Ana Gane Masu Bauta Ta Gaskiya Ta Haɗin Kansu
“Zan harhaɗa su kamar tumakin Bozrah.”—MI. 2:12.
1. Ta yaya halitta ta nuna tabbaci na hikimar Allah?
WANI marubucin zabura ya furta: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka: duniya cike ta ke da wadatarka.” (Zab. 104:24) Hikimar Allah a bayyane take a kan miliyoyin shuke-shuke, ƙwari, dabbobi, da ƙwayoyin halitta dabam-dabam masu ban al’ajabi na duniya da suka dangana da juna. A jikinka kuma akwai ƙwayoyin rayuwa dabam dabam masu yawa, daga manyan gaɓaɓuwa zuwa ƙwayar rai mitsitsiya, duk suna aiki tare don su sa ka zama cikakken mutum mai koshin lafiya.
2. Kamar yadda aka nuna a shafi na 13, me ya sa haɗin kai tsakanin Kiristoci ya zama kamar mu’ujiza?
2 Jehobah ya halicci ’yan Adam su dangana da juna. Mutane suna da sura, halaye, da iyawa dabam-dabam. Ƙari ga haka, ya ba ’yan Adam na farko irin halayensa da za su taimaka musu su haɗa kai da juna kuma su dangana da juna. (Far. 1:27; 2:18) Amma, ’yan Adam gabaki ɗaya yanzu suna bare daga Allah kuma ba su taɓa kasancewa da haɗin kai gabaki ɗayansu ba. (1 Yoh. 5:19) Saboda haka, sanin cewa ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko ta ƙunshi mutane dabam-dabam kamar bayin Afisa, sanannun matan Girka, Yahudawa maza masu ilimi, da masu bauta wa gunki a dā, haɗin kansu kamar mu’ujiza ce.—A. M. 13:1; 17:4; 1 Tas. 1:9; 1 Tim. 6:1.
3. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta haɗin kan Kiristoci, kuma menene za mu bincika a wannan nazarin?
3 Bauta ta gaskiya tana taimaka wa mutane su kasance da haɗin kai kamar gaɓaɓuwan jikinmu. (Karanta 1 Korantiyawa 12:12, 13.) Wasu fannoni da za mu bincika a wannan talifin su ne: Ta yaya bauta ta gaskiya take sa mutane su kasance da haɗin kai? Me ya sa Jehobah ne kaɗai zai iya haɗa kan mutane miliyoyi daga dukan al’ummai? Waɗanne tangarɗa ga haɗin kai ne Jehobah zai taimaka mana mu sha kansu? Kuma a batun haɗin kai, ta yaya Kiristanci na gaskiya ya bambanta da Kiristendom?
Yaya Bauta ta Gaskiya Take Sa Mutane Su Kasance da Haɗin Kai?
4. Ta yaya bauta ta gaskiya take sa mutane su kasance da haɗin kai?
4 Mutane da suke bauta ta gaskiya sun fahimci cewa domin Jehobah ne ya halicci dukan abubuwa, shi ne Mamallakin sararin samaniya. (R. Yoh. 4:11) Saboda haka, ko da yake Kiristoci na gaskiya suna zaune a yankuna dabam-dabam kuma a cikin yanayi dabam-dabam, duk suna biyayya ga dokokin Allah kuma suna rayuwar da ta jitu da waɗannan ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki. Dukan masu bauta ta gaskiya suna kiran Jehobah a matsayin ‘Uba.’ (Isha. 64:8; Mat. 6:9) Da haka, dukansu ’yan’uwa na ruhaniya ne kuma suna iya more haɗin kai mai kyau da mai zabura ya kwatanta: “Duba, me ya fi wannan kyau da kuwa daɗi ’yan’uwa su yi zaman jiyayya!”—Zab. 133:1.
5. Wane hali ne yake sa masu bauta ta gaskiya su kasance da haɗin kai?
5 Ko da yake Kiristoci na gaskiya ajizai ne, suna yin bauta tare cikin haɗin kai domin sun koyi su ƙaunaci juna. Jehobah ya koya masu yadda za su iya nuna ƙauna fiye da kowa. (Karanta 1 Yohanna 4:7, 8.) Kalmarsa ta ce: “Ku yafa zuciya ta tausai, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kol. 3:12-14) Wannan kamiltaccen magami, wato, ƙauna, ita ce hali na musamman da ake sanin Kiristoci na gaskiya da shi. Daga abin da ka fuskanta, ba ka ga cewa wannan haɗin kai shi ne fannin da ke bambanta bauta ta gaskiya ba?—Yoh. 13:35.
6. Ta yaya begen Mulkin yake taimakon mu mu more haɗin kai?
6 Masu bauta ta gaskiya suna da haɗin kai domin sun dogara ga Mulkin Allah a matsayin begen da ’yan Adam suke da shi kaɗai. Sun sani cewa ba da daɗewa ba Mulkin Allah zai canja gwamnatin ’yan Adam kuma ya albarkaci ’yan Adam masu biyayya da tabbatacciyar salama na dindindin. (Isha. 11:4-9; Dan. 2:44) Ta yin hakan, Kiristoci suna yin biyayya da abin da Yesu ya faɗa game da mabiyansa: “Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yoh. 17:16) Kiristoci na gaskiya ba sa saka hannu a yaƙe-yaƙen duniya; shi ya sa suke moran haɗin kai ko ma a lokacin da waɗanda suka kewaye su suke yin yaƙi.
Tushe Ɗaya Tak na Koyarwa ta Ruhaniya
7, 8. A wace hanya ce koyarwa ta Littafi Mai Tsarki take sa mu kasance da haɗin kai?
7 Kiristoci na ƙarni na farko sun more haɗin kai domin dukansu sun sami ƙarfafa daga tushe guda. Sun fahimci cewa Yesu yana koyarwa da kuma yi wa ikilisiyar ja-gora ta wurin hukumar mulki, da ta ƙunshi manzanni da dattawa a cikin Urushalima. Waɗannan maza masu ibada sun tsai da shawarwarinsu bisa Kalmar Allah kuma sun sa masu kula masu ziyara su sanar da umurnansu ga ikilisiyoyi a ƙasashe masu yawa. Game da wasu cikin irin waɗannan masu kula, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Suna cikin tafiyassu, suna bibbiyan birane, sai suka yi ta baba su hukunce-hukunce, waɗanda manzanni da dattiɓai da ke cikin Urushalima suka hukunta, domin su kiyaye su.”—A. M. 15:6, 19-22; 16:4.
8 A yau ma, Hukumar Mulki da ta ƙunshi Kiristoci shafaffu tana sa ikilisiyar dukan duniya ta kasance da haɗin kai. Hukumar Mulki tana wallafa littattafai masu ƙarfafa ruhaniya a harsuna masu yawa. An ɗauko wannan abinci na ruhaniya daga cikin Kalmar Allah. Da haka, abin da ake koyarwa ba daga mutane ba ne amma daga wurin Jehobah.—Isha. 54:13.
9. Ta yaya aikin da Allah ya ba mu yake taimaka mana mu kasance da haɗin kai?
9 Dattawa suna sa a kasance da haɗin kai ta wajen yin ja-gora a aikin wa’azi. Dangantaka na kud da kud da ke tsakanin waɗanda suke aiki tare a hidimar Allah ta fi dangantaka na mutane a duniya da kawai suke cuɗanya tare. An kafa ikilisiyar Kirista ba don ta zama wurin cuɗanya kawai ba, amma wurin ɗaukaka Jehobah da kuma cika wani aiki, wato, aikin wa’azin bishara, almajirantarwa, da kuma ƙarfafa ikilisiya. (Rom. 1:11, 12; 1 Tas. 5:11; Ibran. 10:24, 25) Hakan ya sa manzo Bulus ya ce game da Kiristoci: “Kuna tsayawa da ƙarfi cikin ruhu ɗaya, kuna yaƙi gaba ɗaya domin imanin bishara.”—Filib. 1:27.
10. A waɗanne hanyoyi ne muke da haɗin kai a matsayin mutanen Allah?
10 Saboda haka, a matsayin mutanen Jehobah muna da haɗin kai domin mun amince da ikon mallakar Jehobah, muna ƙaunar ’yan’uwanmu, mun sa begenmu a Mulkin Allah, kuma muna daraja waɗanda Allah yake amfani da su ya yi ja-gora a tsakaninmu. Jehobah yana taimaka mana mu bar wasu halayen da saboda ajizancinmu za su iya hana mu mu kasance da haɗin kai.—Rom. 12:2.
Yadda Za Mu Daina Fahariya da Kishi
11. Me ya sa fahariya ke kawo jayayya, kuma yaya Jehobah ya taimaka mana mu sha kanta?
11 Fahariya tana raba mutane. Mai fahariya yana so ya fifita kansa fiye da wasu kuma yana jin daɗin ɗaga kai. Amma sau da yawa hakan yana jawo rashin haɗin kai; waɗanda suka ji bugun kirjin da yake yi suna iya yin kishi. Almajiri Yakubu ya gaya mana kai tsaye: “Irin fahariyan nan duka mugu ne.” (Yaƙ. 4:16) Ba shi da kyau a riƙa nuna wa mutane an fi su. Jehobah misali ne mai kyau na tawali’u domin yana sha’ani da mutane ajizai kamar mu. Dauda ya rubuta: “[Tawali’un Allahnka] kuma ta maishe ni mai-girma.” (2 Sam. 22:36) Kalmar Allah tana taimaka mana mu kawar da fahariya ta wajen koya mana mu yi tunani da kyau. An hure Bulus ya yi tambaya: “Wanene ya bambance ka? me ke gare ka da ba ka karɓa kuwa? idan fa karɓa ne ka yi, don me ka ke fahariya, sai ka ce ba karɓa ka yi ba?”—1 Kor. 4:7.
12, 13. (a) Me ya sa yake da sauƙi mu yi kishi? (b) Waɗanne sakamako ake samu ta wajen ɗaukan wasu yadda Jehobah yake ɗaukansu?
12 Kishi wani abu ne kuma da ke kawo rashin haɗin kai. Domin ajizancin da muka gada, dukanmu muna da halin yin “kishi,” har Kiristoci da suka daɗe a cikin gaskiya a wani lokaci suna yin kishin yanayi, dukiya, gata, ko kuma iyawar wasu. (Yaƙ. 4:5) Alal misali, ɗan’uwa mai iyali yana iya yin kishin gatan da mai hidima na cikakken lokaci yake morewa, ba tare da fahimtar cewa mai hidima na cikakken lokaci yana iya ɗan kishin mutum mai yara. Ta yaya za mu hana irin wannan kishin ya ɓata haɗin kanmu?
13 Domin a taimaka mana mu guji yin kishi, ku tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ’yan’uwa shafaffu na ikilisiyar Kirista da gaɓaɓuwan jiki. (Karanta 1 Korintiyawa 12:14-18.) Alal misali, ko da yake ana ganin idanunka fiye da zuciyarka, amma ba dukansu ba ne suke da amfani a gare ka ba? Hakazalika, ko da yake wasu suna iya kasancewa sanannu fiye da wasu, Jehobah yana mutunta dukan waɗanda suke cikin ikilisiya. Saboda haka, bari mu ɗauki ’yan’uwanmu kamar yadda Jehobah yake ɗaukansu. Maimakon mu yi kishin wasu, muna iya nuna muna kula da su kuma muna ƙaunarsu. Ta yin hakan, muna nuna bambancin da ke tsakanin Kiristoci na gaskiya da waɗanda ke cocin Kiristendom.
Kiristendom Tana Cike da Rarrabuwa
14, 15. Ta yaya Kiristoci ’yan ridda suka kasance da rashin haɗin kai?
14 Haɗin kan Kiristoci na gaskiya ya bambanta da jayayyar da ke cocin Kiristendom. A ƙarni na huɗu, Kiristoci ’yan ridda sun yaɗu sosai da har sarki arne na Roma ya soma ja-gorarsu, hakan ya daɗa ga yaɗuwar Kiristendom. Saboda rarrabuwa da yawa da aka samu, masarauta da yawa sun rabu daga Roma kuma suka kafa coci na Jiharsu.
15 Masarautun nan da yawa sun yi ƙarnuka da yawa suna yaƙar juna. A ƙarnuka na 17 da 18, mutanen da ke Britaniya, Faransa, da kuma Amirka sun ɗaukaka kasancewa da aminci ga Jiharsu, saboda haka, kishin ƙasa ya zama kamar addini. A ƙarnuka na 19 da 20, kishin ƙasa ya soma rinjayar tunanin yawancin mutane. Daga baya, cocin Kiristendom suka rarrabu zuwa ɗarikoki masu yawa, kuma yawancinsu sun amince da kishin ƙasa. Masu zuwan coci sun yi yaƙi da ’yan’uwansu masu bi da ke wata ƙasa. A yau, Kiristendom ta rabu ta hanyar imanin ɗarikoki da kishin ƙasa.
16. Waɗanne irin batutuwa ne suka jawo rashin haɗin kai ga addinan Kiristendom?
16 A ƙarni na 20, wasu ɗarurruwan ɗariku na Kiristendom sun kafa ƙungiya don su ɗaukaka kasancewa da haɗin kai. Amma bayan shekaru da yawa na ƙoƙarce-ƙoƙarcensu, coci kaɗan ne kawai suka haɗa kai, kuma masu zuwa coci har ila sun rabu game da tambayoyi kamar su ra’ayin bayyanau, zubar da ciki, luwaɗi, da kuma naɗa mata limamai. A wasu ɓangarorin Kiristendom, shugabannin addini sun yi ƙoƙarin su sa mutane daga ɗariku dabam-dabam su kasance da haɗin kai ta wajen rage muhimmancin koyarwa da a dā ya jawo rarrabuwa. Duk da haka, rage muhimmancin koyarwar ta hana mutanen kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi kuma hakan bai kawo haɗin kai ga addinan Kiristendom da suka rabu ba.
Bauta ta Gaskiya Ta fi Kishin Ƙasa
17. Ta yaya aka annabta cewa bauta ta gaskiya za ta kawo haɗin kai a “kwanaki na ƙarshe”?
17 Ko da yake ’yan Adam sun rabu yanzu sosai fiye da dā, haɗin kai ya ci gaba da sa masu bauta ta gaskiya su kasance dabam. Annabin Allah Mikah ya annabta: “Zan harhaɗa su kamar tumakin Bozrah.” (Mi. 2:12) Mikah ya annabta cewa za a ɗaukaka bauta ta gaskiya fiye da dukan sauran fasalolin bauta, na allolin ƙarya ko kuma na bauta wa Jihar a matsayin alla. Ya rubuta: “Amma a cikin kwanaki na ƙarshe dutsen gidan Ubangiji za ya kafu a bisa ƙwankolin duwatsu, za ya ɗaukaka kuma bisa tuddai; al’ummai za su rugungunto zuwa gareshi. Gama dukan kabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu.”—Mi. 4:1, 5.
18. Bauta ta gaskiya ta taimake mu yin waɗanne canje-canje?
18 Mikah ya kuma kwatanta yadda bauta ta gaskiya za ta kawo haɗin kai ga magabta na dā. “[Mutane daga] al’ummai da yawa za su hau, su ce, Ku zo mu hau zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub; za ya koya mana tafarkunsa, za mu yi tafiya kuma cikin hanyoyinsa; . . . Har su buga takubansu su zama garmuna, masunsu kuma su zama lauzuna; al’umma ba za ta zare wa al’umma takobi ba, ba kuwa za su ƙara koya yaƙi ba.” (Mik. 4:3) Waɗanda suka daina bauta wa allolin da ’yan Adam suka yi ko kuma na ƙasashe domin su rungumi bauta wa Jehobah, suna more haɗin kai a dukan duniya. Allah yana koya musu hanyoyin ƙauna.
19. Haɗin kan miliyoyin mutane a bauta ta gaskiya tabbaci ne na menene?
19 Haɗin kai na Kiristoci na gaskiya a duniya yau ya fita dabam kuma tabbaci ne cewa Jehobah ya ci gaba da yi wa mutanensa ja-gora ta wurin ruhu mai tsarki. Mutane ɗaɗɗaya daga dukan ƙabilu suna kasancewa da haɗin kai fiye da dā a tarihin ’yan Adam. Wannan cikawa ne na musamman na abin da aka faɗa a Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, kuma ta nuna cewa mala’ikun Allah ba da daɗewa ba za su saki “iskoki” da za su halaka wannan mugun zamanin. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:1-4, 9, 10, 14.) Ba gata ba ne mu kasance da haɗin kai a ’yan’uwanci na dukan duniya ba? Ta yaya kowannenmu zai saka hannu wajen sa a kasance da haɗin kai? Za a tattauna wannan a talifi na gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya bauta ta gaskiya take sa mutane su kasance da haɗin kai?
• Yaya za mu hana kishi ya ɓata haɗin kanmu?
• Me ya sa kishin ƙasa bai raba masu bauta ta gaskiya ba?
[Hoton da ke shafi na 13]
Kiristoci na ƙarni na farko sun fito daga wurare dabam dabam
[Hotuna da ke shafi na 15]
Ta yaya taimakawa wajen gina Majami’ar Mulki take kawo haɗin kai?