Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 136
  • Maryamu Uwar Allah ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Maryamu Uwar Allah ce?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ƙage Na 5: Maryamu Mahaifiyar Allah ce
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 136
Maryamu da jariri Yesu

Maryamu Uwar Allah ce?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A’a, Littafi Mai Tsarki bai koyar cewa Maryamu uwar Allah ce ba. Ban da haka, bai ba Kiristoci umurnin su rika bauta da kuma daukaka Maryamu ba.a Ka yi la’akari da wannan:

  • Maryamu ba ta taba da’awa cewa ita uwar Allah ce ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa ta haifi “Dan Allah” ne, ba Allah ba​—Markus 1:1; Luka 1:32.

  • Yesu kristi bai taba cewa Maryamu uwar Allah ce ba ko kuma a ba ta daraja ta musamman. Ban da haka ma, ya yi wa wata mata gyara saboda ta mai da hankali ga gatan da maryamu ta samu na haifan sa, ya ce: “I, amma albarka tā fi tabbata ga wadanda ke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”​—Luka 11:27, 28.

  • Lakabin nan “Uwar Allah” da “Theotokos” (Wadda ta haifi Allah) ba sa cikin Littafi Mai Tsarki.

  • Furucin nan “Sarauniyar Sammai” da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ba ya nufin Maryamu, amma allahiyar karya ce da Isra’ilawan da suka yi ridda suke bautawa.(Irmiya 44: 15-​19) Watakila Sarauniyar Sammai” nan Ishtar (Astarte) ce wadda Babiloniyawa ke bautawa.

  • Kiristoci a karni na farko ba su bauta wa Maryamu ba, balle ma su ba ta wata daraja ta musamman. Wani masani ya ce Kiristoci a karni na farko “ba su amince da bautar gumaka ba kuma watakila sun guji nuna wa Maryamu daraja fiye da kima domin kada mutane su yi zargin su da bauta wa allahiya. ”​—In Quest of the Jewish Mary.

  • Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana wanzuwa. (Zabura 90:1, 2; Ishaya 40:28) Tun da yake ba shi da mafari, ba zai yiwu a ce yana da uwa ba. Ban da haka ma, Maryamu ba za ta iya daukar Allah a cikinta ba; Littafi Mai Tsarki ya bayana cewa sammai da kanta ta yi masa kadan.​—1 Sarakuna 8:​27.

Maryamu​—Uwar Yesu ba “Uwar Allah ba”

Maryamu Bayahudiya ce, kuma daga zuriyar Sarki Dauda ta fito. (Luka 3:​23-31) Ta sami tagomashi daga Allah saboda bangaskiya da kauna da take da shi. (Luka 1:​28) Allah ya zabe ta ta haifi Yesu. (Luka 1:​31, 35) Maryamu ta haifa wa mijinta Yusufu wasu ’ya’ya.​—Markus 6:3.

Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Maryamu ta zama almajirar Yesu, babu wani karin bayani da aka bayar game da ita.—A. M. 1:14.

Me ya sa wasu suka dauka cewa Maryamu uwar Allah ce?

An soma gano cewa mutane suna bauta wa Maryamu ne a karshen karnin na hudu. A wannan lokacin ne, cocin Katolika ta zama addini da kowa ke bi a daular Roma. A sakamakon haka, ne masu bautar gumaka da yawa suka zama Kiristoci.

Cocin ta kuma soma koyarwar allah-uku-cikin-daya da ba ta cikin Littafi Mai Tsarki.

Koyarwar Allah-uku-cikin-daya ya sa Kiristoci da yawa su dauka cewa idan Yesu Allah ne, to dole ne Maryamu ta zama uwar Allah. A shekara ta 431 bayan haihuwar Yesu, wani rukunin shugabannin coci a Afisa ya sanar cewa sun amince Maryamu “Uwar Allah” ce. Bayan wannan sanarwa, mutane sun soma bauta wa Maryamu da kuma daukaka ta fiye da yadda suke yi a dā. Kari ga haka, sa’ad da arna suka soma zuwa cocin, siffofi da gunkin Maryamu suka soma maye gurbi allahiyar haihuwa kamar su Artimas (wato Diana ga Romawa) da Isis.

A shekara ta 432 bayan haihuwar Yesu, Paparoma Sixtus na uku ya ba da umurni a gina coci a Roma domin daukaka Uwar Allah. An gina cocin ne kusa da wurin da a dā aka gina haikali don daukaka Lucina, wato allahiyar haihuwa ta Roma. Wani marubuci ya yi magana game da cocin ya ce: “Bayan da Romawa suka zama Kiristoci wannan cocin ya zama alama ta musamman da ke nuna yadda bautar Maryamu ya maye gurbin allahiyar haihuwa da arna ke bauta wa kafin su zama Kiristoci.”​—Mary​—The Complete Resource.

a Yawancin darikun Kiristoci suna koyar da cewa Maryamu uwar Allah ce. Suna kiran ta da lakabi kamar “sarauniyar sammai” ko kuma Theotokos, wato kalmar Hellenanci da ke nufin “Uwar Allah.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba