Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Disamba p. 31
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Sashe na 1
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Disamba p. 31

Ka Tuna?

Shin, ka karanta duka Hasumiyar Tsaro da aka fitar a shekarar nan da kyau? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Waɗanne abubuwa ne suke sa mu ɗaukaka Jehobah?

Muna ɗaukaka Jehobah domin muna daraja da kuma ƙaunar sa sosai. Ƙari ga haka, muna ɗaukaka Jehobah domin muna so mutane su san shi.—w25.01, shafi na 3.

Idan wani ya ɓata mana rai, ta yaya za mu nuna cewa mu masu gafartawa ne?

Kar mu yi kamar ba abin da ya faru, ko mu riƙe mutumin a zuciya. Mu yi ƙoƙari mu daina fushi. Hakan zai taimaka mana mu iya yafewa.—w25.02, shafi na 15-16.

Ta yaya Markus ya kafa wa ꞌyanꞌuwa maza misali mai kyau?

Markus ya nuna cewa yana da niyyar yin hidima. Ko da yake akwai abin da ya faru da ƙila ya dame shi sosai, hakan bai hana shi ci-gaba da yin hidimarsa ba. Ya ƙulla dangantaka mai kyau da Bulus da kuma ꞌyanꞌuwan da suka manyanta.—w25.04, shafi na 27.

Mene ne Yesu yake nufi saꞌad da ya yi adduꞌa cewa: “Na kuma sanar musu da sunanka”? (Yoh. 17:26)

Almajiransa sun riga sun san sunan Allah. Amma Yesu yana so su san fiye da hakan. Ya taimaka musu su ƙara sanin abubuwa game da Jehobah. Hakan ya ƙunshi nufinsa, da ayyukansa, da kuma halayensa.—w25.05, shafi na 20-21.

Idan mu masu sauƙin kai ne, me za mu riƙa tunawa?

Ya kamata mu riƙa tuna cewa akwai abubuwa da yawa da ba mu sani ba. Alal misali, ba mu san lokacin da ƙarshen zamanin nan zai zo ba, ko abubuwan da Jehobah zai yi a lokacin ba. Ba mu kuma san abin da zai faru gobe ba, ko ainihin yadda Jehobah yake ɗaukan mu ba.—w25.06, shafi na 15-18.

Mene ne zai taimaka mana mu amfana sosai daga wani talifi ko jawabi?

Mu tambayi kanmu, ‘Me aka faɗa da ya nuna cewa wannan batun gaskiya ne? Shin, akwai wani kwatancin da zan iya amfani da shi wajen koyarwa? Waye ne zai so mu tattauna wannan batun?’—w25.07, shafi na 19.

Mene ne za mu iya koya daga yadda Jehobah ya gafarta wa Dauda?

Ko da yake Dauda ya yi zunubai masu tsanani, saꞌad da ya tuba da gaske, Jehobah ya gafarta masa. (1 Sar. 9:​4, 5) Idan Jehobah ya gafarta mana, ba zai sake kama mu da laifi, ko kuma ya hukunta mu domin zunubin ba.—w25.08, shafi na 17.

Me za ka iya yi idan wani batu ya yi wa ɗalibinka wuyar fahimta?

Idan akwai wani batu da ya yi wa ɗalibinka wuyar fahimta, za ku iya ci-gaba da wani batu dabam kuma ku dawo kan batu mai wuyar a wani lokaci.—w25.09, shafi na 24.

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “ruɗu na zunubi.” (Ibran. 3:13) Mene ne hakan yake nufi?

Zunubi yana iya sa mu yi abin da bai dace ba. Zai kuma iya sa mu yi ta shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu.—w25.10, shafi na 16.

Waɗanne abubuwa uku ne za mu iya yi don mu inganta yadda muke adduꞌa?

(1) Yin tunani game da halayen Jehobah. (2) Yin tunani game da matsalolin da muke fuskanta a yanzu haka. Alal misali mu yi tunani ko akwai wanda ya kamata mu gafarta masa. (3) Kada mu riƙa yin adduꞌa da gaggawa. Hakan zai ba mu damar bayyana ainihin yadda muke ji.—w25.10, shafi na 19-20.

Ta yaya za mu iya taimaka ma waɗanda suka tsufa?

Za mu iya kira ko ziyartar su. Za mu iya raka su zuwa asibiti. Ko kuma mu yi waꞌazi tare da su.—w25.11, shafi na 6-7.

Waɗanne abubuwa ne za ku yi don aurenku ya ɗaukaka Jehobah?

Ku bi dokar da gwamnati ta kafa game da aure. Ku tabbata cewa bikin aurenku ya nuna cewa kuna da halaye masu kyau da ruhu mai tsarki yake bayarwa. Ku zaɓi kaya masu kyau kuma ku guje wa alꞌadun da suka saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Ku riƙa nuna cewa kuna daraja juna saꞌad da kuke shirye-shiryen aurenku.—w25.12, shafi na 21-24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba