Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 p. 3
  • Allah Yana Yi Mana Horo Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Yana Yi Mana Horo Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bala’i?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Bala’i—Me Ya Sa Suka Yi Yawa Haka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Jimrewa da Waɗannan Matsalolin
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 p. 3

Allah Yana Yi Mana Horo Ne?

“Ina ganin tembatsu ne (wato, horo daga sama), ko da yake na tausaya ma waɗanda bala’in ya faɗa musu,” in ji wani babban ɗan siyasa a Japan bayan girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da kuma ambaliyar teku (tsunami) da suka auku a watan Maris 2011.

Sa’ad da mutane fiye da 220,000 suka halaka a girgizar ƙasar da ta auku a ƙasar Haiti a watan Janairu 2010, wani shahararren mai wa’azi a talabijin ya ce mutanen sun “bi hanyar iblis ne” kuma suna bukatar su “tuba su koma ga alla.”

“Allah yana son ya ta da mataccen lamirinmu ne,” in ji wani firist na Katolika sa’ad da mutane 79 suka rasu bayan an tattake su a birnin Manila a Philippines. Wata jarida a wurin ta ba da rahoto cewa “kashi ashirin da ɗaya na mutanen da suka manyanta sun gaskata cewa Allah yana nuna fushinsa ne ta wajen yin amfani da zamewar ƙasa, guguwa da sauran bala’in” da suke addabar ƙasar a yawancin lokaci.

RA’AYIN da mutane suke da shi cewa Allah yana kawo bala’i ne domin ya hukunta miyagun mutane ba sabon abu ba ne. A shekara ta 1755, bayan mutane 60,000 sun halaka a girgizar ƙasa da wuta da ambaliyar teku a birnin Lisbon, Portugal, wani sanannen ɗan falsafa Voltaire ya yi wannan tambayar: “Zunubin da ake yi a Lisbon da aka halaka ya fi na mazauna Paris ne waɗanda suke aikata mugun zunubi kuma suna cike da farin ciki?” Hakika, miliyoyin mutane suna tunanin ko Allah yana amfani ne da bala’in don ya yi wa mutane horo. A ƙasashe da yawa ana kiran waɗannan bala’i ayyukan Allah.

Saboda waɗannan abubuwan, muna bukatar mu yi wannan tambayar: Da gaske ne cewa Allah yana amfani da bala’o’i don ya yi wa mutane horo? Bala’in da suka auku kwanan baya horo ne daga Allah?

Domin su ɗora wa Allah laifi, wasu sun ambata labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki inda Allah ya yi amfani da abubuwan da ya halitta wajen halaka mutane. (Farawa 7:17-22; 18:20; 19:24, 25; Littafin Lissafi 16:31-35) Amma binciken da aka yi a kan waɗannan labaran na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a kowannensu, akwai muhimman abubuwa guda uku da suka bambanta su da waɗanda ke faruwa a yau. Na farko, an ba da gargaɗi kafin halakar ta auku. Na biyu, akasin bala’in da ke aukuwa a yau, waɗanda suke kashe mutanen kirki da miyagu, Allah yana zaɓan waɗanda yake halakawa. Mugayen da suka zama kangararru ko kuma waɗanda suka ƙi su saurari gargaɗi ne aka halaka. Na uku, Allah ya buɗe hanyar tsira ga mutane masu adalci.—Farawa 7:1, 23; 19:15-17; Littafin Lissafi 16:23-27.

Babu wata shaidar da ta nuna cewa Allah ne ya jawo bala’o’i masu yawan gaske da suka halaka miliyoyin mutane a yau. To, mene ne ya jawo bala’in da ke ƙaruwa? Ta yaya za mu iya jurewa da su? Da akwai lokaci ne da bala’o’i ba za su ƙara aukuwa ba? Za ka samu amsoshin a talifofin da ke gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba