Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Yuli pp. 14-19
  • Abubuwan da Ka Koya Tun Farko Za Su Amfane Ka a Yau Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abubuwan da Ka Koya Tun Farko Za Su Amfane Ka a Yau Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH NE MAHALICCI
  • ME YA SA ALLAH YA ƘYALE WAHALA?
  • MUNA RAYUWA A “KWANAKIN ƘARSHE”
  • KA NUNA GODIYA DON ABUBUWAN DA JEHOBAH YAKE TUNA MANA
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka San Bambancin Gaskiya da Karya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Yuli pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 30

WAƘA TA 97 Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu

Abubuwan da Ka Koya Tun Farko Za Su Amfane Ka a Yau Kuwa?

“Zan dinga tuna muku da waɗannan abubuwa, ko da yake kun riga kun san su, kun kafu sosai cikin gaskiya da kuka karɓa.”—2 BIT. 1:12.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda abubuwan da muka koya farko-farko saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki za su ci gaba da taimaka mana a yau.

1. Yaya ka ji da ka soma koyan gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

ABUBUWAN farko da muka koya saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki sun canja rayuwarmu. Alal misali, lokacin da muka koya cewa sunan Allah Jehobah ne, hakan ya sa muka yi marmarin ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. (Isha. 42:8) Saꞌad da muka koyi gaskiya game da matattu, hakan ya sa mun daina damuwa da tunani cewa wani namu da ya mutu yana shan wahala. (M. Wa. 9:10) Ƙari ga haka, saꞌad da muka koyi gaskiya game da alkawarin aljanna a nan duniya, mun daina yawan damuwa game da yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Muna da tabbaci cewa ba za mu yi rayuwa na ꞌyan shekaru 70 ko 80 kawai ba. A maimakon haka, za mu yi rayuwa har abada.—Zab. 37:29; 90:10.

2. Me ya sa Bitrus ya tuna wa Kiristoci da suka daɗe suna bauta wa Jehobah su ci gaba da tuna abubuwan farko da suka koya daga Littafi Mai Tsarki? (2 Bitrus 1:​12, 13)

2 Abubuwan farko da muka koya saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki suna da muhimmanci sosai. Kuma bai kamata mu manta da su ba. Shi ya sa a wasiƙa na biyu da Bitrus ya rubuta, ya rubuta shi ne zuwa ga Kiristoci da suka “kafu sosai cikin gaskiya.” (Karanta 2 Bitrus 1:​12, 13.) A lokacin, akwai mugayen mutane da malaman ƙarya a cikin ikilisiya, da suke so su ruɗi mutane. (2 Bit. 2:​1-3) Bitrus ya so ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da mata su san yadda za su kāre kansu daga ƙaryar da mutanen suke koyarwa. Don ya iya cim ma hakan, ya tuna musu abubuwan da suka koya tun daga farko. Waɗannan abubuwan za su taimaka musu su riƙe amincinsu ga Jehobah.

3. Me ya sa dukan Kiristoci suke bukatar su ci gaba da yin tunani a kan abubuwan da suka koya farko-farko daga Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.

3 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, za mu iya amfana daga abubuwan da muka koya farko-farko daga Littafi Mai Tsarki. Alal misali: Wanda ya ƙware a dafa abinci da wanda bai ƙware ba za su iya yin amfani da kayan miya iri ɗaya. Amma wanda ya ƙware zai san yadda zai yi amfani da kayan miyan wajen dafa miya mai ɗanɗano a hanyoyi dabam-dabam. Haka ma, waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah za su iya koyan darussa dabam-dabam daga wata aya fiye da waɗanda ba su daɗe da soma bauta wa Jehobah ba. Mai yiwuwa yanayinmu ya canja tun da muka yi baftisma, ko kuma mun yi ayyuka dabam-dabam a ƙungiyar Jehobah. Saboda haka, idan muka yi tunani a kan abubuwan da muka koya farko-farko saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, za mu iya ga wasu hanyoyi dabam-dabam da za su iya taimaka mana.

JEHOBAH NE MAHALICCI

4. Ta yaya sanin cewa Jehobah ne Mahalicci ya taimaka mana?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ne ya gina kome.” (Ibran. 3:4) Mun san cewa Allah, mafi iko da hikima ne ya halicci duniyar nan, da kome da ke ciki. Shi ne ya halicce mu, kuma ya san mu ciki da waje. Mafi muhimmanci ma, ya damu da mu kuma ya san abin da zai fi amfanar mu. Sanin cewa Jehobah ne Mahaliccinmu ya sa rayuwarmu ta kasance da maꞌana.

5. Mene ne zai taimaka mana mu zama masu sauƙin kai? (Ishaya 45:​9-12)

5 Sanin cewa Jehobah ne Mahalicci zai kuma sa mu zama masu sauƙin kai. Alal misali, akwai lokacin da Ayuba ya faɗi wasu abubuwa da ba su dace ba game da Jehobah. Ya yi ƙoƙarin nuna cewa bai da laifi, maimakon ya mai da hankali a kan abin da ya fi muhimmanci. Amma Jehobah ya tuna masa cewa shi ne ya halicci kome da kome. (Ayu. 38:​1-4) Hakan ya sa Ayuba ya gane cewa yadda Allah yake yin abubuwa dabam ne da na ꞌyanꞌadam. Shi ya sa annabi Ishaya ya yi tambaya ya ce: “Ko laka za ta yi gardama da mai gina tukunya cewa, ‘Me kake yi?’”—Karanta Ishaya 45:​9-12.

6. A wane lokaci ne zai dace mu yi tunani game da hikima da kuma ikon Mahaliccinmu? (Ka kuma duba hotunan.)

6 Idan mutum ya daɗe yana bauta wa Jehobah, zai iya soma dogara ga nashi tunani, maimakon dogara ga Jehobah da kuma Kalmarsa. (Ayu. 37:​23, 24) Amma mutum zai fi amfana idan ya yi tunani a kan yawan hikima da ikon Mahaliccinsa. (Isha. 40:22; 55:​8, 9) Yin hakan zai sa ya gane cewa raꞌayin Jehobah ya fi nashi muhimmanci, kuma hakan zai sa ya kasance da sauƙin kai.

Hotuna: Na 1. Wani dattijo ya ba da shawarar da sauran dattawa ba su amince da shi ba. Na 2. Daga baya da dare, ya kalli taurari a sama sai yana tunani.

Me zai taimaka mana mu tuna cewa raꞌayin Jehobah ya fi namu? (Ka duba sakin layi na 6)e


7. Mene ne ꞌYarꞌuwa Rahela ta yi don ta iya amincewa da wani canjin da aka yi?

7 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Rahela daga Slovenia ta gano cewa yin tunani game da Mahaliccinta, ya taimaka mata ta amince da wasu canje-canjen da ƙungiyarmu take yi. Ta ce: “A wasu lokuta, ba ya min sauƙi in amince da wasu canje-canjen da ake yi a ƙungiyarmu. Alal misali, ko da yake na kalli Karin Bayania da aka ce maza za su iya barin gemu, na yi mamaki da farko da na ga wani ɗanꞌuwa da gemu yana ba da jawabi. Na roƙi Jehobah ya taimaka min in amince da wannan canjin.” ꞌYarꞌuwa Rahela ta gane cewa, da yake Jehobah ne Mahalicci, yana yi wa ƙungiyarsa ja-goranci a hanyar da ta fi dacewa. Idan yana maka wuya ka amince da wani canjin da aka yi, zai dace ka yi tunani a kan yawan hikima da ikon Mahaliccinmu.—Rom. 11:​33-36.

ME YA SA ALLAH YA ƘYALE WAHALA?

