Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 137
  • Mene ne Yake Nufi Mutum ya Zama Mai Tsarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Yake Nufi Mutum ya Zama Mai Tsarki?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Shin mutum ajizi zai iya zama mai-tsarki?
  • Shin za a iya kasancewa da rashin tsarki a gaban Allah?
  • Ra’ayin da bai dace ba game da zama mai-tsarki
  • “Ku Zama da Tsarki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Kana Daraja Abubuwa Masu Tsarki Kamar Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Ni Ubangiji Allahnku Mai-Tsarki Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne” Jehobah
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 137
Musa da kurmi mai ci da wuta

Mene ne Yake Nufi Mutum ya Zama Mai Tsarki?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Mutum ya zama mai tsarki yana nufin ba zai sa hannu a duk wani abin da zai kazantar da shi ba. An dauko kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “tsarki” daga furucin da ke nufin “ware” wani abu.Saboda haka, abu mai tsarki abu ne da aka ware ko kuma kebe, musamman ma don yana da tamani da kuma tsabta.

Allah ne ya fi tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji.”a (1 Sama’ila 2:2) Saboda haka, Allah ne ke da izinin kafa mizani na abu mai-tsarki.

Za a iya yin amfani da kalmar nan “tsarki” a duk abin da ya shafi Allah, musamman ma abubuwan da aka kebe su domin sujada. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da:

  • Wurare masu tsarki: Allah ya yi magana da Musa a kusa da kurmin da ke ci da wuta ya ce: “Wurin da kake tsayawa wuri mai-tsarki ne.”​​—Fitowa 3:​2-5.

  • Taro masu tsarki: Isra’ilawa na dā sun yi taro don bauta wa Allah kuma suka kira hakan taro “masu tsarki.”​​—Levitikus 23:37.

  • Kayayyaki masu tsarki: Ana kiran kayayyakin da aka yi amfani da su domin sujada ga Allah a Urushalima “kayayyaki masu tsarki.” (1 Sarakuna 8:4) An bukaci a rika daraja wadannan kayayyaki masu tsarki, ko da yake ba za a yi masu sujada ba.b

Shin mutum ajizi zai iya zama mai-tsarki?

E. Allah ya umurci Kiristoci: “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.” (1 Bitrus 1:​16) Hakika, mutane ajizai ba za su iya zama kamiltattu kamar yadda Allah yake ba. Duk da haka, ana daukan mutanen da suka kiyaye dokokin Allah “tsattsarka, abar karɓa ga Allah.” (Romawa 12:1) Duk wanda yake kokarin ya zama mai-tsarki yana nunawa a furucinsa da ayyukansa. Alal misali mutumin yana bin shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce “ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,” da kuma “ku ma kanku sai ku zama tsarkaka cikin dukan al’amuranku.”​​—1 Tasalonikawa 4:3; 1 Bitrus1:​15.

Shin za a iya kasancewa da rashin tsarki a gaban Allah?

E. Duk wanda ya ki bin mizanan Allah, mutumin ba zai kasance da tsarki a gaban Allah ba. Alal misali Littafin Ibraniyawa ya yi magana game da “’yan’uwa tsarkaka,” kari ga haka ya yi masu kashedi cewa “kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.” ​​—Ibraniyawa 3:​1, 12.

Ra’ayin da bai dace ba game da zama mai-tsarki

Ra’ayi: Mutum yana iya zama mai tsarki ta wurin hana zuciyarsa abin da take bukata.

Gaskiyar: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “wahalar da jiki” ko kuwa hana zuciya abin da take bukata, “ba ta da amfani” a wurin Allah. (Kolosiyawa 2:​23) A maimakon haka, Allah na son mu ji dadin abubuwa masu kyau. “Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.”​​—Mai-Wa’azi 3:13.

Ra’ayi: Kin yin aure zai sa mutum ya kara zama mai-tsarki

Gaskiyar: Kirista ne zai yanke wa kansa shawarar yin aure ko a’a, ko mutum ya yi aure ko bai yi ba, hakan ba hanya ce na kasancewa da tsarki a gaban Allah ba. Gaskiya ne cewa wadanda suka zabi su zauna babu aure za su iya ba da hankulansu ga aikin ibada sosai. (1 Korintiyawa 7:​32-​34) Ban da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa masu aure ma za su iya kasancewa da tsarki. Daya daga cikin manzannin Yesu wato Bitrus na da aure.​​—Matta 8:​14; 1 Korintiyawa 9:5.

Daga ina ne furucin nan “Littafi Mai Tsarki” ya fito?

A cikin darrurukan shekaru, duka rubuce-rubucen hurarriyar Kalmar Allah ana ce da shi “Littafi Mai Tsarki” domin wadannan dalilai:

  • Tushensa. “Sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki ke izawa, Allah na magana ta bakinsu.”​—2 Bitrus 1:​21.

  • Sakonsa.“Ƙa’idodin Yahweh daidai suke, suna farantar da zuciya. Umarnan Yahweh masu sauƙin ganewa ne, sukan fahimtar da zuciya.”​—Zabura 19:​8, 9.

Don haka, za a iya ce Kalmar Allah Littafi ne mai-tsarki. Domin an ware shi daga wasu littattafai saboda sakon da ke ciki da kuma yadda ake amfani da shi a ibada.

a Jehobah ne sunan Allah. Ayoyin Littafi Mai Tsarki da yawa sun nuna cewa wannan suna tana da “tsarki” ko kuma “tsarkakewa”

b Littafi Mai Tsarki ya hana yi wa kayayyakin addini sujada.​—1 Korintiyawa 10:14.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba