Jimrewa da Waɗannan Matsalolin
Domin yawan aukuwa da kuma ƙarin munin bala’i, mene ne mutum zai iya yi domin ya jimre da su? Bari mu duba matakai masu amfani da za a iya ɗauka.
Ka guji bala’i. “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Misalai 22:3) Wannan shawara ce mai kyau da za ta iya taimakawa a lokacin bala’i. Idan aka yi gargaɗi cewa wani dutse zai yi aman wuta, ko za a yi ambaliyar ruwa, ko kuma za a yi ruwa da iska mai ƙarfi, zai kasance hikima idan waɗanda suke zaune a wannan wurin suka ƙaura zuwa inda babu haɗari. Rai ya fi gida ko dukiya tamani.
Yana yiwuwa wasu su guji zama a wurin da haɗari zai iya aukuwa. Wata majiya ta ce: “Aukuwar bala’i a yawancin lokaci ta dangana ne ga ɓangaren duniya. Bala’i sun cika aukuwa ne a wasu ɓangarori kaɗan na Duniya kuma yawancin bala’i masu girma da za su faru a nan gaba za su auku ne a wuraren nan.” Alal misali, hakan zai iya faruwa a ƙasashen da ke gaɓar teku ko kuma wuraren da ke kusa da inda ƙasa ta tsage. Idan za ka iya guje wa zama a irin waɗannan wurare masu haɗari ko kuma ka ƙaura zuwa inda babu haɗari, za ka iya rage yiwuwar faɗawa cikin bala’i.
Ka tsara abin da za ka yi. Duk da matakan da ka ɗauka, kana iya samun kanka a inda bala’i ya faru ba zato. Idan ka tsara abin da za ka yi kafin hakan ya faru, tsira daga bala’i zai kasance maka da sauƙi. Wannan ya jitu da shawarar da ke Misalai 22:3, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu. Kana da abubuwan da ka riga ka ajiye da za ka ɗauka cikin sauƙi a lokacin gaggawa? Littafin nan, 1-2-3 of Disaster Education ya ambata cewa mutum zai iya yin tanadin waɗannan abubuwan da ke gaba: Kayan jinyar gaggawa, ruwan kwalaba, abincin da ba zai lalace ba, da kuma muhimman takardu. Zai dace sosai ka tattauna da iyalinka game da irin bala’in da za su iya aukuwa a inda kuke da kuma irin matakan da za ku ɗauka idan hakan ya faru.
Ka kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Hakan zai iya taimakawa a kowane yanayi. Littafi Mai Tsarki ya kira Allah “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” Wata aya dabam ta kwatanta shi a matsayin Allah “wanda yake yi ma masu-tawali’u ta’aziya.”—2 Korintiyawa 1:3, 4; 7:6.
Hakika, Allah yana sane da abin da ke faruwa da waɗanda suka dogara da shi. Shi Allah ne mai ƙauna kuma yana ƙarfafa mutanensa a hanyoyi dabam-dabam. (1 Yohanna 4:8) Yin addu’a ba don mu’ujiza ba, amma don samun ruhu mai tsarki mai iko na Allah zai iya taimakawa a kowane yanayi. Ruhu mai tsarki zai iya sa waɗanda suke fuskantar masifu su tuna nassosin Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa su kuma su sanyaya musu zuciya. Hakika, bayin Allah masu aminci za su iya ji kamar yadda Dauda, sarkin Isra’ila ta dā ya ji, wanda ya ce: “Hakika, ko tafiya ni ke yi ta tsakiyar kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron kowace masifa ba, gama kana tare da ni: sandarka da kerenka suna yi mani ta’aziya.”—Zabura 23:4.
’Yan’uwa Kiristoci suna taimaka wa juna. A ƙarni na farko, wani Kirista mai suna Agabus ya annabta cewa “za a yi babbar yunwa ko’ina cikin duniya: wannan kuwa cikin zamanin Kuludiyus ya faru.” Wannan yunwar ta shafi almajiran Yesu da yawa da ke Yahudiya. Mene ne almajiran da ke wasu wurare dabam suka yi sa’ad da suka sami labarin wahalar da waɗannan ’yan’uwansu Kiristoci suke sha? Labarin ya ce: “Masu bi fa, kowane mutum gwargwadon abin da ya iya, suka kudurta su aike gudunmuwa ga ’yan’uwa da ke zaune cikin Yahudiya.” (Ayyukan Manzanni 11:28, 29) Sun kai agaji saboda ƙauna.
Bayin Allah suna yin hakan sa’ad da bala’i mai tsanani ya auku a yau. An san Shaidun Jehobah sosai da taimaka wa ’yan’uwansu masu bi. Alal misali, sa’ad da aka yi wata girgizar ƙasa mai tsanani a ƙasar Chile a ranar 27 ga Fabrairu, 2010, nan da nan Shaidun Jehobah suka kai agaji ga waɗanda abin ya shafa. Karla, wadda ambaliya ta kwashe gidanta, ta ce: “Ganin [’yan’uwa Kirista] a washegari sun zo su taimaka mana daga wurare dabam-dabam ya ƙarfafa mu. Babu shakka, Jehobah ya ƙarfafa mu ta wurin alherin waɗannan ’yan’uwan. Na shaida ƙauna da kuma kāriya.” Kakanta, wanda ba Mashaidi ba ne, ya ga irin taimakon da aka bayar. Ya ce: “Wannan ya bambamta da abin da na saba gani a cocin mu.” Abin da ya gani ya motsa shi ya gaya wa Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
Yin tarayya da waɗanda suke ƙaunar Allah yana taimakawa sosai a lokacin masifa. Duk da haka, da akwai lokacin da ba za a ƙara samun bala’i a duniya ba? Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan wannan batun.
[Hoton da ke shafi na 6]
Shin, ka shirya abubuwan da za ka ɗauka a lokacin gaggawa?
[Hoton da ke shafi na 7]
Yin addu’a, ba don mu’ujiza ba, amma don samun ruhu mai tsarki mai iko na Allah, zai iya taimakawa a kowane yanayi
[Hoton da ke shafi na 7]
’Yan’uwa Kiristoci suna taimaka wa juna su magance sakamakon bala’i
[Hoton da ke shafi na 7]
“Na shaida ƙauna da kāriya”