8. Ta yaya muka amfana don mun san dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala?

8 Me ya sa Allah ya ƙyale wahala? Wasu da ba su san amsar wannan tambayar ba suna fushi da Allah, wasu kuma sun ce babu Allah ma kwatakwata! (K. Mag. 19:3) Amma mun koyi cewa, wahalar da muke sha ba laifin Jehobah ba ne. Mutane suna shan wahala kuma suna mutuwa ne don zunubi da ajizancin da muka gāda. Mun kuma koyi cewa, haƙurin da Jehobah yake yi ya ba wa miliyoyin mutane damar koya game da shi, da kuma yadda zai kawo ƙarshen wahalar da muke sha. (2 Bit. 3:​9, 15) Sanin dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala ya ƙarfafa mu, kuma ya sa mu ƙara kusantar sa.

9. A waɗanne yanayoyi ne za mu bukaci mu yi tunani a kan dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala?

9 Mun san muna bukatar mu kasance da haƙuri yayin da muke jiran Jehobah ya kawar da wahalar da muke sha. Duk da haka, idan wani namu ya rasu, ko aka yi mana rashin adalci, ko kuma muna fama da wani yanayi mai wuya, za mu iya gani kamar Jehobah yana ɓata lokaci wajen kawo ƙarshen wahalar da muke sha. (Hab. 1:​2, 3) A irin wannan lokacin, abin da zai fi alheri shi ne, mu yi tunani a kan dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala.b (Zab. 34:19) Ƙari ga haka, zai dace mu yi tunani a kan shirin da yake yi na kawo ƙarshen wahala har abada.

10. Me ya taimaka wa ꞌYarꞌuwa Anne lokacin da mahaifiyarta ta mutu?

10 Sanin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala zai taimaka mana mu jimre. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anne, da ke zama a tsibirin Mayotte, a Tekun Indiya ta ce: “Mutuwar mahaifiyata ꞌyan shekaru da suka wuce ya sa ni baƙin ciki sosai. Amma ina tuna wa kaina kullum cewa ba Jehobah ne sanadiyyar wahalar da muke sha ba. A maimakon haka, yana marmarin kawar da dukan wahalolin da muke sha, da kuma tā da ƙaunatattunmu da suka mutu. Yin hakan yana ba ni kwanciyar hankali fiye da yadda nake tsammani.”

11. Me ya sa Jehobah ya ƙyale shan wahala, kuma ta yaya hakan zai motsa mu mu riƙa yin waꞌazi?

11 Sanin ainihin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala zai motsa mu mu riƙa yin waꞌazi. Bitrus ya rubuta cewa, Jehobah yana haƙuri ne don yana so mutane su tuɓa su sami ceto. Ya ƙara da cewa: “Wane irin mutane ya kamata ku kasance? Sai ku yi rayuwa mai tsarki, mai hali iri na Allah.” (2 Bit. 3:11) Ɗaya daga cikin “hali iri na Allah” da ya kamata mu kasance da shi, shi ne yin waꞌazi da ƙwazo. Kamar Ubanmu, muna ƙaunar mutane. Muna so su yi rayuwa a sabuwar duniya. Jehobah yana haƙuri da mutanen da ke yankinmu, don su sami damar bauta masa. Saboda haka, muna da babban gata na yin aiki tare da Allah wajen taimaka wa mutane su koya game da shi kafin ƙarshen ya zo!—1 Kor. 3:9.

MUNA RAYUWA A “KWANAKIN ƘARSHE”

12. Ta yaya sanin cewa muna “kwanakin ƙarshe” ya amfane mu?

12 Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda mutane za su zama a “kwanakin ƙarshe.” (2 Tim. 3:​1-5) Halayen mutane a yau sun nuna sarai cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne. Yayin da muke ganin yadda halayen mutane yake daɗa muni, hakan yana ƙara tabbatar mana cewa abin da Allah ya faɗa gaskiya ne.—2 Tim. 3:​13-15.

13. Ta yaya kwatancin da Yesu ya yi a Luka 12:​15-21 zai taimaka mana?

13 Sanin cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe zai sa mu mai da hankali a kan abin da ya fi muhimmanci. Kwatancin da Yesu ya yi a Luka 12:​15-21 (karanta) ya taimaka mana mu ga muhimmancin yin hakan. Me ya sa Yesu ya kira mai arzikin “wawa”? Ba don arzikinsa ba ne, amma domin bai san abin da ya fi muhimmanci a rayuwa ba. “Ya tara wa kansa kaya, amma a gaban Allah ba shi da arziki.” Wannan babban kuskure ne a wurinsa, domin lokaci kaɗan ne ya rage masa. Allah ya gaya masa cewa: “A wannan dare za ka mutu.” Ta yaya wannan labarin zai taimaka mana a yau? Ba da daɗewa ba, ƙarshen wannan zamanin zai zo. Saboda haka, zai dace kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Maƙasudaina suna nuna na fi mai da hankali a kan abubuwan da suka fi muhimmanci? Waɗanne irin maƙasudai ne nake sa yarana su kafa? Ina amfani da ƙarfina, da lokacina, da kuma dukiyata, musamman wajen tara wa kaina arziki ne a duniya, ko a sama?’

14. Ta yaya labarin ꞌYarꞌuwa Miki ya taimaka mana mu ga muhimmancin tuna cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe?

14 Yin tunani a kan abubuwan da suka tabbatar mana cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe zai taimaka mana mu san irin shawarwarin da za mu yanke a rayuwa. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Miki ke nan. Ta ce: “Na so in je jamiꞌa domin in sami damar koya game da dabbobi. Na kuma so in yi hidimar majagaba kuma in ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiyarmu sun ce in yi tunani in ga ko zan iya yin dukan waɗannan abubuwan. Wato, zuwa jamiꞌa, da hidimar majagaba, da kuma ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Sun tuna min cewa ƙarshen zamanin nan zai zo nan ba da daɗewa ba. Kuma sun ce a cikin aljanna, zan sami damar koya game da dukan dabbobi. Shawarar da suka ba ni ta sa na canja raꞌayina. Na koyi sanaꞌa da ba ta bukatar lokaci da karatu da yawa. Hakan ya sa na sami aikin da ya taimaka mini in sami kuɗin biyan bukatuna, kuma in iya yin hidimar majagaba. Daga baya, na ƙaura zuwa Ecuador inda ake bukatar masu shela.” Yanzu, ꞌYarꞌuwa Miki da mijinta suna hidimar masu kula da daꞌira a Ecuador.

15. Me ya sa bai kamata mu fid da zuciya idan mutane ba su saurari waꞌazinmu ba? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)

15 Bai kamata mu fid da zuciya idan mutane ba su saurari waꞌazinmu ba. Me ya sa? Domin da shigewar lokaci, mutane za su iya canjawa. Abin da ya faru da Yakub ɗanꞌuwan Yesu ke nan. A idonsa ne Yesu ya yi girma, ya zama Almasihu, kuma ya koyar da mutane a hanyar da ba a taɓa gani ba. Duk da haka, Yakub bai zama mabiyinsa ba. Bayan Yesu ya tashi daga mutuwa ne Yakub ya zama mabiyinsa, kuma ya yi hakan da ƙwazo!c (Yoh. 7:5; Gal. 2:9) Saboda haka, kada mu ga kamar danginmu da ba sa bauta wa Jehobah ba za su iya yin hakan a nan gaba ba. Ban da haka ma, zai dace mu sake yi wa mutanen da suka ƙi sauraran mu a dā waꞌazi. Ka tuna cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Saboda haka, waꞌazinmu yana da muhimmanci sosai. Abin da muka gaya wa mutane a yau, zai iya ratsa zuciyarsu a nan gaba, mai yiwuwa ma bayan an soma ƙunci mai girma.d

Wata ꞌyarꞌuwa da take yin nazari ta kira ꞌyarꞌuwarta da ba ta bauta wa Jehobah a waya, lokacin da take sayayya a wani shago tare da ꞌyarta.

KA NUNA GODIYA DON ABUBUWAN DA JEHOBAH YAKE TUNA MANA

16. Ta yaya ka amfana daga abubuwan da Jehobah yake tuna mana? (Ka kuma duba akwatin nan “Ka Yi Amfani da Su Wajen Taimaka Ma Wasu.”)

16 Wasu abubuwa da ƙungiyarmu take koya mana daga Littafi Mai Tsarki, an shirya su ne don mutanen da ba su san Littafi Mai Tsarki sosai ba. Alal misali, jawabai ga jamaꞌa, wasu talifofi da bidiyoyi da ke jw.org, da kuma mujallu na waꞌazi. An shirya su ne musamman don waɗanda ba Shaidun Jehobah ba. Duk da haka, mu ma muna amfana daga waɗannan tunasarwar. Suna sa mu ƙara ƙaunar Jehobah, mu ƙara amincewa da Kalmarsa, kuma suna taimaka mana mu ƙware wajen koya ma wasu Littafi Mai Tsarki.—Zab. 19:7.

Ka Yi Amfani da Su Wajen Taimaka Ma Wasu

Idan ka karanta wani talifi, ko ka kalli wani bidiyo, ko kuma ka saurari wani jawabi da aka shirya musamman don mutanen da suke so su koyi gaskiya da ke Littafi Mai Tsarki, ka yi tunanin yadda za ka yi amfani da shi wajen taimaka ma wasu. Ka tambayi kanka:

  • ‘Mene ne aka yi amfani da shi wajen nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batun gaskiya ne?’

  • ‘Shin, akwai kwatanci mai kyau da na ji da zan iya yin amfani da shi wajen koya ma wani gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki?’

  • ‘Waye ne zai iya son wannan batun, kuma a wane lokaci ne za mu iya tattaunawa tare?’

17. A waɗanne yanayoyi ne zai dace mu yi tunani a kan abubuwan da muka koya farko-farko daga Littafi Mai Tsarki?

17 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna farin ciki sosai idan mun sami ƙarin haske a kan wata koyarwarmu. Duk da haka, muna godiya don abubuwan da muka koya farko-farko saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, domin sun taimaka mana mu soma kusantar Jehobah. Kamar yadda muka gani, waɗannan abubuwan da muka koya za su taimaka mana mu karɓi duk wani canjin da aka yi a ƙungiyarmu hannu bibbiyu. Idan ya yi mana wuya mu amince da wani canjin da aka yi, zai dace mu kasance da sauƙin kai, kuma mu tuna cewa Mahaliccinmu mai iko duka ne yake wa ƙungiyarsa ja-goranci. Idan mu ko wani namu yana fama da wata matsala, yin tunani a kan dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala zai taimaka mana mu kasance da haƙuri. Kuma idan ya zo ga batun yadda za mu yi amfani da lokacinmu da kuma dukiyarmu, zai dace mu tuna cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Bari abubuwan da Jehobah yake tuna mana, su sa mu kasance da hikima, kuma mu ci gaba da bauta masa da aminci.

TA YAYA ABUBUWAN NAN DA KA KOYA FARKO-FARKO ZA SU TAIMAKA MAKA A YAU?

  • Jehobah ne Mahalicci

  • Abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala

  • Muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe”

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

a Ka duba 2023 Karin Bayani na 8 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu.

b Ka duba talifin nan mai jigo “Abin Da Ya Sa Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 2007, shafi na 11-15.

c Ka duba darassi na 8 na ƙasidar nan Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su.

d Ka duba talifin nan mai jigo “Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?” da ke Hasumiyar Tsaro ta Mayu 2024, shafi na 8-13.

[Karin Bayanai]

e BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo ya ba da shawarar da sauran dattawa ba su amince da shi ba. Daga baya da dare, ya kalli taurari a sama sai ya yi tunani a kan yawan iko da hikima na Jehobah. Hakan ya tuna masa cewa, abin da Jehobah yake so ne ya fi muhimmanci.

f BAYANI A KAN HOTO: Saꞌad da take nazarin Littafi Mai Tsarki, wata ꞌyarꞌuwa ta bincika abubuwan da suka nuna cewa muna kwanakin ƙarshe. Hakan ya sa ta kira ꞌyarꞌuwarta ta yi mata waꞌazi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba