Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/1 p. 8
  • Sanin Amsoshin Yana da Wani Muhimmanci Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sanin Amsoshin Yana da Wani Muhimmanci Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yesu Kristi Yadda Saƙonsa Ya Shafe Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/1 p. 8

Sanin Amsoshin Yana da Wani Muhimmanci Ne?

‘Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.’—YOHANNA 8:32.

LITTAFI MAI TSARKI yana ɗauke da gaskiyar da za ta iya ’yanta mu daga ra’ayoyi masu ruɗarwa game da Yesu. Amma, abin da muka gaskata game da Yesu yana da wani muhimmanci ne? Hakika, yana da muhimmanci. Yana da muhimmanci ga Jehobah da Yesu. Kuma ya kamata ya kasance da muhimmanci a gare mu.

● Me ya sa yake da muhimmanci ga Jehobah? Domin “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Jehobah yana son mu zauna har abada cikin farin ciki. Yesu ya ce: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya [’yan Adam] har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi . . . ya sami rai madawwami.” (Yohanna 3:16, Littafi Mai Tsarki) Allah ya aiko da Ɗansa don ya zama Mai Cetonmu kuma ya ba mu damar yin rayuwa a Aljanna a duniya har abada, kamar yadda Ya nufa tun asali. (Farawa 1:28) Allah yana marmarin ba da kyautar rai na har abada ga waɗanda suka koyi gaskiya game da Ɗansa kuma suka yi rayuwar da ta jitu da abin suka koya.—Romawa 6:23.

● Me ya sa yake da muhimmanci ga Yesu? Yesu ma yana ƙaunar ’yan Adam. Ya nuna cewa yana ƙaunarmu sa’ad da ya sadaukar da ransa domin mu. (Yohanna 15:13) Ya fahimci cewa mutane za su iya samun ceto ne kawai idan ya ba da ransa. (Yohanna 14:6) Bai kamata mu yi mamaki ba cewa Yesu yana son mutane da yawa su amfana daga fansarsa. Shi ya sa Yesu ya umurci mabiyansa na gaskiya su koya wa mutane nufin Allah a faɗin duniya.—Matta 24:14; 28:19, 20.

● Ya kamata ya kasance da muhimmanci ne a gare mu? Ka ɗan yi tunani a kan abubuwan da ka ɗauka da muhimmanci sosai, wato, lafiyar jikinka da kuma iyalinka. Kana marmarin samun ƙoshin lafiya da kuma rayuwa mafi daɗi wa kanka da kuma waɗanda kake ƙauna? Ta hanyar Yesu, Jehobah ya ba kai da waɗanda kake ƙauna begen yin rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya ba tare da azaba ko wahala ba. (Zabura 37:11, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Za ka so ka yi rayuwa a cikin irin wannan duniyar? Idan amsarka e ce, akwai abin da kake bukatar ka yi.

Ka sake duba nassin da aka yi ƙaulinsa a ƙarƙashin jigon wannan talifin: ‘Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.’ Gaskiya game da Yesu da kuma rawar da ya taka wajen cika nufin Allah za ta iya ’yanta mu daga zunubi da mutuwa. Amma idan kana son ka samu wannan ’yancin, kana bukatar ka “san gaskiya.” Me zai hana ka ƙara koyan wannan gaskiyar da kuma yadda kai da waɗanda kake ƙauna za ku amfana daga hakan? Shaidun Jehobah za su yi farin cikin koya maka hakan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba