Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 2/15 pp. 3-7
  • Wannan Ne Gādonmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wannan Ne Gādonmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MUNA DA GĀDO MAI TAMANI
  • JEHOBAH YA ADANA KALMARSA
  • JEHOBAH YA ADANA SUNANSA
  • JEHOBAH YA ADANA KOYARWA TA GASKIYA
  • JEHOBAH YA HANA SHAIƊAN ƁOYE GASKIYA
  • Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Gadōnmu Mai Tamani—Menene Yake Nufi A Gare Ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 2/15 pp. 3-7

Wannan Ne Gādonmu

“Gādon bayin Ubangiji ke nan.”—ISHA. 54:17.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne Allah ya yi don ya kāre Littafi Mai Tsarki?

  • Ta yaya Jehobah ya adana sunansa domin mutanensa su yi amfani da shi?

  • Ta yaya Jehobah ya sa muka san koyarwa ta gaskiya a yau?

1. Mene ne Jehobah ya adana domin amfanin ’yan Adam?

JEHOBAH zai dawwama, kuma ya gaya mana abin da muke bukatar mu yi don mu rayu har abada. Har ila abubuwan da ya gaya mana ba su canja ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar Ubangiji ta tabbata har abada.” (1 Bit. 1:23-25) Muna godiya sosai domin Jehobah ya adana maganarsa mai muhimmanci a cikin Littafi Mai Tsarki.

2. Mene ne Allah ya adana don amfanin mutanensa a cikin Littafi Mai Tsarki?

2 Jehobah yana son dukanmu mu san sunansa. Lokaci na farko da aka ambata sunan nan Jehobah a Littafi Mai Tsarki, shi ne sa’ad da yake bayyana yadda ya halicci sama da duniya. (Far. 2:4) Allah ya rubuta sunansa sau da yawa ta hanyar mu’ujiza, a allunan dutse da ke ɗauke da Dokoki Goma. Alal misali, doka ta farko ta ce: ‘Ni ne [Jehobah, NW] Allahnka.’ (Fit. 20:1-17) Har wa yau, an san sunan Allah domin Ubangiji Jehobah Mamallaki ya kāre Kalmarsa da kuma sunansa, duk da ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya kawar da su.—Zab. 73:28.

3. Mene ne Allah ya adana a cikin Kalmarsa, duk da koyarwa ta ƙarya da ta zama gama gari?

3 Jehobah ya kuma adana koyarwa ta gaskiya a cikin Kalmarsa. Muna godiya sosai domin Allah ya sa mun samu koyarwa ta gaskiya, duk da cewa koyarwa ta ƙarya gama gari ce a yau. (Karanta Zabura 43:3, 4.) Duniya tana cikin duhu, amma mu muna cikin haske da Jehobah yake tanadarwa.—1 Yoh. 1:6, 7.

MUNA DA GĀDO MAI TAMANI

4, 5. Wane babban gata ne aka ba mu tun a shekara ta 1931?

4 Mutane suna da al’adu da halaye da kuma salon rayuwa dabam-dabam. Kowace tsara takan gāji waɗannan al’adun kuma ta koya wa ta gaba. A matsayin Shaidun Jehobah, mu ma muna da wani gādo. Jehobah ya sa mun koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da shi da kuma nufe-nufensa. Ban da haka ma, ya ba mu gata na musamman na zama masu ɗauke da sunansa.

5 Mun soma more wannan gatan sa’ad da aka yi wani babban taro a birnin Columbus, Ohio da ke ƙasar Amirka, a shekara ta 1931. An saka wasu harufa biyu a tsarin ayyukan taron, kuma ’yan’uwan da suka halarci taron sun yi ta ƙoƙari su san ma’anarsu. Ashe, waɗannan harufan suna wakiltar sabon sunanmu. Kafin wannan lokacin, ana kiranmu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Amma, a ranar Lahadi, 26 ga Yuli, 1931, sai muka soma amfani da sunan nan Shaidun Jehobah. Wannan ranar farin ciki ne sosai, domin mun soma amfani da sabon sunan da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ishaya 43:12.) Wani ɗan’uwa ya ce: “Ba zan taɓa manta da irin tafin da kuma ihun da aka yi ranar ba.” Sauran mutane a duniya sun tsani wannan sunan, amma Allah ya yarda mana mu amsa wannan suna mai tamani har fiye da shekaru 80 yanzu. Hakan ba ƙaramin gata ba ne.

6. Gādonmu ya haɗa da wane bayani?

6 Wani gādo da muke da shi kuma, shi ne sahihan tarihi mai tamani game da bayin Allah da ke cikin Littafi Mai tsarki. Ka yi la’akari da misalin Ibrahim da Ishaku da kuma Yakubu. Babu shakka, sun tattauna da iyalinsu game da salon rayuwar da ke faranta wa Jehobah rai. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne cewa Yusufu ya ƙi yin lalata don ba ya son ya “yi zunubi ga Allah.” (Far. 39:7-9) Kiristoci na ƙarni na farko sun koya wa juna game da Allah. Alal misali, Bulus ya gaya wa ikilisiya abin da Yesu ya koya masa game da Jibin Maraice na Ubangiji. (1 Kor. 11:2, 23) An rubuta dukan waɗannan bayanan a cikin Littafi Mai Tsarki don su taimaka mana mu san yadda za mu bauta wa Allah. (Karanta Yohanna 4:23, 24.) Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa dukan mutane, amma mu bayin Jehobah ne ya kamata mu fi nuna godiya dominsa.

7. Wane alkawari ne ya zama gādonmu?

7 A yau ma, Jehobah yana taimaka wa bayinsa. (Zab. 118:7) Littattafanmu sun bayyana yadda Jehobah yake kāre bayinsa. Hakan yana sa mu kasance da gaba gaɗi cewa zai kāre mu, ko idan ana tsananta mana. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari mai daɗaɗa zuciya, kuma wannan ma gādonmu ne. Ya ce: “Babu alatun da aka halitta domin cutarki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi. Gādon bayin Ubangiji ke nan, adalcinsu wanda shi ke daga wurina, in ji Ubangiji.” (Isha. 54:17) Tabbas, Shaiɗan ba zai iya yi mana lahani na dindindin ba.

8. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?

8 Shaiɗan ya ƙoƙarta ya halaka Littafi Mai Tsarki, ya hana mutane sanin sunan nan Jehobah da kuma koyarwa ta gaskiya. Amma, bai yi nasara ba. A wannan talifin da kuma na gaba, za mu tattauna (1) yadda Allah ya adana Littafi Mai Tsarki da (2) yadda Jehobah ya tabbata cewa mutane sun san sunansa da kuma (3) yadda Ubanmu na sama ya sa ya yiwu mu samu koyarwa ta gaskiya.

JEHOBAH YA ADANA KALMARSA

9-11. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Jehobah ya kāre Littafi Mai Tsarki?

9 Jehobah ya kāre Littafi Mai Tsarki, duk da yake mutane sun yi ƙoƙari su halaka shi. Wani littafin tarihi ya ce: “A shekara ta 1229, Limaman birnin Toulouse sun hana mutane yin amfani da Littafi Mai Tsarki da aka fassara. Sun yi hakan don su shawo kan wani rukunin addini da ake kiran Albigenses da Waldenses. . . . An ba da irin wannan kashedin ma a wani taron da aka yi a shekara ta 1234 a birnin Tarragona, a ƙasar Sifen, ƙarƙashin ja-gorancin James na Ɗaya. . . . Limaman Roma sun saka hannu a batun a lokaci na farko a shekara ta 1559, sa’ad da Paul na Huɗu ya hana a buga ko kuma a samu Littafi Mai Tsarki da aka fassara ba tare da izini ba.”

10 Jehobah ya kāre Littafi Mai Tsarki duk da ƙoƙarin da aka yi a halaka shi. A shekara ta 1382, John Wycliffe da abokansa suka soma fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci. Bayan haka, sai William Tyndale ya yi nasa fassara zuwa Turanci, kuma saboda haka ne aka kashe shi a shekara ta 1536. Sa’ad da yake kan gungumen da aka ɗaure shi, ya yi ihu cewa: “Ya Ubangiji, ka wayar da kan sarkin Ingila.” Sai aka maƙure shi, kuma aka ƙone gawarsa.

11 A shekara ta 1535, wani Miles Coverdale ya fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci. Ya yi amfani da wasu sassa na fassarar Tyndale, kuma ya yi amfani da fassarar yaren Latin da na Martin Luther da ke yaren Jamus don fassara sauran sassan. A zamaninmu, muna da New World Translation of the Holy Scriptures a Turanci. Wannan fassarar ta yi daidai da rubutu na asali kuma ba ta da wuyan fahimta. Tana kuma da sauƙin yin wa’azi da ita. Muna farin ciki sosai don Shaiɗan da kuma ’yan Adam ba su iya halaka Kalmar Allah ba.

JEHOBAH YA ADANA SUNANSA

12. Ta yaya New World Translation ya taimaki mutane su san sunan Jehobah?

12 Jehobah ya tabbata cewa ba a kawar da sunansa daga cikin dukan Littafi Mai Tsarki ba. ’Yan’uwan da suka wallafa New World Translation, sun tabbata cewa sun yi amfani da sunan nan Jehobah a dukan wuraren da yake a cikin rubutu na asali. Sunan ya bayyana sau 6,973 a Nassosin Ibrananci da kuma sau 237 a Nassosin Helenanci. A yanzu, an fassara New World Translation zuwa fiye da harsuna 116, kuma an buga kofofi fiye da 178,545,862.

13. Me ya sa za mu ce mutane sun san sunan Allah tun lokacin da aka halicci ’yan Adam?

13 Ba yau ba ne mutane suka soma amfani da sunan Allah ba. Adamu da Hawwa’u sun san wannan sunan kuma sun yi amfani da shi. Nuhu ma ya yi amfani da shi sa’ad da ɗansa Ham ya yi masa rashin kunya bayan Rigyawa. Ya ce: “Mai-albarka ne [Jehobah, NW] Allah na Shem; Kan’ana [ɗan Ham] kuma shi zama bawansa.” (Far. 4:1; 9:26) Allah kansa ma ya yi amfani da sunansa. Ya ce: “Ni ne [Jehobah, NW]; wannan ne sunana: ba ni kuwa bada ɗaukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassaƙaƙu.” Ya daɗe cewa: “Ni ne [Jehobah], babu wani kuma; banda ni babu Allah kuma.” (Isha. 42:8; 45:5) Jehobah ya sa ya yiwu mutane a duk faɗin duniya su san sunansa. Babban gata ne cewa muna amfani da wannan sunan, kuma mu Shaidunsa ne. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin sunan Allahnmu za mu kafa tutoshinmu.”—Zab. 20:5.

14. Ban da Littafi Mai Tsarki, a wane wuri ne kuma za a ga sunan Allah?

14 Ba Littafi Mai Tsarki kaɗai ba ne ke ɗauke da sunan Allah. Alal misali, sunan ya bayyana a wani Dutse da ke garin Dhiban (Dibon) mai nisan mil 13 daga gabashin Tekun Gishiri a ƙasar Mowab. A jikin dutsen, an rubuta Omri, sarkin Isra’ila, da kuma abin da Mesha, sarkin Mowab ya faɗa game da yaƙin da ya yi da ƙasar Isra’ila. (1 Sar. 16:28; 2 Sar. 1:1; 3:4, 5) Amma, abin da ya fi muhimmanci game da wannan dutsen shi ne yana ɗauke da sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu, wato YHWH. An kuma rubuta waɗannan baƙaƙe sau da sau a harufan yaren Lachish, a jikin wasu gutsurorin tulun laƙa da aka tono a ƙasar Isra’ila.

15. Mece ce ake kira Septuagint, kuma me ya sa aka bukace ta?

15 Mafassaran Littafi Mai Tsarki na farko sun taimaka wajen kāre sunan Allah. Bayan bautar da suka yi a ƙasar Babila a shekara ta 607 zuwa 537 kafin zamaninmu, Yahudawa da yawa ba su koma Yahuda da kuma Isra’ila ba. Kuma da shigewar lokaci, sai Yahudawa da yawa suka ƙaura zuwa birnin Iskandariya na ƙasar Masar. Waɗannan Yahudawan suna bukatar Nassosin Ibrananci da aka fassara zuwa Helenanci, domin yaren da ake yi a kusan duk faɗin duniya ke nan a lokacin. Wannan fassarar ce ake kira Septuagint, kuma wasu suna ɗauke da sunan Allah da aka rubuta da harufan Ibrananci.

16. Ta yaya wani littafin da aka buga a shekara ta 1640 ya yi amfani da sunan Allah?

16 Littafi na farko da aka wallafa a yankunan Amirka shi ne Littafin Zabura da aka fassara daga Ibrananci zuwa Turanci. Wannan Littafin yana ɗauke da sunan Allah. An soma buga shi a shekara ta 1640, kuma ana kiran shi Bay Psalm Book. A wannan fassarar, an yi amfani da sunan Allah a Zabura 1:1, 2, wanda ya ce “mai albarka ne mutum” wanda bai bi shawarar miyagu ba, amma “yana son dokar Iehovah.” Don ƙarin bayani game da sunan Allah, ka duba ƙasidar nan The Divine Name That Will Endure Forever, a Turanci.

JEHOBAH YA ADANA KOYARWA TA GASKIYA

17, 18. (a) Mece ce gaskiya? (b) “Gaskiyar bishara” ta ƙunshi waɗanne koyarwa?

17 Muna farin cikin bauta wa Jehobah “Allah na gaskiya.” (Zab. 31:5) Mece ce gaskiya? Gaskiya ita ce bayyani dalla-dalla game da wani abu. A harsunan da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da kalmar nan “gaskiya” don a nuna cewa abin da ake zancensa daidai ne, kuma za a iya amincewa da shi.

18 Jehobah ya adana koyarwa ta gaskiya, kuma yana taimaka mana mu ci gaba da saninta. (2 Yoh. 1, 2) Hakan ya yi daidai da abin da muka koya a cikin littafin Misalai 4:18 da ya ce: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” Sa’ad da Yesu yake addu’a ga Allah, ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” Kuma mun yarda da hakan. (Yoh. 17:17) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da “gaskiyar bishara,” kuma an ɗauko dukan imaninmu a matsayin Kiristoci daga cikinsa ne. (Gal. 2:14) Waɗannan abubuwa da muka gaskata sun ƙunshi sunan Allah Jehobah, da ikonsa na yin sarauta bisa halittunsa da hadayar fansa ta Yesu da tashin matattu da kuma Mulkinsa. Yanzu za mu mai da hankali ga yadda Allah ya adana koyarwa ta gaskiya duk da ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya ɓoye ta.

JEHOBAH YA HANA SHAIƊAN ƁOYE GASKIYA

19, 20. Wane ne Nimrod, kuma mene ne mutane suka yi ƙoƙarin yi a zamaninsa?

19 Bayan Rigyawa, an yi wani mafarauci mai suna Nimrod, wanda ya yi ‘gāba da Ubangiji.’ (Far. 10:9) Da yake Nimrod ya yi gāba da Jehobah Allah, babu shakka, Shaiɗan ne ya yi wa sujada. Hakan ya yi daidai da magabtan da Yesu ya ce musu: “Ku na ubanku Shaiɗan ne, ƙyashe ƙyashe na ubanku kuma kuna da nufi ku yi. Ba ya tsaya a kan gaskiya ba.”—Yoh. 8:44.

20 Nimrod ya yi sarauta bisa birnin Babel da kuma biranen da ke tsakanin kogin Tigris da Yufiretis. (Far. 10:10) Wataƙila shi ne ya ja-goranci gina birnin Babel da hasumiyarsa a shekara ta 2269 kafin zamaninmu. Waɗannan maginan sun yi abin da ya saɓa wa nufin Jehobah, don sun ce: “Mu je, mu gina birni, da hasumiya, wadda kanta za ta kai har sama, mu yi wa kanmu suna; kada mu warwatsu a fuskar dukan duniya.” Amma, ba su iya kammala ginin ba domin Allah “ya dama harshen dukan duniya” kuma ya warwatsar da maginan. (Far. 11:1-4, 8, 9) Shaiɗan ya so ya kawar da bauta ta gaskiya kuma ya sa kowa ya soma bauta masa. Amma, bai yi nasara ba Jehobah ya kāre bauta ta gaskiya. Kuma a kowace wayewar gari, mutane suna rungumar bauta ta gaskiya.

21, 22. (a) Me ya sa za a ce bauta ta ƙarya, ba ta taɓa rinjayar bauta ta gaskiya ba? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Bauta ta ƙarya ba ta taɓa rinjayar bauta ta gaskiya ba. Me ya sa muka ce hakan? Domin Jehobah mai-koyarwa mai-girma ya tabbata cewa mun sami Littafi Mai Tsarki kuma mun san sunansa da kuma koyarwa ta gaskiya. (Isha. 30:20, 21) Idan muka bauta wa Allah a hanyar da ta dace, za mu yi farin ciki sosai. Amma, muna bukatar mu yi imani da koyarwa ta gaskiya, kuma mu bi ja-gorar da Jehobah yake mana ta wajen ruhunsa mai tsarki.

22 A talifi na gaba, za mu koyi tushen wasu koyarwa ta ƙarya game da Allah. Za mu ga yadda suka saɓa da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Kuma za mu ga cewa Jehobah ya yi mana albarka ta wajen koya mana gaskiya. Hakika, dukan waɗannan gādo ne masu tamani.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba