Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Mayu pp. 2-7
  • Me Ya Sa Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Suke da Muhimmanci?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Suke da Muhimmanci?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI?
  • ME YA SA ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI SUKE DA MUHIMMANCI?
  • TA YAYA ZA MU IYA GANE ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI?
  • MU ƘUDURA NIYYAR BIN ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI
  • Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Za Su Sa Mu Kasance da Lamiri Mai Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Yi Ja-gorar Sawayenka Da Ƙa’idodin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ta Yaya Ne Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Suke Amfanar Mu?
    Albishiri Daga Allah!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Mayu pp. 2-7

6-12 GA YULI, 2026

WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

Me Ya Sa Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Suke da Muhimmanci?

“Ku yi wa Allah hidima mai tsarki da dukan tunaninku.”—ROM. 12:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da ake nufi da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, da kuma yadda za mu iya gane su saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki.

1-2. (a) A wane lokaci ne aka rubuta Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya sa shawarwarin da suke Littafi Mai Tsarki suke da amfani har wa yau?

AN RUBUTA Littafi Mai Tsarki shekaru da yawa da suka shige. An soma rubutawa shekaru 3,500 da suka shige, kuma an kammala wajen shekaru 2,000 da suka shige. Duk da haka, saƙon da ke ciki yana da amfani sosai a gare mu. (Ibran. 4:12; 2 Tim. 3:​16, 17) Miliyoyin mutane a yau suna bin shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki, kuma hakan yana taimaka musu su yanke shawarwari masu kyau kuma su yi farin ciki.

2 Amma tambayar ita ce, me ya sa shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki suke da amfani a yau duk da cewa an daɗe da rubutawa? Ga dalilai guda biyu. Na ɗaya, shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki sun zo ne daga wurin “Allah mai rai.” Shi ne mahaliccinmu, kuma ya fi mu sanin abin da zai amfane mu. (1 Tim. 4:10; Rom. 16:​26, 27) Na biyu, Littafi Mai Tsarki na ɗauke da ƙaꞌidodi da ba sa canjawa. Shi ya sa shawarwarin da ke ciki suna taimaka wa mutane a yau su shawo kan matsalolinsu kamar yadda suka taimaka wa mutane a dā.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu sami amsoshinsu a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu ga amsoshin tambayoyin nan: Mene ne ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki? Me ya sa suke da muhimmanci sosai a gare mu? Ta yaya za mu gane su saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki? Ƙari ga haka, za mu kuma ga yadda Yesu ya taimaka wa mutane su fahimci ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki.

MENE NE ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI?

4. Mene ne ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki?

4 Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki su ne abubuwan da suke taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ba da wata doka. A wasu lokuta, akan sami ƙaꞌidodin nan a cikin dokar da aka bayar. (Mat. 22:37) A Littafi Mai Tsarki an ba da dokoki don wasu lokuta na musamman, ko don wani yanayi da ake ciki. Amma sanin dalilin da ya sa Jehobah ya ba da dokar zai taimaka mana mu san raꞌayinsa da kuma abin da ya fi muhimmanci a gare shi. Waɗannan dalilan ba sa taɓa canjawa. (Zab. 119:111) Saboda haka, ko da an canja dokar, ko kuma babu doka kwata-kwata game da wani batu, za mu iya sanin raꞌayin Jehobah game da batun.—Isha. 40:8.

5. Ka ba da misalin da ya nuna bambancin da ke tsakanin dokoki da ƙaꞌidodi. (Ka kuma duba hotunan.)

5 Bari mu yi laꞌakari da wani misali da zai taimaka mana mu fahimci bambancin da ke tsakanin dokoki da ƙaꞌidodi. Idan wata mahaifiya tana dafa abinci, za ta iya ba wa ɗan yaronta doka cewa, ‘Kada ka taɓa tukunyar.’ Amma ƙaꞌida, wato dalilin da ya sa ta ba da wannan dokar shi ne don ta san cewa yaron zai ji rauni idan ya taɓa abu mai zafi. Ƙaꞌidar kuma za ta taimaka wa yaron ya guje wa duk wani abin da yake da zafi kamar dutsen guga wato iron, ko kuma wani abu mai zafi da zai iya ƙona shi. Ƙari ga haka, ƙaꞌidar za ta iya taimaka masa a duk inda ya je. Gaskiyar ita ce, idan yaron ya yi girma, zai dafa abinci da tukunya, amma zai bukaci ya yi hakan a hanyar da ba za ta ji masa ba. Ko da yake ba ya bukata ya bi wancan dokar da mahaifiyarsa ta ba shi lokacin da yake ƙarami, yana bukatar ya riƙa tuna da dalilin da ya sa ta ba da dokar.

Hotuna: Wata mahaifiya da ɗanta suna dafa abinci a kicin. Na 1. Ta gaya wa ɗanta cewa kada ya taɓa tukunyar da take dafa abinci da shi da ke kan wuta. Na 2. Bayan wasu shekaru, mahaifiyar tana taimaka wa ɗanta yayin da yake dafa abinci.

Doka na iya canjawa, amma dalilin da ya sa aka kafa dokar ba ya canjawa (Ka duba sakin layi na 5)


ME YA SA ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI SUKE DA MUHIMMANCI?

6. (a) Mene ne Jehobah ya tanada mana a Littafi Mai Tsarki? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya yarda da mu?

6 Jehobah yana ƙaunar mu sosai. Shi ya sa ya ba mu wasu dokoki da za su taimaka mana mu guje wa abubuwan da za su iya jawo mana lahani. (Yak. 2:11) Yana kuma taimaka mana mu fahimci dalilan da suka sa ya ba mu dokokin. Jehobah bai ba mu doka a kan kome da kome ba. Amma, ya ba mu shawarwari a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu yi abin da ya dace ko da babu doka kai tsaye a kan wani batu. Ta haka Jehobah ya nuna ya yarda da mu. Shi ya sa ya ba mu damar yanke shawarwarin da za su nuna cewa muna ƙaunar sa, kuma muna son mu yi masa biyayya.—Gal. 5:13.

7. Ka ba da misalin da ya nuna yadda ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suke taimaka mana? (Ka kuma duba hoton.)

7 Don mu fahimci yadda ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana, bari mu yi laꞌakari da yadda alamu da ake samu a kan titi a wasu ƙasashe suke taimaka wa direbobi. Wasu alamun dole ne a bi su. Alal misali, wata alama za ta iya nuna wa direba yawan gudun da zai iya yi a kan hanyar, ko kuma lokacin da zai bukaci ya tsaya. Idan direban ya ƙi ya bi abin da alamar take nunawa, za a iya hukunta shi. Amma akwai wasu alamu da suke taimaka wa direba ya guje wa duk wani abin da zai iya sa shi cikin damuwa. Alal misali, wata alama za ta iya nuna wa direba cewa hanyar ta yi kwana-kwana, ko kuma cewa ꞌyan makaranta suna wucewa. Idan direban da ya iya tuƙi ya ga irin alamun nan, yakan yi tunani a kan abin da zai yi don kada ya yi hatsari. Kamar rage gudu, ko buga hon da dai sauransu. Haka ma, muna guje wa duk wani abin da Littafi Mai Tsarki ya haramta. Amma ba shi ke nan ba. Muna mai da hankali sosai don kada mu yi tunani, ko mu yi wani abin da zai kai ga yin abin da Jehobah ba ya so. Don mu iya yin hakan, muna bukatar mu fahimci raꞌayin Jehobah game da batutuwa.

Wani dereba yana tuƙi a hanyar da ta yi kwana-kwana kusa da wani dutse. Wutar motar tana haska alamun da ke hanyar.

Kamar yadda alamu da ke kan hanya suke taimaka wa direbobi su guje wa duk wani abin da zai sa su cikin damuwa, haka ma ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suke taimaka mana (Ka duba sakin layi na 7)


8. Saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki mene ne muke bukatar mu yi, kuma ta yaya yin hakan zai amfane mu? (Romawa 12:​1, 2)

8 Me ya sa Jehobah bai ba mu doka a kan kome da kome ba? Domin hakan zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake ɗaukan abubuwa. Saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, zai dace mu yi ƙoƙari mu fahimci darussan da ke ciki kuma mu tambayi kanmu cewa, Me ya sa Jehobah ya sa aka rubuta wannan darasin a cikin Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu yi amfani da darasin a rayuwarmu? Yin hakan zai taimaka mana mu riƙa yin tunani kuma mu fahimci abubuwan da Jehobah yake so. Ta hakan za mu iya “sanin nufi mai kyau na Allah, wanda yake daidai da kuma wanda ya amince da shi.”—Karanta Romawa 12:​1, 2.a

9. A wace hanya ce kuma za mu amfana idan muna bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki? (Ibraniyawa 5:​13, 14)

9 Bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu zama Kristocin da suka manyanta. Idan muna bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, hakan yana ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. (Karanta Ibraniyawa 5:​13, 14.) Iyaye suna ba wa yaransu dokoki da yawa don yaran su san abubuwan da suke bukatar su yi, da waɗanda suke bukatar su guje wa. A wasu lokuta, yaran sukan yi biyayya don kawai kada a hukunta su. Amma ba haka Ubanmu Jehobah yake bi da mu ba. Yana da tabbaci cewa za mu tsai da shawarwari da suka jitu da nufinsa. Idan muka yi hakan, yana farin ciki sosai.—Zab. 147:11; K. Mag. 23:​15, 26; 27:11.

TA YAYA ZA MU IYA GANE ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI?

10. Ta yaya za mu iya gane ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki?

10 Saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, zai dace mu nemi darussa da za su taimaka mana mu fahimci raꞌayin Jehobah game da batutuwa. Zai kuma dace mu yi ƙoƙari mu san dalilin da ya sa Jehobah ya ba da wasu dokoki. Yin hakan zai taimaka mana mu ƙara fahimtar raꞌayin Jehobah. Yana da muhimmanci mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu fahimci ra’ayinsa, kuma muna bukatar mu yi tunani sosai a kan abin da muka karanta. (K. Mag. 2:​10-12) Za mu iya yi wa kanmu tambayoyi kamar: ‘Me ya sa Jehobah ya ba da wannan dokar? Idan Jehobah ya ce kada mu yi wani abu, yaya zai ji idan muka yi abin da ya yi kama da wanda ya ce kada mu yi? Wane darasi ne na koya daga labarin nan, kuma ta yaya zan yi amfani da shi a rayuwata?’ Idan muka sami darussa da ke wani labari, kuma muka fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ba da wata doka, hakan zai taimaka mana mu yanke shawarwarin da za su sa Jehobah farin ciki.

11. Ta yaya Yesu ya koya mana yadda za mu iya gane ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki? (Ka kuma duba hotunan.)

11 A huɗubar da Yesu ya yi a kan dutse, ya nuna mana yadda za mu iya gane ƙaꞌidodin da ke Littafi Mai Tsarki. Bari mu yi laꞌakari da misalai uku. Yesu ya soma da ambata dokar da Jehobah ya bayar, saꞌan nan ya ambata ƙaꞌidar, wato dalilin da ya sa Jehobah ya ba da dokar. Yayin da muke tunani a kan ƙaꞌidodin da Yesu ya koyar, za mu ga yadda za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau a rayuwarmu.

Yesu yana zaune a ƙarƙashin wata bishiya yana koyar da almajiransa.

A Huɗuba a kan Dutse, Yesu ya nuna mana yadda za mu iya gane ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 11)


12. Wace ƙaꞌida ce muka koya daga dokar da ke Matiyu 5:​21, 22? (Ka kuma duba hoton.)

12 Karanta Matiyu 5:​21, 22. “Kada ka yi kisa.” Mene ne muka koya daga wannan dokar? Jehobah ba ya son mu yi fushi da mutane. Ba ya son mu yi ko mu faɗa ko kuma mu yi tunanin wani abin da zai cutar da su. Yesu ya nuna cewa, ko da ba mu yi kisa kai tsaye ba, Jehobah ba zai ji daɗi ba idan mun ci-gaba da yin fushi ko faɗan munanan abubuwa game da mutane. Me ya sa? Domin irin tunani da halayen nan ne suke kai mutum ga yin kisa.—1 Yoh. 3:15.

13. Ta yaya za mu iya yin amfani da ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​21, 22 a yau? (Ka kuma duba hotunan.)

13 Ta yaya za mu iya yin amfani da ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​21, 22 a yau? Ba zai dace mu ci-gaba da yin fushi da wani ba ko da mutumin ya ɓata mana rai. (L. Fir. 19:18; Ayu. 36:13) Me ya sa? Domin hakan zai iya sa mu yi ko mu faɗa abin da bai kamata ba. (K. Mag. 10:12) Alal misali, idan muna fushi da wani za mu iya soma gulma game da shi, ko kuma mu faɗi wasu abubuwa da za su ɓata sunansa. (K. Mag. 20:19; 25:23) A lokacin da Yesu ya koyar da wannan darasin babu intane, ko waya, ko kuma kwamfuta. Amma shawarar da Yesu ya bayar ya nuna cewa bai kamata mu yi amfani da wayarmu ko kwamfuta wajen faɗa munanan abubuwa game da mutane ba. A taƙaice, kamar yadda ba za mu yi kisa kai tsaye ba, ba za mu taɓa faɗa ko mu rubuta abin da zai ɓata sunan wani ko kuma abin da zai sa mutane su daina daraja shi ba.

Hotuna: Na 1. Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka yi kisa.” Na 2. ꞌYanꞌuwa mata biyu suna gulma, wata ꞌyarꞌuwa kuma da take wurin ba ta jin daɗin abin da suke faɗa.

(Ka duba sakin layi na 12-13)


14. Wace ƙaꞌida ce muka koya daga dokar da ke Matiyu 5:​27, 28? (Ka kuma duba hoton.)

14 Karanta Matiyu 5:​27, 28. “Kada ka yi zina.” Mene ne muka koya daga wannan dokar? Jehobah ya tsani lalata. Amma ya kuma tsani duk wani abin da zai kai mutum ga yin lalata. Yesu ya bayyana cewa, idan mutum ya ci-gaba da kallon mace da ba matarsa ba har ya yi shaꞌawar kwana da ita, ya riga ya yi zunubi. Saboda haka, wajibi ne mutum ya yi saurin kawar da shaꞌawar yin lalata, ko da yin hakan bai da sauƙi. (Mat. 5:​29, 30) Waɗanda ba su yi aure ba ma suna bukatar su bi wannan ƙaꞌidar.

15. Ta yaya za mu iya yin amfani da ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​27, 28 a yau? (Ka kuma duba hotunan.)

15 Ta yaya za mu iya yin amfani da ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​27, 28 a yau? Zai dace mu kawar da duk wani tunanin yin lalata ba tare da ɓata lokaci ba. (2 Sam. 11:​2-4; Ayu. 31:​1-3) Hakan ya ƙunshi guje wa kallon hotuna ko bidiyoyin batsa. Ba za mu ce ai kallo kawai muke yi, ba aikatawa ba. Bai kamata mu kasance da irin raꞌayin mutanen duniya da suke ganin cewa kallon wasu irin hotuna ko bidiyoyin batsa ba laifi ba ne. A zamanin Yesu, babu naꞌurori, ko bidiyoyi, ko kuma hotuna kamar yadda suke a yau. Duk da haka, abin da Yesu ya faɗa ya koya mana raꞌayin Jehobah game da hotuna ko bidiyoyin batsa. Abin da Yesu ya faɗa ya kuma koya mana cewa, Jehobah ba zai ji daɗi ba idan muna tura wa mutane saƙonni, ko hotuna, ko bidiyoyin batsa, ko kuma yin taɗin lalata ta waya. Ƙari ga haka, bin wannan shawarar zai taimaka wa maꞌaurata kada su ci amanar juna. (Mal. 2:15) Zai kuma taimaka wa dukanmu ko da mun yi aure ko ba mu yi ba mu guje wa duk wani abin da zai kai ga yin lalata.—K. Mag. 5:​3-14.

Hotuna: 1. Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka yi zina.” 2. Wani ɗanꞌuwa yana cire wata manhajar dandalin sada zumunta a wayarsa.

(Ka duba sakin layi na 14-15)


16. Wace ƙaꞌida ce muka koya daga dokar da ke Matiyu 5:​43, 44? (Ka kuma duba hoton.)

16 Karanta Matiyu 5:​43, 44. “Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka.” Mene ne muka koya daga wannan dokar? Jehobah yana so mu ƙaunaci dukan mutane. Amma abin baƙin cikin shi ne, Yahudawa a zamanin Yesu sun ɗauka cewa abin da dokar take nufi shi ne su ƙaunaci ꞌyanꞌuwansu Yahudawa kuma su tsani maƙiyansu. Amma Yesu ya san cewa ba abin da dokar take nufi ba ke nan. Ya san cewa Jehobah yana so mu ƙaunaci dukan mutane ko da daga ina ne suka fito.—Mat. 5:​45-48.

17. Ta yaya ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​43, 44 za ta taimaka mana a yau? (Ka kuma duba hotunan.)

17 Ta yaya ƙaꞌidar da ke Matiyu 5:​43, 44 za ta taimaka mana a yau? Ƙaꞌidar za ta taimaka mana mu ƙaunaci dukan mutane, kuma ba za mu goyi bayan wani ɓangare saꞌad da ake yaƙi ko tashin hankali ba. (Isha. 2:4; Mik. 4:3) Za ta kuma taimaka mana mu yi wa mutane alheri ko da ƙasarsu, ko alꞌadunsu, ko kuma addininsu ba ɗaya ba ne da namu. (A. M. 10:​34, 35) Za ta kuma taimaka mana mu gafarta wa waɗanda suka yi mana ko kuma ꞌyanꞌuwanmu laifi.—Mat. 18:​21, 22; Mar. 11:25; Luk. 17:​3, 4.

Hotuna: 1. Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka.” 2. Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna nuna wa wani mutum daga wata ƙasa ƙasidar nan “Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!” saꞌad da suke waꞌazi a kasuwa.

(Ka duba sakin layi na 16-17)


MU ƘUDURA NIYYAR BIN ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI

18. (a) Mene ne ya kamata mu ƙudura niyyar yi? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Muna farin ciki cewa Jehobah bai ba mu dokoki da yawa da za mu riƙa bi ba! Yana so mu riƙa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki wajen yanke shawarwari. (1 Kor. 14:20) Saboda haka, idan muna so mu yanke wata shawara, yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu fahimci raꞌayin Jehobah game da batun. (Afis. 5:17) Muna yin hakan don muna ƙaunar sa, ba don muna tsoron hukuncin da zai yi mana ba. Amma, akwai wani abu kuma da zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau, kuma mu sa Jehobah farin ciki. A talifi na gaba, za mu ga yadda ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne bambancin da ke tsakanin dokoki da ƙaꞌidodi?

  • Ka ambata wasu ƙaꞌidodin da Yesu ya koyar a huɗubar da ya yi a kan dutse.

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

a Akwai yanayoyi da dama da Jehobah bai ba mu doka kai tsaye ba. Don haka, muna bukatar mu nemi ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau game da yanayoyin. Jehobah ya ba mu damar yin tunani. Saboda haka, za mu iya yin tunani kuma mu yanke shawarwarin da za su sa shi farin ciki. Yin hakan zai sa ya albarkace mu. Yawancin Kristoci a ƙarni na farko ba su saba da hakan ba. Sun saba da bin dokoki da yawa da malaman addinin Yahudawa suka kafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba