Bala’i—Me Ya Sa Suka Yi Yawa Haka?
LABARAN da suka fi yaɗuwa a kafofin labari su ne na bala’i. Mutane da yawa suna faɗa wa bala’i dabam-dabam. Wata Cibiyar Bincike ta Yaɗuwar Bala’i, a ƙasar Belgium, ta ba da rahoto cewa a shekara ta 2010 kaɗai bala’i guda 373 ne suka auku kuma aƙalla mutane 296,000 ne suka rasa rayukansu a sakamakon haka.
A cikin shekaru da dama da suka shige, rahotannin bala’in da ke faruwa sun ƙaru sosai. Alal misali, a tsakanin shekara ta 1975 da 1999, bala’i ƙasa da 300 ne suka auku a kowace shekara. Amma a tsakanin shekara ta 2000 da kuma 2010, kusan bala’i 400 ne suka auku a kowace shekara. Mai yiwuwa kana cikin waɗanda suke mamaki cewa, ‘Me ya sa bala’i da yawa suke faruwa ne yanzu?’
Ko da yake mutane da yawa suna kiran waɗannan bala’in “ayyukan Allah,” bala’i ba ayyukan Allah ba ne ba. Ba Allah ba ne yake haddasa bala’in da suke addabar mutane da yawa a yau ba. Amma, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa bala’i za su auku a zamaninmu. Alal misali, a Matta 24:7, 8, kalmomin Yesu sun ce: “Za a yi yunwa da rayerayen duniya wurare dabam dabam. Amma dukan waɗannan al’amura mafarin wahala ne.” Me ya sa Yesu ya annabta cewa waɗannan abubuwan za su auku, kuma mene ne ma’anar su a gare mu?
Ɗan Allah, Yesu yana amsa tambayar da aka yi masa ne: “Mecece alamar . . . ƙarewar zamani?” (Matta 24:3; Littafi Mai Tsarki) Ya ambata abubuwa dabam-dabam da za su faru, har da irin bala’in da aka ambata a sama. Sai ya yi wannan furuci mai muhimmanci: “Lokacinda kun ga waɗannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.” (Luka 21:31) Saboda haka, waɗannan bala’in suna da ma’ana mai girma a gare mu. Suna nuni ne ga lokacin da za a samu gagarumin canji nan ba da daɗewa ba.
Abubuwan da ke Jawo Bala’i
Duk da haka, mutane da yawa suna cewa, Idan ba Allah ne yake haddasa bala’i ba, to waye ne ko kuma mene ne ke haddasa su? Za mu gane amsar ne kawai idan muka fahimci wata muhimmiyar gaskiya da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” (1 Yohanna 5:19) Wannan ayar ta nuna cewa ba Allah ba ne yake haddasa munanan abubuwan da ke faruwa a duniya, amma a yawancin lokaci, maƙiyinsa ne, “Shaitan,” wanda Littafi Mai Tsarki ya kira “Iblis.”—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.
Domin son kansa, wannan maƙiyin Allah ya ɗauki mutane a matsayin abubuwan da za a iya watsarwa. Da yake dukan duniya tana ƙarƙashin ikonsa, ya sa irin wannan halin ya yi tasiri a tsakanin mutane. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya annabta hakan sa’ad da ya ce a “kwanaki na ƙarshe,” mutane za su zama “masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai.” (2 Timotawus 3:1, 2) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Iblis ya ƙirƙiro wani irin tsari a duniya wanda yake yaɗuwa sa’ad da mutane suka nuna irin waɗannan munanan halaye da makamancin hakan. Yana sa mutane su kasance masu haɗama da kuma son kai, halayen da ke jefa mutane cikin haɗari.
A wace hanya ce wannan tsari na duniya da ke cike da haɗama yake jawo bala’i? Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya a kan bala’i a duniya ya bayyana cewa: “Sau da yawa jama’a suna zama ne a wurare masu haɗari kamar su bakin kogi. Ƙari ga haka, sare itutuwan daji da kuma rufe wuraren da ruwa ke taruwa yana ƙara yiwuwar jefa mahalli cikin haɗari. Mafi girma a cikin waɗannan abubuwan shi ne barazana na canjin yanayi da kuma yawan ruwa a sakamakon iska mai guba da mutane ke fitarwa da ke yaɗuwakuma hakan yana jawo dumamar yanayi a Duniya.” Ko da yake an ce ana yin yawancin waɗannan ‘ayyuka na mutane’ don bunƙasa tattalin arziki ne, amma gaskiyar ita ce, ana yin ayyukan nan ne saboda son kai da haɗama da suka mamaye duniya.
Saboda haka, masana da yawa a yanzu sun gano cewa ayyukan da ’yan Adam suke yi ba tare da yin tunani ba sun ƙara yawan munanan sakamakon da bala’i ke jawowa. Hakika, ’yan Adam suna tallafa wa tsarin da Iblis yake amfani da shi don ya daɗa wahalar da ’yan Adam suke sha sa’ad da bala’i ya auku.
Saboda haka, mun ga cewa ayyukan da muntane ke yi ba tare da tunani ba su ne ke haddasa yawancin bala’in da ke aukuwa. Wasu bala’in suna kasancewa da mugun sakamako ne saboda wuraren da suka faru. A sassa da yawa a duniya, sakamakon bala’in da ke faruwa suna ƙara muni ne saboda ayyukan mugayen mutane ko kuma domin mutane da yawa suna zaune ne a wuraren da ke da haɗari saboda talauci ko wariya da ya zama ruwan dare a yau a duniya. Hakika, wasu mutane suna shan wahala sa’ad da bala’i ya auku ba domin laifi ko sakacin wani ba, amma domin “sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.”—Mai-Wa’azi 9:11; LMT.
Ko da mene ne ya jawo hakan, idan ka faɗa cikin bala’in da yanayi yake jawowa, ta yaya za ka jure? Yanzu za mu duba abin da za a iya yi domin a sauƙaƙa sakamakon hakan sa’ad da bala’i suka suka auku.
[Hoton da ke shafi na 5]
Cunkoso
[Hoton da ke shafi na 5]
Sare itatuwa
[Hoton da ke shafi na 5]
Gurɓata mahalli
[Wuraren da aka Ɗauko 5]
A hagu: © Mark Henley/Panos Pictures Middle: © Jeroen Oerlemans/Panos Pictures