya kamata mu yi tun da mun san gaskiya?
19 Muna godiya sosai domin ba ma cikin duhu, amma mun san gaskiya game da Allah. (Mis. 4:18, 19) Saboda haka, zai dace mu ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bishara ga mutane. Muna da ra’ayin wani marubucin zabura wanda ya ce: “Zan ambaci adalcinka, naka kaɗai. Ya Allah, tun ina yaro kā koya mani; har wa yau fa ina bayyana ayyukanka masu-ban al’ajibi. I, har lokacin da na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah; sai dai na bayyana ikonka ga tsara mai-zuwa, ƙarfinka kuma ga dukan wanda ya ke zuwa.”—Zab. 71:16-18.
20. Me za mu nuna idan mun kasance da aminci ga Jehobah, kuma mene ne ra’ayinmu game da hakan?
20 Idan mun kasance da aminci, za mu nuna mun yarda cewa Jehobah yana da iko ya mallake mu kuma ya kamata mu bauta masa. (R. Yoh. 4:11) Jehobah yana ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimake mu mu yi shelar bishara ga mutane da kuma ta’aziya da bege ga masu makoki. (Isha. 61:1, 2) Ko da yake Shaiɗan yana ƙoƙari ya mallaki kowa, amma muna godiya don gādonmu a bautar Jehobah, kuma mun duƙufa mu kasance da aminci ga Jehobah kuma mu yabe shi har abada.—Karanta Zabura 26:11; 86:12.