Wani Matsarin Sarkin Ƙasar Roma Ya Saurari Bishara
Wani hafsa ɗan ƙasar Roma mai suna Yuliyas da sojojinsa da suka gaji tikis sun kai wasu fursunoni zuwa ƙasar Roma a shekara ta 59 a zamaninmu. Sun shiga birnin ta ƙofar Porta Capena. A kan Tudun Falasɗinu, sun ga fadar Sarki Nero da sojoji suke gadinta da takubba a ɓoye a ƙarƙashin tufafinsu.a Yuliyas ya bi da fursunonin ta filin Roma kuma suka hau Tudun Viminal. Sai suka bi ta wani lambu da aka gina bagadai da yawa na allolin Roma, kuma suka wuce babban filin da ake farati da kuma horar da sojoji.
Manzo Bulus yana cikin fursunonin. Watanni da suka shige, sa’ad da aka yi wani haɗari a teku, wani mala’ika ya gaya masa cewa: “Dole za ka tsaya gaban Kaisar.” (A. M. 27:24) Wataƙila Bulus ya yi shakka ko hakan zai faru da gaske. Sa’ad da ya juya ya kalli birnin, mai yiwuwa ya tuna da abin da Yesu ya gaya masa shekaru da suka shige a Hasumiyar Antonia da ke birnin Urushalima cewa: “Ka yi farin ciki: gama kamar yadda ka bada shaida a kaina cikin Urushalima, haka kuma dole za ka yi shaida a cikin Roma.”—A. M. 23:10, 11.
Wataƙila Bulus ya kalli sansanin sojoji da ake kira Castra Praetoria. Wannan babban sansani ne mai manyan garu da hasumiyoyi. Rukuni 12 na sojoji masu gadin sarki da sojoji masu yawa da ke tsare birnin da kuma mahaya duk suna zama a sansanin.b Wannan sansanin yana tuna wa mutanen cewa sarkin yana da iko sosai. Yuliyas ya kai waɗannan fursunonin zuwa Roma, tun da yake matsaran suna tsare fursunoni daga wasu ɓangarorin ƙasar Roma. A ƙarshe fursunonin sun isa Roma bayan sun yi watanni da yawa a hanya.—A. M. 27:1-3, 43, 44.
BULUS BAI DAINA WA’AZI BA
Abubuwa masu ban mamaki sun faru a hanya sa’ad da Bulus yake zuwa ƙasar Roma da jirgin ruwa. Sa’ad da ake guguwa a teku, an saukar wa Bulus da wahayi cewa dukan waɗanda suke cikin jirgin za su tsira. Wani maciji mai dafi ya sare shi, amma ba abin da ya same shi. Bayan hakan, ya warkar da marasa lafiya da ke tsibirin Malita, kuma mutanen suka soma cewa shi allah ne. Wataƙila wasu sojoji matsara sun ji wannan labarin kuma sun yi ta taɗinsa.
Bulus ya riga ya haɗu da ’yan’uwa da suka zo daga Roma don su tarbe shi a “Kasuwar Abiyus, da Rumfa Uku.” (A. M. 28:15) Amma, da yake shi fursuna ne, yaya zai cika muradinsa na yin wa’azi a Roma? (Rom. 1:14, 15) Wasu suna ganin za a fara kai fursunonin wurin shugaban matsara. Idan haka ne, wataƙila an kai Bulus wurin shugaba Afranius Burrus, wanda ikonsa ya kusan kai na sarki.c Soja guda ne yake gadin Bulus, maimakon matsara da yawa. An ba Bulus izinin neman gidan haya kuma an ƙyale baƙi su riƙa ziyartarsa. Bulus ya yi musu wa’azi ba tare da wani ya hana shi ba.—A. M. 28:16, 30, 31.
BULUS YA YI WA MANYA DA ƘANANA WA’AZI
Wataƙila Sextus Afranius Burrus ya tuhumci Bulus a sansanin matsara, ko kuma a fada kafin ya kai shi gaban Nero. Bulus ya yi amfani da wannan zarafin don ya ba da “shaida ga ƙanƙanana duk da manya.” (A. M. 26:19-23) Ba mu san ko Sextus Afranius Burrus ya kama Bulus da laifi ba, amma mun san cewa bai tura shi zuwa fursuna da ke sansanin matsara ba.d
Bulus ya gayyaci shugabannan Yahudawa da kuma mutane da yawa zuwa gidansa kuma ya yi musu wa’azi. Ya kuma yi wa sojoji matsara wa’azi. Sun saurara sa’ad da Bulus yake wa Yahudawa wa’azi game da Yesu da kuma mulkin Allah “tun safiya har maraice.”—A. M. 28:17, 23.
Rukunin sojoji matsara dabam-dabam ne suke gadin fadar a kowace rana. Wataƙila ana canja sojan da ke gadin Bulus a kowace rana. Sojoji da yawa sun ji bishara ta hakan. Suna saurarawa sa’ad da yake gaya wa wani abin da zai rubuta zuwa ga Kiristoci da ke Afisa da Filibi da Kolosi da kuma Ibraniyawa. Sun kuma ga sa’ad da ya rubuta wasiƙa zuwa ga wani Kirista mai suna Filimon. Sa’ad da Bulus yake fursuna, ya taimaki wani bawa da ya gudu mai suna Unisimus. Ya zama kamar ɗa a gare shi, amma Bulus ya gaya masa ya koma wajen shugabansa. (Fil. 10) Babu shakka, Bulus yana ƙaunar sojojin da suke gadinsa. (1 Kor. 9:22) Alal misali, wataƙila ya tattauna da wani soja da ke gadinsa game da yadda ake amfani da makamai dabam-dabam, sai ya yi amfani da bayanin da ya samu don yin kwatanci a koyarwarsa.—Afis. 6:13-17.
KA ‘FAƊI MAGANAR ALLAH BAN DA TSORO’
Zaman da Bulus ya yi a ƙasar Roma a matsayin fursuna, ya taimaka wajen ‘yaɗa bishara’ ga dukan matsara da kuma wasu mutane. (Filib. 1:12, 13) Me ya sa muka ce hakan? Domin matsara sukan yi sha’ani da kusan kowa a Roma. Waɗannan sun haɗa da sarki da iyalinsa da kuma bayi. Saboda haka, mutane da yawa sun samu zarafin jin bishara, kuma wasu cikinsu sun zama Kiristoci. (Filib. 4:22) Misalin Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwa da ke Roma su ‘faɗi maganar Allah ban da tsoro.’—Filib. 1:14.
Misalin Bulus ya ƙarfafa mu mu yi wa’azin bishara “ko da dama, ko ba dama.” (2 Tim. 4:2) Alal misali, wasu a cikinmu ba sa iya fita waje, ko suna zama a gidan jinya ko a asibiti ko kuma an tsare su a fursuna don imaninsu. Ko da wane irin yanayi muke ciki, muna iya yin wa’azi ga waɗanda muka haɗu da su. Waɗannan sun ƙunshi waɗanda suka zo su kula da mu ko su taimaka mana da wasu ayyuka. Idan muka yi wa’azi a kowane zarafi da muka samu, muna nuna cewa babu abin da zai hana “maganar Allah” yaɗuwa.—2 Tim. 2:8, 9.
a Ka duba akwatin nan “Aikin Matsari a Zamanin Sarki Nero.”
b Akwai kusan sojoji 1,000 a cikin kowane rukunin sojojin ƙasar Roma.
c Ka duba akwatin nan “Wane ne Sextus Afranius Burrus?”
d Kaisar Tiberius ya saka Hiridus Agaribas a fursuna a shekara ta 36/37 a zamaninmu, don ya ce yana fatan cewa Caligula zai zama sarki ba da daɗewa ba. Bayan Caligula ya zama sarki, sai ya sāka wa Hiridus ta wajen naɗa shi sarkin Yahudiya.—A. M. 12:1.