Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 15
  • Me Za Ka Yi Idan Ka Kadaita?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Za Ka Yi Idan Ka Kadaita?
  • Karin Batutuwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka kusaci Allah
  • Ka karanta Nassosin da za su karfafa ka
  • Ka bincika abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa
  • Ka guji yawan alhini ko damuwa
  • Ka nemi abokan kirki
  • Ka rika motsa jiki
  • Yadda Za A Ci Gaba Da Abuta A Duniya Marar Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Za Mu Ci-gaba da Ƙarfafa Dangantakarmu da ꞌYanꞌuwanmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Zabi Abokan Kirki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Karin Batutuwa
mrt talifi na 15
Wata mata a cikin gida tana kallon waje ta wundo.

Me Za Ka Yi Idan Ka Kadaita?

Kana ji kamar kana fama kai kadai ne ko ka kadaita? Idan haka ne, yanayinku daya ne da wani marubucin Zabura da ya ce: “Na zama kamar tsuntsu a saman daki, tsuntsun da yake shi kadai.” (Zabura 102:7) Shawarar da ke Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka maka ka magance matsalolin da ke tattare da kadaici.

  • Ka kusaci Allah

  • Ka karanta Nassosin da za su karfafa ka

  • Ka bincika abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa

  • Ka guji yawan alhini ko damuwa

  • Ka nemi abokan kirki

  • Ka rika motsa jiki

Ka kusaci Allah

Ko da ka kadaita, za ka iya yin farin ciki idan ka san cewa kana bukatar ka kulla dangantaka mai kyau da Allah kuma ka kokarta ka yi hakan. (Matiyu 5:​3, 6, New World Translation) Ga wasu abubuwa da za su taimaka maka ka yi hakan.

  • Gajerun bidiyoyi a kan muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki

  • “Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki”​—An ba da amsoshin tambayoyin da mutane suke yawan yi

  • “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu”​—Jerin talifofin nan za su taimaka maka ka ji dadin karanta labaran amintattun bayin Allah maza da mata da ke Littafi Mai Tsarki

  • “Halittarsa Aka Yi?”​—Jerin talifofin nan sun nuna yadda abubuwan da ke duniyar nan suke da kyau da kuma wuyar fahimta

Ka karanta Nassosin da za su karfafa ka

Nassosin nan sun karfafa mutane da yawa. Maimakon ka karanta Nassosi da yawa a tāke, ka karanta su kadan-kadan, sai ka yi tunani a kansu kuma ka yi addu’a.​—Markus 1:35.

  • Zabura 23:​1-6

  • Zabura 34:​1-22

  • Zabura 46:​1-11

  • Zabura 63:​6-8

  • Zabura 91:​1-6

  • Matiyu 6:​25-34

  • 2 Korintiyawa 1:​3, 4

  • Filibiyawa 4:​6, 7

  • 1 Bitrus 5:​6, 7

Ka bincika abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa

Idan kana fama da wata matsala, sanin abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa da kuma yadda Allah zai kawar da su zai taimake ka ka jimre.​—Ishaya 65:17.

  • Me ya sa Allah ya kyale mutane su sha wahala?

  • Me ya nuna cewa muna kwanaki na karshe?

  • Su wane ne mahaya hudu da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?

  • Mene ne Mulkin Allah zai yi?

Ka guji yawan alhini ko damuwa

Talifofin da ke kasa za su iya taimaka maka ka magance matsalolin da ke tattare da kadaici kuma su sa ka daina yawan ‘damuwa.’​—Matiyu 6:25.

  • Shin, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka daina alhini?

  • Yawan damuwa a kan kudi

Ka nemi abokan kirki

Zama da abokan kirki zai sa ka kasance da ra’ayi mai kyau kuma za ka yi murna. Hakan na da muhimmanci musamman idan ba zai yiwu ka kasance tare da su ba. Idan kana zama a gida kai kadai, za ka iya amfani da manhajar sadarwa da ake amfani da ita wajen kira ana ganin juna wato, videoconferencing, ko ka rika kiran abokanka ta waya kuma ka nemi sabbin abokai. Talifofi na gaba za su taimaka maka ka nemi abokan kirki kuma ka san yadda za ka zama abokin kirki.​—Karin Magana 17:17.

  • Wane ne abokin kirki? (Bidiyo)

  • Zai dace in yi abota da mutane dabam-dabam?

  • Me ya sa ba ni da abokai?

  • Albarkar da ake samu don bayarwa

Ka rika motsa jiki

Littafi Mai Tsarki ya ce, “wasa jiki tana da amfaninta.” (1 Timoti 4:​8, Tsohuwar Hausa a Saukake) Motsa jiki zai iya taimaka maka ka yi tunani da kyau kuma ka yi farin ciki musamman idan ka kadaita. Ko da ba za ka iya fita daga gida ba, akwai wasu abubuwa da za ka iya yi don ka rika motsa jiki.

  • Me zai taimaka min in rika motsa jiki?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba