Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/15 p. 12
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • “Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kwatancin Alkama da Zawan
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • “Yanzu, Ku “Jama’ar Allah Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/15 p. 12

Ka Tuna?

Ka yi farin cikin karanta fitowar Hasumiyar Tsaro na kwanan nan? Ka ga ko za ka iya amsa waɗannan tambayoyin:

• Me ya sa Almasihu ya mutu?

Ga dalilai guda biyu: Mutuwar Yesu ta tabbatar da cewa kamiltaccen mutum zai iya kasancewa da ibada duk da gwaji mafi tsanani. Kuma ya biya hukuncin zunubi da ’ya’yan Adamu suka gāda, kuma hakan ya buɗe hanyar samun rai madawwami.—12/15, shafuffuka na 22-23.

• Menene sadarwa mai ma’ana ya ƙunsa?

Fiye da tattaunawa kawai da su, ta ƙunshi yin tambayoyi da kuma saurara wa amsoshinsu da haƙuri. Iyalai da yawa sun gane cewa lokacin cin abinci yana ba da zarafi mai kyau na tattaunawa da kyau.—1/15, shafuffuka na 18-19.

• A wane yanayi ne za a yi tunanin sake yin baftisma?

Za a yi hakan idan a lokacin baftisma, yana zama a yanayi ko kuma yana yin wani abu a ɓoye da zai iya sa a yi masa yankan zumunci idan da ya riga ya yi baftisma.—2/15, shafi na 22.

• A cikin almarar Yesu na alkama da zawan, menene shuka iri mai kyau yake wakilta?

Ɗan mutum, Yesu, ya shirya filin ne a lokacin hidimarsa a duniya. Tun daga Fentikos na shekara ta 33 A.Z., an shuka iri mai kyau ne sa’ad da aka shafa Kiristoci a matsayin ’ya’yan Allah, ’ya’yan Mulki.—3/15, shafi na 20.

• Ta yaya ne ake kai alkama ta alama zuwa cikin rumbun Jehobah? (Mat. 13:30)

Cikawar ta ɗauki lokaci mai tsawo a ƙarshen wannan tsarin abubuwan. Shafaffun ’ya’yan Mulkin, alkama ta alama, ana kai su ne zuwa cikin rumbun Jehobah sa’ad da aka shigar da su cikin ikilisiyar Kirista da aka mai ko kuma sa’ad da suka samu ladarsu ta samaniya.—3/15, shafi na 22.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba