Ka Zama Mabiyin Kristi Na Gaske
“Kowane itacen kirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki; amma mumunan itace ya kan fitarda munanan ’ya’ya.”—MAT. 7:17.
1, 2. Yaya mabiyan Kristi na gaskiya suka bambanta da na ƙarya, musamman a waɗannan kwanaki na ƙarshe?
YESU ya ce za a san bambancin da ke tsakanin Kiristoci na ƙarya da Kiristoci na gaskiya ta ’ya’yansu, wato, ta koyarwarsu da halayensu. (Mat. 7:15-17, 20) Hakika, abin da mutane suke sakawa a zukatansu yana shafansu. (Mat. 15:18, 19) Waɗanda ake koya wa ƙaryace-ƙaryace suna ba da “munanan ’ya’ya,” amma waɗanda ake koya musu gaskiya ta ruhaniya suna ba da “’ya’yan kirki.”
2 Irin waɗannan ’ya’yan biyu sun bayyana sarai a wannan kwanaki na ƙarshe. (Karanta Daniel 12:3, 10.) Kiristoci na ƙarya suna da ra’ayin da bai dace ba game da Allah kuma sau da yawa suna yin ibada na riya, amma waɗanda suke da fahimi na ruhaniya suna bauta wa Allah “cikin ruhu da cikin gaskiya.” (Yoh. 4:24; 2 Tim. 3:1-5) Suna ƙoƙarin su nuna halaye irin na Kristi. Kowannenmu kuma fa? Yayin da kake bincika alamu biyar na gaba da ke nuna Kiristanci na gaskiya, ka tambayi kanka: ‘Halina da koyarwata sun jitu da Kalmar Allah kuwa? Ina sa gaskiya ta ƙara yin kyau a gaban waɗanda suke nemanta?’
Ka Yi Rayuwa da Ta Jitu da Kalmar Allah
3. Menene ke faranta wa Jehobah rai, kuma menene wannan ya ƙunsa ga Kiristoci na gaskiya?
3 Yesu ya ce: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama.” (Mat. 7:21) Hakika, ba da’awar bin Kiristanci ba ce take faranta wa Jehobah rai amma yin abin da ya kamata Kirista ya yi. Ga mabiyan Kristi na gaskiya, hakan ya ƙunshi duk tafarkin rayuwarsu, har da halinsu game da kuɗi, aikinsu, nishaɗi, al’adu na duniya da bukukuwa, da aure da sauran dangantaka da ’yan Adam. Amma, Kiristoci na ƙarya, suna bin tunani da hanyoyin duniya, da ba sa bisa ibada na gaskiya a waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Zab. 92:7.
4, 5. Ta yaya za mu yi amfani da kalmomin Jehobah da ke Malakai 3:18 a rayuwarmu?
4 Saboda haka, annabi Malakai ya rubuta: “Sa’annan za ku komo, ku rarrabe tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Mal. 3:18.) Yayin da kake tunani a kan waɗannan kalmomin, ka tambayi kanka: ‘Ina yin abubuwa ne kamar mutanen duniya, ko kuwa na fita dabam? Ina ƙoƙarin na dace da abokaina, wataƙila a makaranta ko kuma a wurin aiki, ko kuwa ina manne wa ƙa’idodin Litafi Mai Tsarki, kuma na yi magana a lokacin da ya dace?’ (Karanta 1 Bitrus 3:16.) Hakika, ba ma son mu zama masu adalcin kai, amma ya kamata mu fita dabam daga waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa.
5 Idan ka ga cewa kana bukatan yin canji, me ya sa ba za ka yi addu’a game da batun ba kuma ka nemi taimako na ruhaniya ta wajen nazarin Litafi Mai Tsarki a kai a kai, yin addu’a, da kuma halartan taro? Da zarar ka ci gaba da yin amfani da Kalmar Allah, za ka ƙara ba da “’ya’yan kirki,” haɗe da “ya’yan leɓunan da su ke shaida sunan [Allah].”—Ibran. 13:15.
Ka Yi Wa’azin Mulkin Allah
6, 7. A batun saƙon Mulki, wane bambanci ne ake gani tsakanin Kiristoci na gaskiya da na ƙarya?
6 Yesu ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk 4:43) Me ya sa Yesu ya sa Mulkin Allah ya zama ainihin jigon hidimarsa? Ya san cewa a matsayinsa na Sarkin wannan Mulkin, tare da ’yan’uwansa shafaffu da aka ta da daga matattu, za su kawar da tushen matsalolin ’yan Adam, wato, zunubi da Iblis. (Rom. 5:12; R. Yoh. 20:10) Shi ya sa ya ba mabiyansa umurni su yi shelar Mulkin har sai ƙarshen wannan zamanin. (Mat. 24:14) Mutanen da suke da’awar cewa su mabiyan Kristi ne ba sa yin wannan aikin, kuma gaskiyar ita ce, ba za su iya yinsa ba. Me ya sa? Aƙalla domin dalilai uku: Na farko, ba za su iya yin wa’azin abin da ba su fahimta ba. Na biyu, yawancinsu ba su da tawali’u da gaba gaɗi da ake bukata don a fuskanci ba’a da hamayya da gaya wa maƙwabtansu saƙon Mulki yake jawowa. (Mat. 24:9; 1 Bit. 2:23) Na uku, Kiristoci na ƙarya ba su da ruhun Allah.—Yoh. 14:16, 17.
7 A wani ɓangare kuma, mabiyan Kristi na gaskiya sun fahimci ko menene Mulkin Allah da kuma abin da zai cim ma. Bugu da ƙari, suna sa al’amuran wannan Mulkin farko a rayuwarsu, suna shelarsa a dukan duniya, da taimakon ruhun Jehobah. (Zech. 4:6) Kana sa hannu a wannan aikin a kai a kai kuwa? Kana ƙoƙarin ka kyautata iyawarka a matsayin mai shelar Mulki, wataƙila ta wajen ƙara ba da lokaci a hidima ko kuma ka ƙware a yinsa? Wasu sun yi ƙoƙarin su kyautata hidimarsu ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kyau. “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa,” in ji manzo Bulus wanda halinsa ne ya tattauna da mutane daga Nassosi.—Ibran. 4:12; A. M. 17:2, 3.
8, 9. (a) Waɗanne labarai ne suka nuna amfanin yin amfani da Littafi Mai Tsarki a hidimarmu? (b) Ta yaya za mu ƙara ƙwarewa wajen yin amfani da Kalmar Allah?
8 Sa’ad da yake hidimar ƙofa-ƙofa, wani ɗan’uwa ya karanta wa wani mutum mai bin addinin Katolika Daniel 2:44 kuma ya bayyana masa yadda Mulkin Allah zai kawo salama ta gaskiya da kwanciyar rai. Mutumin ya ce: “Na yi farin ciki da ka buɗe Littafi Mai Tsarki kuma ka nuna mini abin da nassi ya ce maimakon kawai ka gaya mini da kai.” Sa’ad da wani ɗan’uwa ya karanta wani nassi ga wata mata mai zuwa cocin Orthodox na Helenanci, ta yi tambayoyi da yawa masu kyau. A nan ma, ɗan’uwan tare da matarsa, sun ba da amsa daga Littafi Mai Tsarki. Daga baya matar ta ce: “Kun san abin da ya sa na yi magana da ku? Kun zo gidana da Littafi Mai Tsarki, kuma kun karanta daga ciki.”
9 Hakika, littattafanmu suna da muhimmanci kuma ya kamata mu ba da su a hidima. Amma, Littafi Mai Tsarki ne kayan aikinmu na musamman. Saboda haka, idan ba ka yawan yin amfani da shi a kai a kai a hidimarka ba, me zai hana ka kafa makasudin yin hakan? Kana iya zaɓan wasu ayoyi na musamman da suka bayyana Mulkin Allah da kuma yadda zai magance matsalolin da ke damun mutane a yankinku. Sai ka kasance a shirye ka karanta su sa’ad da kake wa’azi na ƙofa-ƙofa.
Ka Yi Amfani da Sunan Allah da Alfahari
10, 11. Game da yin amfani da sunan Allah, wane bambanci ne ke tsakanin Yesu da mutane da yawa da suke da’awar suna binsa?
10 “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, ni ne Allah kuwa.” (Isha. 43:12) Yesu Kristi, fitaccen Mashaidin Jehobah, ya ɗauki kasancewa mai ɗauke da sunan Allah da kuma sanar da shi a matsayin daraja. (Karanta Fitowa 3:15; Yohanna 17:6; Ibraniyawa 2:12.) Hakika, domin Yesu ya yi shelar sunan Ubansa, an kira shi “Mashaidi Mai-aminci.”—R. Yoh. 1:5; Mat. 6:9.
11 Akasin haka, mutane da yawa da suke da’awar cewa suna wakiltan Allah da Ɗansa sun nuna hali mai ban kunya game da hurarren sunan, har da cire shi daga nasu Littafi Mai Tsarki. Ta wurin nuna irin wannan ra’ayin, wani umurni da aka ba limaman Katolika a kwanan nan ya ce “kada a yi amfani ko kuma a furta sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu, wato, YHWH” a lokacin bauta.a Wannan mugun tunani ne!
12. Ta yaya aka ƙara sanin cewa bayin Jehobah suna tarayya na kud da kud da Jehobah a shekara ta 1931?
12 Ta wajen yin koyi da Kristi da “taron shaidu mai-girma” da suka wanzu a duniya kafin shi, Kiristoci na gaskiya suna yin amfani da sunan Allah da alfahari. (Ibran. 12:1) A shekara ta 1931, an ƙara sanin cewa bayin Allah suna tarayya na kud da kud da Jehobah sa’ad da suka amince da sunan nan Shaidun Jehobah. (Karanta Ishaya 43:10-12.) Ta haka, a azanci na musamman, mabiyan Kristi na gaskiya suka zama mutane “waɗanda an kira sunan [Allah] a bisansu.”—A. M. 15:14, 17.
13. Ta yaya za mu yi rayuwar da ta jitu da sunan da Allah ya ba mu?
13 Ta yaya za mu yi rayuwar da ta jitu da sunanmu da babu kamarta? Na farko, dole ne mu yi shaida ga Allah da aminci. Bulus ya rubuta: “Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira. Ƙaƙa fa za su kira bisa ga wanda ba su bada gaskiya gare shi ba? kuma ƙaƙa za su bada gaskiya ga wanda ba su ji ba? ƙaƙa za su ji kuwa in ba mai-yin wa’azi ba? ƙaƙa za su yi wa’azi kuma, in ba a aike su ba?” (Rom. 10:13-15) Kuma ya kamata cikin dabara mu fallasa ƙaryace-ƙaryacen addinai da suke ɓata sunan Mahaliccinmu, kamar su koyarwar wutar jahannama, wadda ke nuna cewa Allah mai ƙauna yana da halayen zalunci na Iblis.—Irm. 7:31; 1 Yoh. 4:8; gwada Markus 9:17-27.
14. Sa’ad da suka koya game da sunan Allah, menene wasu suka yi?
14 Kana alfaharin kasancewa mai ɗauke da sunan Ubanka na samaniya? Kana taimaka wa mutane su san wannan suna mai tsarki? Wata mata a Faris, a ƙasar Faransa, ta ji cewa Shaidun Jehobah sun san sunan Allah, sai ta gaya wa wata Mashaidiya da ta sadu da ita ta nuna mata wannan sunan a nata Litafi Mai Tsarki. Sa’ad da ta karanta Zabura 83:18, abin ya shafe ta sosai. Sai ta fara nazarin Litafi Mai Tsarki kuma yanzu ita ’yar’uwa ce mai aminci da ke hidima a wata ƙasa. Wata mata ’yar Katolika da take da zama a ƙasar Ostereliya ta yi kukan farin ciki sa’ad da ta ga sunan Allah a lokaci na farko a cikin Litafi Mai Tsarki. Shekaru da yawa yanzu, tana hidimar majagaba na kullum. A kwanan nan, sa’ad da Shaidu a ƙasar Jamaica suka nuna wa wata mata sunan Allah a nata Litafi Mai Tsarki, ita ma ta yi hawaye na farin ciki. Saboda haka, ka yi alfaharin kasancewa mai ɗauke da sunan Allah, kuma ta yin koyi da Yesu, ka sanar da wannan sunan mai tamani ga kowa.
“Kada Ku Yi Ƙaunar Duniya”
15, 16. Yaya Kiristoci na gaskiya suke ɗaukan duniya, waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?
15 “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.” (1 Yoh. 2:15) Duniya da halinta na jiki suna hamayya da Jehobah da kuma ruhunsa mai tsarki. Shi ya sa mabiyan Kristi na gaskiya ba kawai suna ƙin kasancewa na duniya ba ne. Suna ƙin ta a zuciyarsu, kamar yadda almajiri Yaƙub ya rubuta, sun san cewa “abutar duniya magabtaka ce da Allah.”—Yaƙ. 4:4.
16 Yin biyayya ga kalaman Yaƙub zai iya zama ƙalubale a duniyar da ke gabatar da gwaji masu yawa. (2 Tim. 4:10) Saboda haka, Yesu ya yi addu’a a madadin mabiyansa: “Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yoh. 17:15, 16) Ka tambayi kanka: ‘Ina ƙoƙarin kada na kasance na duniya? Mutane sun san matsayina game da bukukuwa da al’adu da suka saɓa wa nassi da kuma waɗanda ba su da tushe daga arna amma suna nuna ruhun duniya kuwa?’—2 Kor. 6:17; 1 Bit. 4:3, 4.
17. Menene zai iya motsa mutane masu zuciyar kirki su bi Jehobah?
17 Babu shakka, duniya ba za ta so mu ba don matsayinmu da ke bisa Littafi Mai Tsarki, amma yana iya sa mutane masu zuciyar kirki su so sanin gaskiya. Hakika, sa’ad da irin waɗannan mutane suka lura cewa bangaskiyarmu tana bisa Nassosi kuma ta shafi hanyar rayuwarmu gaba ɗaya, suna iya aikatawa ta wajen gaya wa shafaffu cewa: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”—Zech. 8:23.
Ka Nuna Ƙauna ta Gaskiya ta Kirista
18. Menene nuna ƙauna ga Jehobah da maƙwabta ya ƙunsa?
18 Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka” kuma “ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Mat. 22:37, 39) Wannan ƙauna (a·gaʹpe a Helenanci) ƙauna ce da ke bisa abin da ke daidai kuma tana yin la’akari da hakkokin mutum, kuma tana aikatawa daidai bisa ƙa’idodi masu kyau da mizanan ɗabi’a. Amma sau da yawa ta ƙunshi motsin rai mai ƙarfi. Tana iya daɗaɗawa kuma ta kasance na gaske. (1 Bit. 1:22) Ba ta son kai, domin tana bayyana a kalamai da ayyuka na rashin son kai.—Karanta 1 Korantiyawa 13:4-7.)
19, 20. Ka ba da labarai da suka nuna ƙarfin ƙauna ta Kirista.
19 Domin ƙauna sashe ne na ruhu mai tsarki na Allah, tana taimaka wa Kiristoci na gaskiya su yi abin da wasu ba za su iya yi ba, kamar sha kan hani na ƙabilanci, al’adu, da siyasa. (Karanta Yohanna 13:34, 35; Gal. 5:22) Sa’ad da masu kama da tumaki suka ga irin wannan ƙaunar, hakan yana motsa su sosai. Alal misali, sa’ad da wani saurayi Bayahude a Isra’ila ya halarci taronsa na farko, ya yi mamakin ganin yadda ’yan’uwa Yahudawa da Larabawa suke bauta wa Jehobah tare. Saboda haka, ya soma halartan taro a kai a kai kuma ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Kana nuna irin wannan ƙauna ga ’yan’uwanka da zuciya ɗaya? Kana ƙoƙarin ka yi wa sababbi maraba sosai a Majami’ar Mulkinku, ko da daga wace ƙasa ce suka fito, launin fatarsu, ko kuma matsayinsu a gaban jama’a?
20 A matsayin Kiristoci na gaskiya, muna ƙoƙarin mu nuna ƙauna ga kowa. A ƙasar El Salvador, wata mai shela matashiya tana nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata ’yar Katolika mai shekara 87 wadda ta manne wa zuwa cocinta. Wata rana, matar ta soma ciwo sosai kuma aka kwantar da ita a asibiti. Sa’ad da ta koma gida, Shaidun suka ziyarce ta kuma suka kawo mata abinci. Sun ci gaba da yin hakan har wajen wata ɗaya. Babu wani da ya ziyarci matar daga cocinta. Menene sakamakon? Ta watsar da sifofinta, ta yi murabus daga cocinta, kuma ta sake soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Hakika, ƙauna ta Kirista tana da ƙarfi! Tana iya motsa zukata a hanyoyin da wataƙila kalamai ba za su iya ba.
21. Ta yaya za mu sa rayuwarmu ta nan gaba ta zama tabbatacciya?
21 Ba da daɗewa ba, Yesu zai gaya wa dukan waɗanda suke da’awar ƙarya cewa suna bauta masa: “Ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aika mugunta.” (Mat. 7:23) Saboda haka, bari mu nuna ’yar ruhu da ke ɗaukaka Uban da Ɗan. Yesu ya ce: “Kowanene fa mai-jin waɗannan zantattuka nawa, yana kuwa aikata su, za a kwatanta shi da mutum mai-hikima, wanda ya gina gidansa bisa pa.” (Mat. 7:24) Hakika, idan muka nuna cewa mu mabiyan gaskiya na Kristi ne, za mu samu amincewar Allah, kuma begenmu na nan gaba zai zama tabbatacce, kamar wanda aka kafa a kan dutse!
[Hasiya]
a Wasu littattafan Katolika na zamani na Turanci, har da The Jerusalem Bible, sun fassara baƙaƙe huɗu, YHWH zuwa “Yahweh.”
Ka Tuna?
• Ta yaya ake bambanta mabiyan Kristi na gaskiya daga na ƙarya?
• Ka ambata wasu “’ya’ya” da ke bayyana Kiristoci na gaskiya.
• Ta wajen nuna ’yar ruhu, waɗanne makasudai ne za ka iya kafawa?
[Hoton da ke shafi na 13]
Halinka ne ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki a kai a kai a hidimarka?
[Hoton da ke shafi na 15]
Mutane sun san matsayinka game da bukukuwa da suka saɓa wa nassi?