2-8 GA MARIS, 2026
WAƘA TA 97 Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu
Ka Ci-gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah
JIGON SHEKARARMU NA 2026: “Waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah, suna farin ciki.”—MAT. 5:3.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da muke bukatar mu yi don mu yi farin ciki kuma mu amfana daga ja-gorancin da Jehobah yake mana.
1. Waɗanne abubuwa ne ꞌyanꞌadam suke bukata? (Matiyu 5:3)
JEHOBAH ya san abin da mutane suke bukata. Alal misali, don mu rayu muna bukatar abinci, da kayan sakawa, da kuma wurin zama. Idan ba mu da waɗannan abubuwan, rayuwa za ta yi mana wuya ko kuma mu mutu. Ban da haka, akwai wani abu kuma da Jehobah ya san cewa muna bukata. Muna bukatar mu san Jehobah kuma mu bi ja-gorancinsa. (Karanta Matiyu 5:3.) Idan muna so mu yi farin ciki a rayuwa, wajibi ne mu san cewa muna bukatar ja-gorancinsa kuma mu ci-gaba da dogara gare shi.
2. Ta yaya yanayinmu ya yi kama da na maroƙi?
2 Ainihin furucin da aka fassara zuwa waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah, zai iya nufin masu roƙo da suke neman a taimaka musu. Ka yi tunanin wani maroƙi da rigarsa ta yi datti, ta yayyage kuma bai da abin da zai ci. Yana kwana a cikin sanyi idan dare ya yi, kuma rana tana tashi ta faɗi a kansa. Mutane ba sa son zuwa kusa da shi saboda yanayinsa. Kullum a gajiye yake, kuma ba ya farin ciki. Wannan maroƙin ya san cewa yana bukatar a taimaka masa don ya rayu. Haka ma, waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Jehobah suna saurin neman taimakonsa kuma suna sauraronsa.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A wannan talifin, za mu ga abin da za mu koya daga wata mata ꞌyar Finikiya da ta roƙi Yesu ya taimaka mata. Labarinta ya nuna halaye uku da muke bukatar mu kasance da su idan muna so Jehobah ya ci-gaba da yi mana ja-goranci. Bayan haka, za mu tattauna game da mazaje uku da suka nuna cewa suna bukatar ja-gorancin Jehobah a rayuwarsu, wato Bitrus da Bulus da kuma Sarki Dauda.
HALAYE UKU DA MUKE BUKATA
4. Mene ne wata mata ꞌyar Finikiya take so Yesu ya yi mata?
4 Wata rana, wata mata ꞌyar Finikiya ta zo wurin Yesu. ꞌYar matar “tana fama da aljani da ke ba ta wahala sosai.” (Mat. 15:21-28) Matar ta durƙusa a gaban Yesu tana roƙon sa ya taimake ta. Bari mu ga wasu halaye uku da za mu iya koya daga wurinta.
5. Waɗanne halaye ne matar ta nuna, kuma mene ne Yesu ya yi? (Ka kuma duba hoton.)
5 Matar ta nuna sauƙin kai sosai. Me ya sa muka ce hakan? Domin ba ta yi fushi da abin da Yesu ya faɗa ba. Yesu ya ce tana kama da yaran karnuka da mutanen da ba Yahudawa ba suke ajiyewa a gidajensu. Da a ce kai ne Yesu ya yi wa magana haka, yaya za ka ji? Shin, za ka ji kamar ya zage ka ne kuma ka fita harkan sa? Matar ba ta yi hakan ba, ta nace kuma ta ci-gaba da roƙon Yesu ya taimake ta. Me ya sa ta yi hakan? Ta ba da gaskiya ga Yesu. Bangaskiyar matar ta sa Yesu ya taimaka mata. Ko da yake Yesu ya gaya mata cewa an turo shi ne “wurin jamaꞌar Israꞌila” kawai. Ya taimaka wa matar, kuma ya cire aljanin daga jikin ꞌyarta.
Mata ꞌyar Finikiya da ta so Yesu ya taimaka wa ꞌyarta ta kasance da sauƙin kai, ta ci-gaba da roƙon sa kuma ta ba da gaskiya cewa Yesu zai iya taimaka mata (Ka duka sakin layi na 5)
6. Mene ne muka koya daga wurin wannan matar?
6 Muna bukatar mu yi koyi da wannan matar idan muna so mu amfana daga ja-gorancin Jehobah. Muna bukatar mu kasance da sauƙin kai kuma mu ci-gaba da roƙon Jehobah ya taimaka mana. Ƙari ga haka, muna bukatar mu ba da gaskiya ga Yesu Kristi kuma mu amince da waɗanda yake amfani da su wajen yi mana ja-goranci. (Mat. 24:45-47) Idan muka kasance da halayen nan, za mu sa Jehobah da Ɗansa farin ciki. Za su ci-gaba da taimaka mana da yi mana ja-goranci. (Ka kuma duba Yaƙub 1:5-7.) Yanzu, bari mu ga yadda Jehobah yake yi mana ja-goranci, da kuma tanada mana abubuwan da muke bukata don mu ci-gaba da yin farin ciki. Za mu kuma ga yadda labaran manzo Bitrus, da Bulus, da kuma Sarki Dauda za su taimaka mana mu san abin da za mu yi don mu amfana daga tanadodin da Jehobah yake mana.
MU CI-GABA DA YIN NAZARIN KALMAR ALLAH KAMAR BITRUS
7. Wane aiki ne Yesu ya ba wa Bitrus, kuma mene ne Bitrus yake bukatar ya yi? Ka bayyana. (Ibraniyawa 5:14–6:1)
7 Ka yi laꞌakari da labarin manzo Bitrus. Yana cikin Yahudawa na farko da suka gane cewa Yesu ne Almasihu. Ya kuma gane cewa Jehobah yana amfani da Yesu wajen koya wa mutane game da yin rayuwa “har abada.” (Yoh. 6:66-68) Kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa Bitrus cewa: “Ka ciyar da ꞌyan tumakina.” (Yoh. 21:17) Bitrus ya cika wannan aikin da aka ba shi, kuma Jehobah ya taimaka masa ya rubuta wasiƙu biyu da suke Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, Bitrus ya bukaci ya ci-gaba da yin nazarin Kalmar Allah. Alal misali, ya yi nazarin wasiƙun da manzo Bulus ya rubuta da suke cikin Littafi Mai Tsarki. Bitrus ya ce, wasu abubuwan da Bulus ya rubuta a wasiƙarsa suna da “wuyar ganewa.” (2 Bit. 3:15, 16) Amma Bitrus ya ci-gaba da yin nazari a kansu. Yana da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa ya fahimce su, kuma ya yi abin da ya koya.—Karanta Ibraniyawa 5:14–6:1.
8. Mene ne Bitrus ya yi saꞌad da wani malaꞌika ya gaya masa abin da Jehobah yake so ya yi?
8 Bitrus ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah ta wurin bin ja-gorancinsa. Alal misali, wata rana Bitrus ya ga wahayi. A wahayin, wani malaꞌika ya gaya masa ya ci dabbobin da Dokar Musa ta hana Yahudawa ci. Da yake Bitrus Bayahude ne, ya ga kamar abin da malaꞌikan ya gaya masa ba daidai ba ne. Shi ya sa da farko ya ce: “Aꞌa, Ya Ubangiji, ban taɓa cin wani abu marar tsabta kuma mai ƙazanta ba.” Malaꞌikan ya gaya masa cewa: “Ka daina kiran abin da Allah ya tsabtace, abu mai ƙazanta.” (A. M 10:9-15) Shin, Bitrus ya canja raꞌayinsa kuma ya bi abin da malaꞌikan ya gaya masa? Ƙwarai kuwa! Ta yaya muka san hakan? Jim kaɗan bayan da Bitrus ya ga wahayin, wasu mazaje uku sun zo wurinsa. Sun ce maigidansu Karniliyus yana kiran sa. Da a dā ne, Bitrus ba zai taɓa yarda ya je gidansa ba, domin shi ba Bayahude ba ne. A lokacin, Yahudawa suna ganin bai kamata Bayahude ya shiga gidan wani da ba Bayahude ba. (A. M 10:28, 29) Amma saꞌad da Jehobah ya nuna wa Bitrus cewa yana son dukan mutane su ji waꞌazin labari mai daɗi, Bitrus ya canja raꞌayinsa ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ya yi abin da Jehobah ya gaya masa. (K. Ma 4:18) Ya yi wa Karniliyus da dukan ꞌyan gidansa waꞌazi. Kuma ya ji daɗin ganin yadda suka amince da abin da ya gaya musu, suka sami ruhu mai tsarki, kuma suka yi baftisma.—A. M 10:44-48.
9. A waɗanne hanyoyi biyu ne za mu amfana idan muna nazarin abubuwan da suke da wuyar fahimta?
9 Kamar Bitrus, muna bukatar mu riƙa karanta Kalmar Allah kullum. A yawancin lokuta, mun fi son karanta abubuwan da suke da sauƙin fahimta. Amma, wajibi ne mu riƙa marmarin yin nazarin abubuwan da suke da wuyar fahimta. Muna bukatar mu tabbata cewa mun sami isasshen lokaci don yin nazarin Kalmar Allah. Kuma yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu fahimci abubuwan da suke mana wuyar fahimta a dā. Me ya sa yin hakan yake da muhimmanci? Ga wasu hanyoyi biyu da za mu amfana idan muka yi hakan: Na ɗaya, za mu koyi abubuwa game da Jehobah. Kuma hakan zai sa mu ƙara ƙauna da kuma daraja shi. Na biyu, za mu yi marmarin gaya wa mutane abubuwan da muka koya game da Jehobah. (Rom. 11:33; R. Yar. 4:11) Labarin Bitrus ya kuma koya mana cewa, idan muka samu ƙarin haske a kan wani batu a Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu yi saurin canja raꞌayi da kuma yadda muke yin abubuwa. Yin hakan ne kawai zai sa mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Kuma Jehobah zai ci-gaba da yi mana ja-goranci.
KA KASANCE DA HALAYEN DA JEHOBAH YAKE SO KAMAR BULUS
10. Bisa ga Kolosiyawa 3:8-10, mene ne muke bukatar mu yi don mu sa Jehobah farin ciki?
10 Wata hanya da Jehobah yake mana ja-goranci ita ce ta wajen koya mana yadda za mu kasance da halayen da yake so. (Karanta Kolosiyawa 3:8-10.) Kasancewa da irin halayen nan ba abu mai sauƙi ba ne. Bari mu yi laꞌakari da labarin Bulus. A lokacin da yake matashi, ya yi ƙoƙarin yin abubuwan da yake ganin za su sa Allah farin ciki. (Gal. 1:14; Filib. 3:4, 5) Amma gaskiyar ita ce, abubuwan da ya yi ba su sa Allah farin ciki ba. A lokacin, Bulus bai san gaskiya game da Yesu ba, kuma shi mai girman kai ne. Bulus da kansa ya ce, a dā shi mai wulaƙanta bayin Allah ne.—1 Tim. 1:13.
11. Wane hali ne Bulus ya yi ƙoƙari sosai ya daina? Ka bayyana.
11 Kafin Bulus ya zama Kirista, shi mai zafin rai ne. Littafin Ayyukan Manzanni ya nuna cewa Bulus ya yi fushi da mabiyan Yesu sosai, har ya so ya “kashe” su. (A. M. 9:1) Amma bayan da Bulus ya zama Kirista, ya zama mutumin kirki da kuma mai haƙuri. (Afis. 4:22, 31) Duk da haka, a lokacin da Bulus da Barnaba suka kasance da raꞌayi dabam-dabam game da wani batu, Bulus ya yi fushi kuma “suka yi gardama sosai” har suka rabu da juna. (A. M. 15:37-39) Ko da yake Bulus ya koma gidan jiya, bai bar hakan ya sa shi ya yi sanyin gwiwa ba. Ya ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsa don ya kasance da halayen da za su sa Jehobah farin ciki.—1 Kor. 9:27.
12. Me ya taimaka wa Bulus ya canja halayensa da ba su dace ba?
12 Me ya taimaka wa Bulus ya canja halayensa da ba su dace ba, kuma ya kasance da halayen da Jehobah yake so? Abin da ya taimaka masa shi ne kasancewa da sauƙin kai. (Filib. 4:13) Kamar Bitrus, Bulus ya dogara ga Jehobah ya taimaka masa ya yi canje-canjen da yake bukata. (1 Bit. 4:11) Duk da haka, a wasu lokuta Bulus ya yi kuskure, kuma hakan ya sa shi sanyin gwiwa. Amma a duk lokacin da ya yi sanyin gwiwa, yakan yi tunani a kan abubuwa masu kyau da Ubansa na sama ya yi masa, kuma hakan yana sa shi ya ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsa.—Rom. 7:21-25.
13. Ta yaya za mu yi koyi da Bulus?
13 Kamar Bulus, ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, muna bukatar mu ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu kasance da halaye masu kyau. A wasu lokuta, za mu iya yin kuskure. Za mu iya yin fushi ko kuma mu faɗi wani abin da bai dace ba. Idan hakan ya faru, bai kamata mu yi tunani cewa ba za mu iya faranta wa Jehobah rai ba. A maimakon haka, mu ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen zama masu halayen kirki. (Rom. 12:1, 2; Afis. 4:24) Yayin da muke yin hakan, zai dace mu tuna cewa, idan muna so mu kasance da halayen kirki, muna bukatar mu ƙara sanin Jehobah, kuma mu bi ja-gorancinsa.
KA BAR JEHOBAH YA KĀRE KA KAMAR DAUDA
14-15. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake kāre bayinsa a yau? (Zabura 27:5) (Ka kuma duba hoton.)
14 Idan Jehobah yana kāre mu, za mu kasance da farin ciki. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake kāre mu, kuma mene ne muke bukatar mu yi don ya kāre mu?
15 Sarki Dauda ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kāre shi a lokacin da yake fama da matsaloli. (Karanta Zabura 27:5.) Ta yaya Jehobah yake kāre bayinsa a yau? Yana kāre mu daga duk wani mutum ko wani abin da zai sa mu daina kasancewa da bangaskiya. Ya yi alkawari cewa, zai sa mu ci-gaba da kasancewa da dangantaka na kud da kud da shi ko da mutane sun yi ƙoƙari su sa mu daina bauta masa. (Zab. 34:7; Isha. 54:17) Ko da yake Shaiɗan da aljanunsa, da waɗanda suke tsananta mana suna da ƙarfi sosai, Jehobah ya fi su ƙarfi. Ko da sun kashe mu, Jehobah zai ta da mu a nan gaba. (1 Kor. 15:55-57; R. Yar. 21:3, 4) Jehobah yana kuma taimaka mana saꞌad da muke cikin damuwa don kada mu daina bauta masa. (K. Mag. 12:25; Mat. 6:27-29) Ƙari ga haka, Ubanmu mai ƙauna ya ba mu ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da suke ƙarfafa mu, kuma suna taimaka mana a lokacin da muke fama da matsaloli. Ya kuma ba mu dattawa da suke koyar da mu don mu ci-gaba da kasancewa da bangaskiya. (Isha. 32:1, 2) Ban da haka ma, a taronmu akan tuna mana wasu abubuwan da muke bukatar mu yi da za su sa Jehobah ya taimaka mana, ya kuma kāre mu.—Ibran. 10:24, 25.
Wata ꞌyarꞌuwa ta nemi ja-gorancin Jehobah ta wurin halartar taro (Ka duba sakin layi na 14-15)
16. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya kāre Dauda?
16 Saꞌad da Dauda yake yin abubuwan da Jehobah yake so, Jehobah ya kāre shi. Ya taimaka masa ya yanke shawarwari masu kyau, kuma hakan ya sa Dauda farin ciki. (Ka duba Karin Magana 5:1, 2.) Amma saꞌad da Dauda ya yi wa Jehobah rashin biyayya, ya yi fama da sakamako marar kyau, kuma Jehobah bai kāre shi ba. (2 Sam. 12:9, 10) A wasu lokuta kuma, Dauda ya yi fama sanadiyyar wulaƙancin da wasu suka yi masa. A lokutan nan, Dauda ya yi adduꞌa ga Jehobah, kuma Jehobah ya kāre shi. Ta yaya Jehobah ya yi hakan? Ya yi wa Dauda alkawari cewa zai kula da shi, kuma zai taimaka masa ya san cewa yana ƙaunar sa.—Zab. 23:1-6.
17. Ta yaya za mu iya yin koyi da Dauda?
17 Za mu yi koyi da Dauda idan muka roƙi Jehobah ya taimaka mana mu iya tsai da shawarwari masu kyau. Zai dace mu tuna cewa idan muka yi wa Jehobah rashin biyayya, Jehobah ba zai kāre mu daga sakamakon mummunan shawarar da muka yanke ba. (Gal. 6:7, 8) Amma idan muna fama da wasu matsaloli da ba laifin mu ba ne, mu yi adduꞌa ga Jehobah da tabbaci cewa zai taimaka mana.—Filib. 4:6, 7.
KA CI-GABA DA BIN JA-GORANCIN JEHOBAH
18. Mene ne raꞌayin mutane da yawa a yau game da ja-gorancin Jehobah, kuma mene ne muke bukatar mu yi idan muna so Jehobah ya ci-gaba da yi mana ja-goranci? (Ka kuma duba hotunan.)
18 Jigon shekararmu na 2026 shi ne: “Waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah suna farin ciki.” A yau, bin ja-gorancin Jehobah yana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin mutane da yawa suna ganin ba sa bukatar Allah a rayuwarsu. Da yawa kuma da suka yi imani da Allah suna bauta masa yadda suka ga dama. Wasu kuma sun dogara ga ja-gorancin ꞌyanꞌadam kuma hakan ba ya sa su farin ciki. Wajibi ne mu guje wa irin waɗannan halayen. Ta yaya za mu yi hakan? Muna bukatar mu ci-gaba da yin nazarin Kalmar Allah, mu kasance da irin halayen da Jehobah yake so, kuma mu riƙa bin ja-gorancinsa.
Muna bukatar mu ci-gaba da bin ja-gorancin Jehobah (Ka duba sakin layi na 18)a
WAƘA TA 162 Koyo don In San Allahna
a BAYANI A KAN HOTUNA : ꞌYarꞌuwar tana nuna cewa tana son Jehobah ya yi mata ja-goranci ta wurin yin nazarin Hasumiyar Tsaro, da yi wa mutane alheri, da kuma neman taimako daga wurin dattawa.