13-19 GA YULI, 2026
WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama
Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Za Su Sa Mu Kasance da Lamiri Mai Kyau
“Ya kamata kowa ya ɗauki kayan kansa.”—GAL. 6:5.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau kuma mu iya yanke shawarwarin da suka dace.
1-2. (a) Wace dama ce Jehobah ya ba Adamu da Hauwaꞌu? (b) Da a ce Adamu da Hauwaꞌu sun yi biyayya da me hakan zai nuna?
DABBOBI suna yin abin da suka ga dama ba tare da yin tunani ba. Naꞌurori kuma sukan yi aiki bisa ga yadda aka tsara su. Amma ꞌyanꞌadam ba haka suke ba. Da aka halicce mu, an ba mu wata dama mai muhimmanci, wato damar yin zaɓi. Hakan yana nufin cewa za mu iya yin tunani kuma mu yanke shawarwari bisa ga abubuwan da muke so. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya halicci mutum a kamanninsa. (Far. 1:26, 27) Jehobah ya halicci Adamu da Hauwaꞌu yadda za su iya zaɓan abubuwan da suke so.
2 Jehobah bai ba wa Adamu da Hauwaꞌu jerin dokoki da yawa ba. Abin da ya gaya musu kawai shi ne su kula da duniya, su hayayyafa, kuma su bi abin da ya ce su yi a matsayinsa na Mahaliccinsu. (Far. 1:28; 2:16, 17) Waɗannan abubuwan ba su fi ƙarfin Adamu da Hauwaꞌu ba, kuma da sun yi, da sun nuna cewa suna ƙaunar Jehobah, kuma suna so su faranta masa rai. Ƙari ga haka, yin hakan zai nuna cewa suna godiya don dukan abubuwa da Jehobah ya ba su.—K. Mag. 23:15.
3. Mene ne Adamu da Hauwaꞌu suka yi da ya nuna cewa ba sa godiya don damar da Jehobah ya ba su?
3 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Adamu da Hauwaꞌu ba su yi zaɓin da ya dace ba. Sun yi wa Jehobah rashin biyayya. Zaɓin da suka yi ya nuna suna son kansu fiye da Jehobah. (Far. 3:1-7) Har wa yau, muna fama don mummunan zaɓin da suka yi.—Rom. 5:12.
4. (a) Bisa ga Galatiyawa 6:5, mene ne dukanmu muke bukatar mu yi? (b) Wane abu ne kuma za mu tattauna a talifin nan?
4 Rayuwa ba sauƙi don kowace rana muna bukatar mu yanke shawarwari da yawa. (Karanta Galatiyawa 6:5.) Wasu suna da wuya sosai, wasu kuma ba su da wuya. Ta yaya za mu yanke shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai? Mataki na farko shi ne, mu fahimci cewa muna bukatar taimakonsa. (K. Mag. 16:3; Irm. 10:23) Duk da cewa Yesu ba ajizi ba ne, ya bukaci taimakon Jehobah. (Ibran. 5:7) Da yake mu ajizai ne, mun fi bukatar taimakon Jehobah. Bari mu tattauna wani abu kuma da Jehobah ya ba mu da zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau, wato lamirinmu.
MENE NE LAMIRI?
5. (a) Mene ne lamiri? (b) Ta yaya lamirinmu yake taimaka mana? (Romawa 2:14, 15)
5 Lamiri wani abu ne da Jehobah ya halicce mu da shi, da ke taimaka mana mu san ko abin da muke yi daidai ne ko ba daidai ba. Kowane ɗanꞌadam yana da lamari ko da bai san dokokin Jehobah ba. (2 Kor. 4:2) Lamirinmu yakan hukunta mu ko ya ꞌyantar da mu don wani tunani ko abin da muka yi. (Karanta Romawa 2:14, 15.) Lamirinmu yakan yi mana gargaɗi idan muna so mu yi wani abin da mun san cewa bai da kyau. (1 Sam. 26:8-11) Zai kuma iya taimaka mana mu yi abin da muka san cewa ya dace. Damar yin zaɓi da Jehobah ya ba mu, ba ya nufin cewa za mu riƙa yanke shawarwarin da za su faranta masa rai a kowane lokaci. Lamirinmu ne zai taimaka mana mu gane ko shawarar da muke so mu yanke ta dace ko ba ta dace ba.
6. Me ya sa ba a kowane lokaci ne lamirinmu yake taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau ba?
6 Amma abin baƙin ciki shi ne, ba a kowane lokaci ne lamirinmu yake taimaka mana ba. Da yake ba mu cika goma ba, haka ma lamirinmu yake. Ƙari ga haka, yadda aka rene mu, ko alꞌadunmu, ko kuma shaꞌawoyinmu marasa kyau za su iya shafan lamirinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce lamirin mutum zai iya zama “bai da ƙarfi,” ko ya zama da “ƙazanta,” ko “ya mutu, kamar an ƙone shi da ƙarfe mai wuta,” ko kuma ya zama mugu. (1 Kor. 8:12; Tit. 1:15; 1 Tim. 4:2; Ibran. 10:22) Irin lamirin da aka ambata a ayoyin nan ba zai taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace ba. Za a iya kwatanta shi da agogon da ba ya aiki da kyau da ya kamata a saita shi don ya ci-gaba da yin aiki da kyau. Don haka, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da lamiri mai kyau. (1 Bit. 3:16) Me zai taimaka mana mu yi hakan?
ABIN DA ZAI TAIMAKA MANA MU KASANCE DA LAMIRI MAI KYAU
7-8. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau? (b) Ta yaya ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suke taimaka mana? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)
7 Mene ne zai taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau? Muna bukatar mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki don mu san raꞌayin Jehobah game da abin da ya dace da abin da bai dace ba. Yin nazarin Kalmarsa zai taimaka mana mu fahimci yadda yake ɗaukan abubuwa. Amma kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, ba a kowane yanayi ne dokoki suke taimaka mana ba. Shi ya sa muke bukatar mu nemi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki domin su ne suke taimaka mana mu ƙara fahimtar yadda Jehobah yake ɗaukan abubuwa.—Isha. 55:9.
8 Za a iya kwatanta rayuwarmu da yin tafiya a wani wuri da babu kowa kuma babu hanya. Yin tafiya a irin wannan wurin ba zai yi sauƙi ba. Amma idan muna da taswira da ke nuna wuraren da za mu iya bi, da wasu abubuwan da za mu iya gani, hakan zai taimaka sosai. Irin wannan taswirar za ta taimaka mana mu tabbata cewa muna bin inda ya kamata, kuma za ta taimaka mana kada mu ɓata. Ainihin dalilin da ya sa muke rayuwa shi ne don mu faranta wa Jehobah rai. Idan muna bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, za mu kasance da tabbaci cewa muna yin abin da ya dace kuma za mu riƙa sa Jehobah farin ciki.
Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki na kama da abubuwan da muke gani saꞌad da muke tafiya a wani wuri da za su tabbatar mana cewa muna bin inda ya kamata (Ka duba sakin layi na 8)
9. Bisa ga Romawa 9:1, wane abu ne kuma zai taimaka wa lamirinmu ya riƙa yin aiki da kyau?
9 Wani abu kuma da zai taimaka wa lamirinmu ya riƙa aiki da kyau shi ne ruhu mai tsarki. (Karanta Romawa 9:1.) Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu fahimci raꞌayin Jehobah game da batutuwa. Yana kuma sa mu ji daɗin yin abin da Jehobah yake so. (Filib. 2:13) Amma me za mu yi don Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki?
10. Me za mu yi don Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki? (Luka 11:10, 13)
10 Mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. (Karanta Luka 11:10, 13.) Muna da tabbaci cewa Jehobah yana a shirye ya ba mu ruhu mai tsarki. (Yoh. 3:34) Yana ba ma waɗanda suke yi masa biyayya ruhu mai tsarki a yalwace. (K. Mag. 1:23; Yak. 1:5) Amma wane abu ne kuma zai taimaka wa lamirinmu ya riƙa yin aiki da kyau?
11. (a) Me ya kamata ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu? (b) Me ya sa zai dace mu tabbata cewa lamirinmu yana aiki da kyau?
11 Mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yi abin da Jehobah yake so. (K. Mag. 8:34, 35) Abin da ya kamata ya fi muhimmanci a rayuwarmu ke nan. Idan muka tuna da hakan a kome da muke yi, hakan zai sa mu kasance da lamiri mai kyau. Lamirinmu zai riƙa yin aiki da kyau idan muna ƙoƙarin sanin raꞌayin Jehobah game da batutuwa, kuma ba ma so mu yi abin da zai ɓata masa rai. Da yake muna rayuwa a mawuyacin lokaci, muna bukatar lamirin da ke aiki da kyau da zai riƙa taimaka mana. A yawancin lokuta, muna bukatar mu yanke shawarwari a kan batutuwan da Littafi Mai Tsarki bai yi magana a kan su dalla-dalla ba. Alal misali, muna bukatar mu yanke shawarwari a kan irin nishaɗin da za mu yi, ko irin aiki ko makarantar da za mu je, ko kuma irin mutanen da za su zama abokanmu. Ta yaya za mu tabbata cewa shawarwarin da muka yanke a irin batutuwan nan za su faranta wa Jehobah rai?—2 Kor. 1:12.
12. Mene ne zai taimaka mana mu san ko lamirinmu yana taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau? (Afisawa 5:10)
12 Mu riƙa yin tunani mai zurfi a kan abubuwan da muke karantawa a Littafi Mai Tsarki. (Zab. 49:3) Saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, zai dace mu nemi ƙaꞌidodin da za su taimaka mana mu gane raꞌayin Jehobah. (Karanta Afisawa 5:10.) Yin hakan zai sa mu san ko lamirinmu yana taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau saꞌad da muke ayyukanmu na yau da kullum ko kuma muna ƙoƙarin warware matsaloli. (K. Mag. 2:4-9, 11-13) Ƙaꞌidodin za su kuma taimaka mana mu inganta yadda lamirinmu yake aiki, kuma za su taimaka mana mu faranta wa Jehobah rai.—Ibran. 5:14.
13. Mene ne muke bukatar mu yi kafin mu yanke wata shawara? Ka ba da misali.
13 Mu nemi sanin raꞌayin Jehobah game da wani batu kafin mu yanke shawara. Kada mu zama kamar Israꞌilawan da suka ci-gaba da zama a Yahuda bayan an hallaka Urushalima a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. Israꞌilawan sun gaya wa Irmiya cewa: “Roƙa mana Yahweh Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.” (Irm. 42:3-6) Amma sun riga sun yanke shawara a kan abin da suke so su yi. Da suka ga cewa abin da Jehobah ya ce su yi ya yi dabam da abin da suke so, sai suka ƙi bin abin da Jehobah ya faɗa, kuma suka yi abin da suka ga dama. Hakan ya jawo mummunan sakamako. (Irm. 42:19-22; 43:1, 2, 4) Saboda haka, kafin mu yanke wata shawara, muna bukatar mu nemi wasu ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu fahimci raꞌayin Jehobah game da batun kuma mu bi abin da muka gani.
14. Me ya sa muke bukatar mu tsai da shawarwari da suka jitu da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki?
14 Mu tsai da shawarwari da suka jitu da ƙaꞌidodin da ke Littafi Mai Tsarki. (Mat. 7:24-29; Yak. 1:23-25) Idan muka tsai da shawarwarin da suka jitu da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, hakan zai nuna cewa muna bin ja-gorancin ruhu mai tsarki, kuma Jehobah zai ci-gaba da ba mu ruhunsa. (A. M. 5:32) Amma idan muka ƙi bin ja-gorancin ruhu mai tsarki, hakan zai nuna cewa ba ma son ruhu mai tsarki ya taimaka mana. (Afis. 4:30; Isha. 63:10; A. M. 7:51) Kuma Jehobah zai iya hana mu ruhu mai tsarkin ma gabaki ɗaya. (Zab. 51:11; 1 Tas. 5:19) Hakan zai yi muni sosai domin muna bukatar ruhu mai tsarki don mu yi nasara.—Afis. 3:16.
YADDA ZA MU IYA SAMUN ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI DA ZA SU TAIMAKA MANA
15-16. (a) Ta yaya za mu iya samun ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana? (b) Waɗanne ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne za su iya taimaka wa ɗalibinmu ya daina shan sigari?
15 Ka yi bincike. Kafin mu iya bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu san wurin da suke a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a ce ɗalibinka ya ga kamar shan sigari ba laifi ba ne. Mai yiwuwa yana tunani cewa: ‘Ai Littafi Mai Tsarki bai ambata kome game da shan sigari ba. To, ta yaya muka san cewa laifi ne?’ Ta yaya za ka taimaka masa ya sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka masa ya fahimci cewa shan sigari zunubi ne? Za ka iya nuna masa Watchtower LABURARE NA INTANE. Idan ya rubuta “sigari,” zai ga talifofi dabam-dabam da suke ɗauke da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki game da shan sigari. Yayin da yake karanta talifofin, waɗanne ƙaꞌidodi ne zai gani?
16 Ga wasu daga cikinsu. (1) Bai kamata mu riƙa shan abin da zai iya kashe mu ba. (Rom. 6:16) (2) Mu guji duk abin da zai jawo mana ila. (2 Kor. 7:1) (3) Jehobah yana so mu bauta masa da dukan zuciyarmu. (Mat. 22:37) (4) Kada mu yi abin da zai cutar da wasu. (Mat. 22:39; 1 Kor. 10:24) (5) Jehobah zai iya ba mu ƙarfin da muke bukata don mu yi abin da ya dace. (Filib. 4:13) Don haka, duk da cewa ba a ambata dalla-dalla game da sigari a Littafi Mai Tsarki ba, ƙaꞌidodin nan za su iya taimaka wa ɗalibinka ya san raꞌayin Jehobah game da shan sigari.
17. Ta yaya waɗanda suke shirin yin aure za su sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka musu?
17 Ta yaya waɗanda suke shirin yin aure za su sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka musu? Har ila, za su iya yin bincike a Watchtower LABURARE NA INTANE. Idan suka rubuta “aure,” za su ga talifofi dabam-dabam da suke ɗauke da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki game da bikin aure. Ga wasu daga cikinsu. (1) Su yi ƙoƙari su yi kome a bikinsu yadda zai ɗaukaka Jehobah. (1 Kor. 10:31, 32) (2) Su saka tufafin da ya dace, da ba zai sa mutane su ji wani iri ba. (1 Tim. 2:9; 1 Bit. 3:3, 4) (3) Su guji yin taƙama da abubuwan da suke da shi kamar yadda mutanen duniya suke yi. (Yoh. 17:14; Yak. 1:27; 1 Yoh. 2:15, 16) (4) Su tsara abubuwan da za a yi a bikinsu da kyau. (1 Kor. 14:40) (5) Kada bikin ya zama wurin shan giya har a bugu. (Gal. 5:21) (6) Su sa wani ya zama uban bikin da zai tabbata cewa kome ya tafi daidai.—Yoh. 2:8, 9.
18-19. (a) Wane littafi ne kuma zai taimaka mana mu sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki? (b) Ta yaya littafin zai taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace game da bukukuwa? (Ka duba akwatin nan “Ka San Raꞌayin Jehobah Game da Batutuwan Nan?”)
18 Wani abu kuma da yake taimaka wa mutane da yawa su sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki shi ne littafin nan, Scriptures for Christian Living. Littafin na ɗauke da jerin nassosi a ƙarƙashin batutuwa dabam-dabam. A kowane batu, akwai tambayoyi da nassosi da za su taimaka mana mu gane ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, idan wani yana shakka ko ya dace ya halarci wani biki ko aꞌa, zai iya samun ƙaꞌidodin da za su taimaka masa a sashen “Celebrations,” (Bukukuwa) a ƙarƙarshin ƙaramin jigon nan, “Celebrations that Christians avoid” (Bukukuwan da Kristoci za su guje wa).
19 A wurin an bayyana dalilin da ya sa zai dace Kristoci su guje wa bukukuwan da ke da alaƙa da addinin ƙarya. (1 Kor. 10:21; 2 Kor. 6:14-18; Afis. 5:10, 11).” An kuma ambata irin bukukuwan. A ƙarƙashin ƙaramin jigon nan, “Nationalistic celebrations,” (Bukukuwa na ƙasa) an ambata nassosin da za su taimaka mana mu san ko za mu yi bukukuwan da suka shafi tarihin ƙasarmu, ko bikin tuna da yaƙin da aka yi a ƙasarmu, ko kuma bikin ɗaukaka wani babban mutum. Muna godiya sosai don tanadodin nan da ƙungiyar Jehobah ta yi mana da suke taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau!
KA NUNA CEWA LAMIRINKA YANA AIKI DA KYAU
20. Ta yaya za mu nuna cewa lamirinmu yana aiki da kyau?
20 Muna godiya sosai don damar yin zaɓi da Jehobah ya ba mu. Amma don mu nuna cewa lamirinmu yana aiki da kyau muna bukatar mu riƙa yanke shawarwarin da za su sa Jehobah farin ciki. Mene ne zai taimaka wa lamirinmu ya riƙa yin aiki da kyau? Muna bukatar taimakon ruhu mai tsarki. Saboda haka, wajibi ne mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa kuma mu ci-gaba da bin ja-gorancinsa. Ƙari ga haka, ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa lamirinmu ya riƙa yin aiki da kyau. Bari mu yi amfani da abubuwan nan da Jehobah ya ba mu a hanyar da ta dace. Yin hakan zai sa mu amfana sosai daga Kalmar Allah.—2 Tim. 3:16, 17; Ibran. 4:12.
WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”