Ka Kusaci Allah
‘Ni Ba Zan Manta da Ke Ba’
ALLAH yana kula da mutanensa da gaske? Idan amsar e ce, ya damu da su sosai kuwa? Za mu iya sanin haka ne daga abin da Allah ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. Jehobah ya bayyana yadda yake ji game da mutanensa. Ka yi la’akari da kalmomin da ke Ishaya 49:15.
Jehobah ya yi amfani da kwatanci mai matuƙar sosa rai don ya nuna irin ƙaunar da yake yi wa mutanensa. Ya soma ne da yin wannan tambaya mai sa tunani: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin ɗan cikinta ba?” Kamar dai amsar a fili take. Zai yi wuya mai jego ta manta da jaririnta. Jaririnta ya dogara ne da ita dare da rana, kuma yakan yi kuka idan yana son wani abu. Amma, amsar wannan tambayar da Jehobah ya yi ba ta tsaya a nan ba.
Me ya sa mai jego take ba jaririnta nono kuma take kula da dukan bukatunsa? Don ya daina kuka ne kawai? A’a. Mahaifiya tana “juyayin ɗan cikinta.” Juyayin da uwa take nuna wa jaririnta da take shayarwa yana ɗaya daga cikin motsin rai mafi girma na mutane.
Abin baƙin ciki, ba kowace mai jego ce ke tausaya wa jaririnta ba. “Ya yiwu waɗannan su manta,” in ji Jehobah. A yau mutane da yawa a duniya sun zama “marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a.” (2 Timotawus 3:1-5) A wasu lokatai, muna jin labarin iyaye mata da suka azabtar da jaririnsu, ko kuma waɗanda suka gudu suka bar jaririnsu. Wani littafin da ke ɗauke da bayani a kan littafin Ishaya 49:15, ya nuna cewa “iyaye mata ajizai ne kuma hakan yana shafan yadda suke nuna ƙauna.” Hakan ya nuna cewa ƙauna mafi girma na ’yan Adam tana iya mutuwa.
Amma Jehobah ya tabbatar wa duk wani mai bauta masa cewa ‘Ni ba zan manta da kai ba.’ Mun fara fahimtar bayanin da Jehobah yake son ya yi a wannan tambayar da ke Ishaya 49:15, ko ba haka ba? Abin da yake cewa a nan shi ne, ya fi uwa ajiza nuna tausayi sosai. Akasin uwaye ajizai da suke iya ƙin tausaya wa jaririnsu, Jehobah ba zai taɓa daina tausaya wa bayinsa a lokacin da suke neman taimako ba. Shi ya sa littafin binciken da aka ambata a sama ya ce game da Ishaya 49:15: “A cikin Tsohon Alkawari, ana ganin cewa wannan shi ne furuci mafi ƙarfi da ya bayyana ƙaunar Allah.”
Abin ƙarfafawa ne mu koya game da “jinƙai mai-taushi na Allahnmu”, ko ba haka ba? (Luka 1:78) Me zai hana ka koyi yadda za ka kusaci Jehobah. Wannan Allah mai ƙauna ya tabbatar wa masu bauta masa cewa: ‘Har abada ba zan bar ku ba. Har abada kuma ba zan yashe ku ba.’—Ibraniyawa 13:5.