7-13 GA SATUMBA, 2026
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
Abubuwan da Za Mu Iya Koya Daga Mutanen Gibiyon
“Mazaunan Gibeyon suka yi yarjejeniyar zaman salama da Israꞌilawa suna kuma zaune a cikinsu.”—YOSH. 10:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga darussan da za mu iya koya daga mutanen Gibiyon da kuma yadda Jehobah ya bi da su.
1-2. Me ya sa zai dace mu yi bincike a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da mutanen Gibiyon?
SHEKARU 40 bayan Israꞌilawa suka bar ƙasar Masar kuma suka shiga Ƙasar Alkawari. Jehobah ya taimaka wa Israꞌilawa su ci ƙasar Jeriko da kuma Ai da yaƙi. Amma daga baya, wani abin da ba a yi zato ba ya faru. Wasu mutane sun zo sun sami Israꞌilawa, sun gaya musu cewa sun zo daga ƙasa mai nisa, kuma sun zo su yi yarjejeniyar zaman lafiya da su maimakon su yi faɗa da su.
2 Mutanen nan ꞌyan Gibiyon ne. Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mutanen Gibiyon, wannan ne karo na farko da Littafi Mai Tsarki ya ambata su. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutanen Gibiyon sun yi zama tare da Israꞌilawa na dogon lokaci. Akwai halaye masu kyau da mutanen Gibiyon suke da su da za mu iya koya. Abin da ya faru da su zai iya koya mana abubuwa game da Jehobah.
KA KASANCE DA BANGASKIYA DA KUMA SAUƘIN KAI
3. (a) Su waye ne Gibiyonawa? (b) Me ya sa suka roƙi Joshuwa ya yi zaman lafiya da su?
3 Saꞌad da Israꞌilawa suka soma cin ƙasar Kanꞌana da yaƙi, Gibiyonawa suna zama a Gibiyon, birni mai katanga. Suna cikin alꞌummar Hiwiyawa, wato ɗaya daga cikin alꞌummai bakwai na Kanꞌaniyawa da suka fi Israꞌilawa ƙarfi da kuma yawa. (M. Sha. 7:1) Don haka, sojojin Gibiyonawa na da ƙarfi sosai. (Yosh. 10:2) Sauran alꞌumman Kanꞌana suna so su yaƙi Israꞌilawa, amma Gibiyonawan ba su yi hakan ba, domin sun san cewa ba za su yi nasara a kan Israꞌilawa ba. Sun kuma san cewa Jehobah yana taimaka wa Israꞌilawa su yi nasara a yaƙe-yaƙen da suke yi. Ban da haka ma, su san cewa Jehobah ya yi wa Israꞌilawan alkawari cewa zai ba su ƙasar Kanꞌana. (Fit. 34:11; Yosh. 9:24) Don haka, bayan da Israꞌilawa suka yi nasara a kan ƙasar Jeriko da kuma Ai, sai mutanen Gibiyon suka tura mutanea wurin Joshuwa a Gilgal don su roƙe shi ya yi zaman lafiya da su.
4. (a) Bisa ga Yoshuwa 9:8-13, ta yaya mutanen Gibiyon suka yaudari Israꞌilawa su yi yarjejeniyar zaman lafiya da su? (Ka kuma duba hoton.) (b) Me ya faru bayan da Israꞌilawa suka gano cewa mutanen Gibiyon sun yaudare su?
4 Karanta Yoshuwa 9:8-13. Gibiyonawan sun yi wa Joshuwa ƙarya cewa sun zo ne daga ƙasa mai nisa. Sun gaya wa Joshuwa cewa sun ji yadda Jehobah ya taimaka wa Israꞌilawa su yi nasara a kan Masarawa, da Amoriyawa, da Sihon, da kuma Og. Gibiyonawan suna da hikima, don haka ba su ambata nasarar da Israꞌilawa suka yi kwana-kwanan nan a kan Jeriko da Ai ba. Da a ce sun faɗi hakan, da Joshuwa zai gane cewa ƙasarsu ba ta da nisa shi ya sa suka ji abin da ya faru kwanan nan. Joshuwa da mutanen Israꞌila sun yarda da abin da mutanen Gibiyon suka gaya musu, kuma suka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su ba tare da sun ji raꞌayin Jehobah ba. (Yosh. 9:14, 15) Jim kaɗan bayan hakan, sai Israꞌilawan suka gane cewa Gibiyonawan sun yaudare su. Amma ba su karya yarjejeniyar da suka yi da Gibiyonawan ba, domin sun ‘rantse da sunan Yahweh’ cewa za su yi hakan. (Yosh. 9:16-19) Sai Joshuwa ya sa Gibiyonawa su zama “masu saran itace da masu ɗiban ruwa domin jamaꞌa da kuma domin wurin da Yahweh ya zaɓa domin a yi masa sujada.”—Yosh. 9:27.
Gibiyonawa sun yaudari Joshua ya yi yarjejeniyar zaman lafiya da su (Ka duba sakin layi na 4)
5. A waɗanne hanyoyi ne Mutanen Gibiyon suka nuna bangaskiya ga Jehobah?
5 Da sarakuna biyar na Amoriyawa suka ji cewa Gibiyonawa sun yi yarjejeniyar zama lafiya da Israꞌila, sai suka haɗa kai don su kai wa Gibiyonawa hari. Gibiyonawan sun roƙi Joshuwa ya taimaka musu. (Yosh. 10:3-7) Sai Joshuwa da sojojin Israꞌila suka je su taimaka musu, kuma Jehobah ya goyi bayan Israꞌilawan. Jehobah ya ma hallakar da wasu maƙiyan da duwatsun ƙanƙara, ya kuma hana rana faɗuwa har sai da Israꞌilawan suka yi nasara. (Yosh. 10:9-14) Yadda mutanen Gibiyon suka yi yarjejeniyar zaman lafiya da Israꞌilawa da kuma yadda suka nemi taimakon su, ya nuna cewa suna da bangaskiya. Sun kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarinsa kuma zai kāre su.
6. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya bi da Gibiyonawa saꞌad da Israꞌilawa suke cin ƙasar alkawari da yaƙi?
6 Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah? Jehobah mai sauƙi ne da kuma jinƙai. Da ma Jehobah ya riga ya umurce su cewa su “kori dukan mazaunan ƙasar,” kuma hakan ya haɗa da Gibiyonawa. (L. Ƙid. 33:51, 52) Amma da Israꞌilawa suka yi alkawari cewa ba za su hallaka mutanen Gibiyon ba, Jehobah ya amince da hakan. Ya yi hakan duk da cewa Israꞌilawan ba su ji raꞌayinsa kafin su yi yarjejeniyar ba. Ƙari ga haka, ya taimaka wa Israꞌila su cika alkawarin da suka yi, ya kuma ceci Gibiyonawan ta hanyar muꞌujiza.—Yosh. 9:26; 11:19.
7. Ta yaya za mu kasance da bangaskiya da kuma sauƙin kai kamar mutanen Gibiyon? (Ka kuma duba hoton.)
7 Ta yaya za mu yi koyi da Gibiyonawa? Ta wajen kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah. Da yake mun san game da halayen Jehobah fiye da mutanen Gibiyon, muna da dalilai da yawa da za su sa mu dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu. (Zab. 40:4, 5) Za mu kuma iya yin koyi da mutanen Gibiyon, ta wajen yin ayyuka a ƙungiyar Jehobah da ba su da sauƙin yi, ko kuma ayyukan da mutane suna yawan renawa. (Yosh. 9:23, 27) Wani ɗanꞌuwa saurayi mai suna Luke ba zai taɓa manta da lokacin da ya ga wani ɗanꞌuwa da ya daɗe yana hidima a Bethel ya yi hakan ba. Duk da cewa ɗanꞌuwan yana da ayyuka masu muhimmanci da yake yi a Bethel, ya ba da kai don ya yi gādi a wata Majamiꞌar Mulkin da ake ginawa. Luke ya ce: “Na gane cewa, muna bukatar mu yi abin zai nuna cewa mu masu sauƙin kai ne, maimakon kawai mu yi tunanin cewa mu masu sauƙin kai ne.” Kamar Gibiyonawan za mu nuna cewa muna da bangaskiya idan muka dogara ga Jehobah a duk lokacin da muke fuskantar matsaloli, da kuma saꞌad da aka ba mu aiki a ƙungiyar Jehobah.
Ka yi koyi da Gibiyonawa ta wurin yin aikin da bai da sauƙi kuma ana yawan renawa (Ka duba sakin layi na 7)
IDAN AKA YI MAKA RASHIN ADALCI, KA BAR KOME A HANNUN JEHOBAH
8. Wane laifi ne Sarki Shawulu ya yi wa mutanen Gibiyon?
8 Littafi Mai Tsarki ya kuma gaya mana abin da ya faru da Gibiyonawa a lokacin da Sarki Shawulu yake mulkin Israꞌila. A lokacin, Shawulu ya yi ƙoƙarin kashe dukan Gibiyonawab saboda “kishin da yake da shi domin mutanen Israꞌila da na Yahuda.” (2 Sam. 21:2, 5, 6) Wannan abin da Shawulu ya yi mugunta ne da rashin adalci. Shawulu ya karya yarjejeniya da aka yi shekaru da yawa da suka shige tsakanin Israꞌilawa da Gibiyonawa.
9. A wane lokaci ne Jehobah ya ɗau mataki don rashin adalcin da aka yi wa Gibiyonawa?
9 Jehobah bai hukunta waɗanda suka yi wa Gibiyonawa rashin adalci nan da nan ba. Amma a lokacin da Dauda ya zama sarkin Israꞌila, Jehobah ya sa ba a yi ruwan sama a Israꞌila ba na tsawon shekara uku. Hakan ya sa aka yi tsananin yunwa a ƙasar Israꞌila. Sai Dauda ya tambayi Jehobah dalilin da ya sa hakan yake faruwa. Jehobah ya gaya masa cewa akwai alhakin jini a kan Shawulu da wasu ꞌyan gidansa domin muguntar da suka yi wa Gibiyonawa shekarun baya.—2 Sam. 21:1.
10. Bisa ga 2 Samaꞌila 21:3-6, ta yaya abin da Gibiyonawan suka gaya ma Dauda ya nuna cewa suna daraja dokar Allah?
10 Karanta 2 Samaꞌila 21:3-6. Dauda ya tambayi Gibiyonawan abin da suke so ya yi musu. Gibiyonawan ba su gaya wa Dauda ya ba su kuɗi mai yawa ba. Sun san Dokar Allah sosai. Dokar ta ce dole ne a kashe wanda ya yi kisa. Don haka, wanda ya yi kisan ba zai iya biyan kuɗi mai yawa don a bar shi ba. (L. Ƙid. 35:30, 31) Sun kuma fahimci cewa ba za su iya kashe mutum ba tare da izinin sarki ba. Don haka, Dauda ya ba su izinin kashe mazaje guda bakwai daga gidan Shawulu. Wataƙila mutanen sun sa hannun wajen kashe Gibiyonawa da yawa. Daga baya, sai aka soma ruwan sama kuma aka daina tsananin yunwar da ake yi ƙasar Israꞌila. Hakan ya nuna cewa Jehobah ya daina fushi da Israꞌilawan.—2 Sam. 21:9, 10, 14.
11. Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah?
11 Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah? Mun ga tabbaci cewa Jehobah Allah ne mai yin adalci. (Zab. 37:28) Mutane da yawa suna wulakanta waɗanda suka fito daga wata ƙasa ko kuma suka yi dabam da su. Amma Jehobah yana so a riƙa yi wa dukan mutane adalci. A daidai lokacin da ya dace, Jehobah zai ɗauki mataki a kan waɗanda suke yi wa bayinsa rashin adalci. Mun kuma koyi cewa Jehobah yana so mu riƙa cika alkawarin da muka yi, kamar yadda ya bukaci Israꞌilawa su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi da Gibiyonawa.—Ka kuma duba Amos 1:9.
12. Ta yaya za mu yi koyi da Gibiyonawa idan aka yi mana rashin adalci?
12 Ta yaya za mu yi koyi da Gibiyonawa? Ko da ꞌyanꞌuwanmu ne suka yi mana rashin adalci, zai dace mu yi haƙuri kuma mu bar kome a hannun Jehobah. Hakan zai nuna cewa muna da tabbaci cewa Jehobah zai ɗau mataki a lokacin da ya dace. Bari mu yi laꞌakari da abin da faru da ꞌyarꞌuwa Laura French. Ta soma hidima a Bethel da ke Kanada a 1926. Wajen shekaru goma bayan hakan, sai aka yi mata rashin adalci. An zarge ta da kasancewa cikin wani rukunin ꞌyan ridda, kuma aka sallame ta daga Bethel. Mene ne ta yi bayan hakan? Ko da yake ta yi baƙin ciki sosai, ba ta yi maganganu marasa kyau game da ꞌyanꞌuwan ko ƙungiyar Jehobah ba. A maimakon haka, ta ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo a matsayin majagaba na shekara huɗu. A 1940, ta yi mamaki saꞌad da aka sake gayyatar ta zuwa Bethel. Daga lokacin, ta yi hidima a Bethel har na tsawon shekara 50, sai ta rasu. Kamar yadda ꞌyarꞌuwa French ta yi, mu ma za mu iya jimre rashin adalci ta wurin ci-gaba da yin abin da ya dace kuma mu bar batun a hannun Jehobah don ya ɗauki mataki a lokacin da ya dace.—Isha. 26:3, 4.
KA CI-GABA DA BAUTA MA JEHOBAH DA AMINCI
13. Su waye ne “dangin masu aiki a Gidan Yahweh,” kuma mene ne suka yi bayan da aka dawo daga zaman bauta a Babila?
13 Wajen shekaru 500 bayan zamanin Sarki Dauda, an sake ambata Gibiyonawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Yahudawa sun yi shekaru 70 suna bauta a Babila. Daga baya, rukunin farko na Yahudawa sun koma Urushalima tare da Gwamna Zerubbabel. (Ezra 2:1, 2, 58) A shekara ta 468 kafin haifuwar Yesu, rukuni na biyu sun koma Urushalima tare da Ezra wanda marubuci ne. (Ezra 7:1-7) A cikin rukunin mutane guda biyun nan, akwai “dangin masu aiki a Gidan Yahweh.” (Ezra 2:58; 7:7) Su waye ne mutanen nan? Su bayi ne waɗanda ba Yahudawa ba da suke aiki a haikali, kuma da alama da yawa daga cikinsu zuriyar Gibiyonawa ne.
14. Ta yaya Gibiyonawa suka nuna aminci ga Jehobah? (1 Tarihi 9:2)
14 Karanta 1 Tarihi 9:2. “Masu aiki a Gidan Yahweh” suna cikin mutane na farko da suka dawo Urushalima daga Babila. Sun nuna bangaskiya fiye da wasu Yahudawa a Babila. Babu shakka Yahudawa da yawa sun yi kuɗi sosai a Babila, kuma ba su yarda su sadaukar da abubuwan nan don su koma Urushalima su sake gina ta ba. Amma masu aminci da suka dawo, a cikinsu har da zuriyar Gibiyonawa, sun daɗe suna marmarin lokacin da za a maido da bauta ta gaskiya a Urushalima. Shi ya sa suka yi iya ƙoƙarinsu don su dawo. Gibiyonawa ba su da gādon ƙasa kamar Yahudawa. Duk da haka, sun koma don su ci-gaba da aikin da suke yi a haikalin Jehobah, kuma sun taimaka wajen sake gina katangar Urushalima.—Neh. 3:26.
15. Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah?
15 Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah? Mun ga cewa Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke bauta masa da aminci, kuma yana kula da su. Daga lokacin da Jehobah ya ceci Gibiyonawa saꞌad da Israꞌilawa suka shiga Ƙasar Alkawari zuwa lokacin da Israꞌilawa suka dawo daga zaman bauta a Babila ya kai kusan shekaru 1,000. Duk da haka, Jehobah ya ci-gaba da yi musu albarka. Zuriyar Gibiyonawa sun tsira saꞌad da aka hallaka Yahuda da Urushalima a shekara ta 607 kafin haifuwar Yesu. Bayan sun dawo daga bautar, sun ci-gaba da ba da kansu don su yi aiki a haikali. Da alama wasunsu suna zama kusa da haikalin. (Ezra 2:70; Neh. 11:21) Kuma ba sa biyan haraji saboda aikin da suke yi a haikali.—Ezra 7:24.
16. Ta yaya za mu yi koyi da Gibiyonawa a hidimarmu ga Jehobah?
16 Ta yaya za mu yi koyi da Gibiyonawa? Kamar yadda Gibiyonawa suka yi, mu ma muna son mu yi iya ƙoƙarinmu a bautarmu ga Jehobah, kuma mu taimaka ma wasu su yi hakan. Muna yin sadaukarwa da son ranmu don mu bauta ma Jehobah domin muna ƙaunar sa, kuma muna so mu faranta masa rai. Abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Alwin da ke ƙasar Filifin ya yi ke nan. A lokacin da yake aiki a wani kamfanin māi, yana samun kuɗi sosai. Amma yana so ya ƙara ƙwazo a hidimarsa ga Jehobah. A duk lokacin da mai kula da daꞌira ya ziyarci ikilisiyarsu, yakan ɗauki hutu daga aiki don ya iya fita waꞌazi a makon, kuma yin hakan ya sa shi farin ciki. Daga baya, Alwin ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya samu wani aiki dabam da zai ba shi zarafin yin hidimar majagaba. Alwin ya san cewa idan ya yi hakan ba zai riƙa samun kuɗi sosai kamar dā ba. Amma ya sami wani aikin da ya ba shi damar yin hidimar majagaba. Matarsa ma ta soma hidimar majagaba tare da shi, kuma su biyun sun koya wa mutane 21 game da Jehobah har suka yi baftisma. Babu shakka, Jehobah ya ji daɗin abin da maꞌauratan nan suka yi. Mu ma za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana jin daɗin sadaukarwar da muke yi don mu yi masa hidima, kuma zai ci-gaba da kula da mu.—Mat. 6:33.
17. Waɗanne darussa ne muka koya daga Gibiyonawa?
17 Mun koyi game da halayen Jehobah masu kyau ta yadda ya bi da mutanen Gibiyon. Shi Allah ne mai sauƙin kai, da jinƙai, da adalci, da kuma aminci. Yana sāka wa waɗanda suke bauta masa da aminci. Labarin nan yana kuma ɗauke da darussa masu muhimmanci da za mu iya koya daga Gibiyonawa. Kamar Gibiyonawa, muna bukatar mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli masu wuya. Muna kuma bukatar mu kasance da sauƙin kai kuma mu yi duk wani aikin da aka ba mu a ƙungiyar Jehobah. Idan aka yi mana rashin adalci, mu yi haƙuri kuma mu bar kome a hannun Jehobah har sai ya ɗau mataki a lokacin da ya dace. Ƙari ga haka, muna so mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Yayin da muke yin hakan, za mu nuna cewa mun koyi darussa masu kyau daga Gibiyonawa.
WAƘA TA 148 Jehobah Zai Ceci Bayinsa
a Da alama mutanen da Gibiyonawa suka tura wurin Joshua sun haɗa da mutane daga birane uku na Hiwiyawa, wato Kefira, Beyerot, da Kiriyat Yeyarim.—Yosh. 9:17.
b Littafi Mai Tsarki bai bayyana mana takamammen dalilin da ya sa Shawulu ya yi laifin nan ba. Wasu masana sun ce da alama Shawulu ya yi hakan ne domin ba ya so waɗanda ba Israꞌilawa ba su ci-gaba da zama a ƙasar Israꞌila.