Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Yuli pp. 8-13
  • Yadda Za Mu Ba Da Shawara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Ba Da Shawara
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IDAN WANI YA CE MU BA SHI SHAWARA
  • YADDA ZA MU BA WA WANI SHAWARA KO DA BAI CE YANA BUKATAR SA BA
  • MUHIMMANCIN BA DA SHAWARA A LOKACI DA KUMA HANYAR DA TA DACE
  • MU CI GABA DA NEMA DA KUMA BA DA SHAWARA
  • Yadda Za Mu Nemi Shawara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka ‘Kira Dattawa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Gargadin da Kake Bayarwa Yana Karfafa Mutane?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • ‘Ka Kasa Kunne Ka Ji Kalmomin Masu Hikima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Yuli pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 29

WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!

Yadda Za Mu Ba Da Shawara

“Zan ba ka shawara, ba zan cire idona a kanka ba.”—ZAB. 32:8.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu ba da shawara da za ta amfani mutane.

1. Waye ne zai iya ba da shawara, kuma me ya sa?

KANA jin daɗin ba wa wasu shawara? Wasu suna jin daɗin yin hakan. Wasu kuma suna jin tsoro, ko su ji wani iri idan za su ba da shawara. Ko da muna son ba da shawara ko aꞌa, a kwana a tashi, za mu bukaci mu ba wa wani shawara. Me ya sa? Domin hanya ce da za mu iya nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Yesu ya ce za a san mabiyansa ta wajen ƙaunar da suke nuna wa juna. (Yoh. 13:35) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Farin cikin abokantaka daga shawara mai kyau ne.”—K. Mag. 27:9.

2. Mene ne ya kamata dattawa su riƙa yi, kuma me ya sa? (Ka kuma duba akwatin nan, “Shawara a Taron Tsakiyar Mako.”)

2 Ya kamata dattawa su san yadda za su ba da shawara mai kyau. Jehobah da Yesu sun ba su hakkin kula da ikilisiya. (1 Bit. 5:​2, 3) Hanya ɗaya da suke yin hakan ita ce, ta wajen ba da jawaban da suke ɗauke da shawarwari daga Littafi Mai Tsarki. Suna ba mu shawara a lokacin da muke bukata, kuma suna taimaka wa waɗanda suka bar bauta wa Jehobah su komo gare shi. Ta yaya dattawa da kuma dukanmu za mu iya ba da shawarwari masu kyau?

Mai kujera a taron tsakiyar mako yana amfani da ƙasidar nan, “Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa” wajen yaba da kuma ba wa wani ɗalibi shawara.

Shawara a Taron Tsakiyar Mako

Idan muka yi wani aiki a taron tsakiyar mako, mai kujeran zai iya ba mu shawara. Yayin da ɗalibi yake gudanar da aikinsa, mai kujeran zai riƙa dubawa ya ga inda ɗalibin ya yi aikinsa da kyau.

Bayan ya gama aikinsa, mai kujeran zai yaba masa. Idan da bukata, zai gaya wa ɗalibin wuraren da ya kamata ya yi gyara cikin basira. Ba ɗalibin ne kawai zai amfana daga irin shawarar nan ba, amma kowa a cikin ikilisiya.—K. Mag. 27:17.

3. (a) Ta yaya za mu koyi ba da shawara mai kyau? (Ishaya 9:6; ka kuma duba akwatin nan, “Ka Riƙa Ba Da Shawara Kamar Yesu.”) (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Za mu koyi ba da shawara mai kyau ta wajen bincika labaran mutane a Littafi Mai Tsarki, musamman labarin Yesu. A Littafi Mai Tsarki, an kira shi, “Mai Ba da Shawara Mai Ban Mamaki.” (Karanta Ishaya 9:6.) A wannan talifin, za mu ga abin da za mu yi idan wani ya ce mu ba shi shawara, da kuma abin da za mu yi idan muna bukatar ba wa wani shawara ko da bai ce mu ba shi shawara ba. Za mu kuma ga muhimmancin ba da shawara a lokaci da kuma hanyar da ya dace.

Ka Riƙa Ba Da Shawara Kamar Yesu

Ga wasu abubuwa da suka sa Yesu ya zama “Mai Ba da Shawara Mai Ban Mamaki,” da kuma yadda za mu yi koyi da shi.

  • Yesu ya san abin da ya kamata ya faɗa. A kullum, ya san abin da ya kamata ya faɗa domin yana ba da shawara ne bisa ga hikimar da Jehobah ya ba shi, ba nasa ba. Shi ya sa ya gaya wa almajiransa cewa: “Maganar da nake yi muku ba da ikon kaina ba ne.”—Yoh. 14:10.

    Abin da muka koya: Ko da mun tsufa ko muna da ilimi sosai, mu tabbata cewa shawarar da muke bayarwa ba namu raꞌayin ba ne, amma daga Kalmar Allah ne.

  • Yesu ya san lokacin da ya kamata ya ba da shawara. Bai gaya wa almajiransa dukan abubuwan da suke bukatar su sani a lokaci guda ba. A maimakon haka, ya jira lokacin da ya kamata, saꞌan nan ya ba su shawara. Kuma ya gaya musu iya abin da za su iya fahimta a lokacin.—Yoh. 16:12.

    Abin da muka koya: Idan za mu ba wa wani shawara, mu jira sai “lokacin yin magana.” (M. Wa. 3:7) Idan muka yi magana da yawa, hakan zai iya rikitar da mutumin ko ya sa shi sanyin gwiwa. Don haka, za mu taimaka masa idan mun gaya masa abin da yake bukatar ya sani ne kawai.

  • Yesu ya san yadda zai ba da shawara cikin ban girma. Sau da yawa ya shawarci manzanninsa a kan yadda za su zama masu sauƙin kai. A duk lokacin da zai yi musu magana game da batun, yakan yi shi ne a hankali kuma cikin ban girma.—Mat. 18:​1-5.

    Abin da muka koya: Ko da muna bukatar mu ba wa mutum shawara sau da yawa a kan abu ɗaya, zai fi saurarar mu idan muka yi shi a hankali da kuma ban girma.

IDAN WANI YA CE MU BA SHI SHAWARA

4-5. Idan wani ya nemi shawara daga wurinmu, me ya kamata mu fara yi? Ka ba da misali.

4 Idan wani ya nemi shawara daga wurinmu, hakan zai iya sa mu farin ciki kuma mu so mu ba da shawara nan tāke. Amma me ya kamata mu fara yi? Zai dace mu fara da tambayar kanmu cewa, ‘Na fahimci batun nan da kyau har zan ba da shawara a kai?’ A wasu lokuta, hanya mafi kyau da za mu taimaka ita ce, mu tura mutumin wajen wanda ya fi fahimtar batun.

5 Ga wani misali. A ce abokinka yana fama da wani ciwo mai tsanani. Kuma ya gaya maka cewa ya riga ya fara bincike a kan yadda zai sami jinya mai inganci. Sai ya ce ka ba shi shawara a kan wanda zai zaɓa. Ko da yake za ka iya kasancewa da naka raꞌayi game da batun, kai ba likita ba ne, kuma ba za ka iya sanin jinyar da za ta fi dacewa ba. A irin wannan yanayin, abin da zai fi alheri shi ne, ka ba wa abokinka shawara yadda zai sami likitan da ya ƙware.

6. Me ya sa zai dace mu ɗan dakata kafin mu ba da shawara?

6 Idan wani ya nemi shawara daga wurinmu, zai dace mu ɗan dakata kafin mu ba shi shawara ko da mun san batun ciki da waje. Me ya sa? Karin Magana 15:28 ta ce: “Zuciyar mai adalci takan yi tunani kafin ta ba da amsa.” Ko da muna ganin mun san abin da za mu faɗa, zai dace mu soma da yin bincike, da yin adduꞌa, da kuma yin tunani game da batun. Idan muka yi hakan, shawarar da za mu bayar za ta jitu da abin da Jehobah yake so. Yanzu, bari mu ga abin da annabi Nathan ya yi.

7. Mene ne za mu iya koya daga labarin annabi Nathan?

7 Sarki Dauda ya gaya wa annabi Nathan cewa yana so ya gina wa Jehobah haikali. Ba tare da ɓata lokaci ba, sai Nathan ya shawarce shi ya yi hakan. Amma da a ce Nathan ya nemi ya san raꞌayin Jehobah kafin ya ba da amsa, da hakan ya fi. Me ya sa? Domin Jehobah bai so Dauda ya gina haikalin ba. (1 Tar. 17:​1-4) Hakan ya nuna cewa, idan aka nemi shawara daga wurinmu, zai dace kada mu yi “saurin magana.”—Yak. 1:19.

8. Wane dalili ne kuma ya sa ya kamata mu yi tunani sosai kafin mu ba da shawara?

8 Ga wani dalilin da ya sa ya kamata mu yi tunani da kyau kafin mu ba da shawara. Idan muka ba wa wani shawara kuma sakamakon bai yi kyau ba, za a iya ɗaura mana laifi. Don haka, yana da muhimmanci sosai mu yi tunani da kyau kafin mu ba da shawara.

YADDA ZA MU BA WA WANI SHAWARA KO DA BAI CE YANA BUKATAR SA BA

9. Kafin dattawa su ba da shawara, me ya kamata su tabbatar tukuna? (Galatiyawa 6:1)

9 A wasu lokuta, wajibi ne dattawa su ba wa wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa shawara, idan suka ga cewa sun soma yin abin da bai kamata ba. (Karanta Galatiyawa 6:1.) Mai yiwuwa mutumin ya soma yin wasu abubuwan da za su sa shi ya yi zunubi. Dattawa za su so su taimaka wa irin mutumin nan don ya ci gaba da bauta wa Jehobah, kuma ya sami rai na har abada. (Yak. 5:​19, 20) Don shawarar ta zama da amfani, zai dace su tabbata cewa mutumin ya yi kuskure tukuna. Ban da haka, zai dace su tuna cewa kowa yana da ꞌyancin yanke shawarwari bisa ga abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki. (Rom. 14:​1-4) Amma idan dattawa suna da tabbaci cewa wani ya yi abin da zai ɓata dangantakarsa da Jehobah, yaya ya kamata su ba shi shawara?

10-12. Idan dattawa suna ba wa wani shawara da bai san yana bukata ba, me ya kamata su yi? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)

10 Bai da sauƙi dattawa su ba wa wani shawara. Me ya sa muka ce hakan? Manzo Bulus ya ce a wasu lokuta mutum ba zai san cewa yana bukatar shawara ba. Don haka, kafin dattawa su ba wa mutum shawara, akwai abubuwan da ya kamata su yi don ya yi wa mutumin sauƙi ya amince da shawararsu.

11 Ka yi laꞌakari da wannan misalin: A ce wani yana so ya shuka iri a wurin da yake da tauri. Dole ne ya gyara wurin, ya sa ƙasar ta yi laushi, kafin ya shuka irin. A ƙarshe, sai ya yi ban ruwa don irin ya yi girma. Haka ma, akwai abubuwan da ya kamata dattijo ya yi don ya yi wa mutum sauƙi ya karɓi shawarar da zai ba shi. Alal misali, ya kamata dattijo ya nemi lokacin da ya dace ya gaya wa ɗanꞌuwan cewa ya damu da shi, kuma akwai abin da yake so ya gaya masa. Idan an san dattijo da nuna ƙauna da kuma alheri, zai yi wa mutane sauƙi su karɓi shawararsa.

12 Saꞌad da suke tattaunawa, dattijon zai iya sa ya yi wa ɗanꞌuwan sauƙi ya karɓi shawararsa idan ya gaya masa cewa, kowa ma yakan yi kuskure kuma ya bukaci shawara. (Rom. 3:23) Zai dace dattijon ya yi magana a hankali da kuma ban girma. Kuma ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki ya nuna masa cewa ya yi kuskure. Idan ɗanꞌuwan ya fahimci cewa ya yi kuskure, sai dattijon ya bayyana masa dalla-dalla yadda zai yi wasu canje-canje. Bayan sun gama tattaunawa, dattijon zai iya sa ya yi wa mutumin sauƙi ya karɓi shawarar ta wajen gaya masa wasu abubuwa masu kyau da yake yi, da kuma yin adduꞌa tare da shi.—Yak. 5:15.

Hotunan da suka kwatanta yadda wani dattijo yake ba wa wani shawara, da shuka iri a wurin da ke da ƙarfi. Na 1. Tona ƙasa: Manomi yana tona ƙasa; dattijon yana yi wa wani ɗanꞌuwa magana a hankali da kuma ban girma. Na 2. Shuki: Manomin ya saka irin a inda ya tona; dattijon yana amfani da Littafi Mai Tsarki wajen tattaunawa da ɗanꞌuwan. Na 3. Ban ruwa: Manomin yana zuba ruwa a wurin da ya saka irin; dattijon yana adduꞌa tare da ɗanꞌuwan.

Idan dattawa suna nuna ƙauna, zai yi wa mutum sauƙi ya karɓi shawarar da bai yi tsammaninsa ba (Ka duba sakin layi na 10-12))


13. Ta yaya dattawa za su tabbata cewa mutumin da suke ba wa shawara ya fahimce su?

13 A wasu lokuta, wanda ake ba wa shawara, ba ya yawan fahimtar abin da wanda yake ba shi shawarar yake faɗa. Mene ne dattawa za su yi domin kada hakan ya faru? Dattawa za su iya yin wasu tambayoyi don su tabbatar cewa mutumin ya fahimci abin da suke ƙoƙarin gaya masa, da irin canje-canjen da ya kamata ya yi. Kuma su yi hakan cikin basira.—M. Wa. 12:11.

MUHIMMANCIN BA DA SHAWARA A LOKACI DA KUMA HANYAR DA TA DACE

14. Me ya sa bai kamata mu ba da shawara saꞌad da muke fushi ba?

14 Mu ajizai ne, shi ya sa a wasu lokuta za mu iya yi, ko faɗan abin da zai ɓata wa wasu rai. (Kol. 3:13) Littafi Mai Tsarki ya ce a wasu lokuta, za mu iya yin abin da zai sa wasu fushi. (Afis. 4:26) Amma kada mu ba da shawara saꞌad da muke fushi. Me ya sa? “Saboda fushin mutum ba ya kai shi ga aikata adalcin Allah.” (Yak. 1:20) Idan mun ba da shawara cikin fushi, hakan zai iya sa yanayin ya ƙara muni. Hakan ba ya nufin ba za mu gaya wa mutumin yadda ya ɓata mana rai ba. Amma zai dace mu jira sai mun daina fushi kafin mu yi magana da mutumin. Za mu iya yin koyi da yadda Elihu ya ba wa Ayuba shawara.

15. Me za mu iya koya daga yadda Elihu ya bi da Ayuba? (Ka kuma duba hoton.)

15 Elihu ya yi kwanaki yana sauraron Ayuba, a lokacin da yake bayyana cewa abin da abokansa ukun nan suka faɗa ba gaskiya ba ne. Elihu ya ji tausayin Ayuba. Amma, a lokacin da Ayuba yake ƙoƙarin kāre kansa, ya faɗi wasu abubuwan da ba gaskiya ba game da Jehobah, kuma hakan ya sa Elihu fushi sosai. Elihu ya daina fushi kafin ya ba wa Ayuba shawara cikin ban girma. (Ayu. 32:2; 33:​1-7) Akwai darasi mai muhimmanci da za mu iya koya daga yadda Elihu ya bi da Ayuba. Yana da kyau mu daina fushi kafin mu ba da shawara, kuma mu yi shi cikin ƙauna da ban girma.—M. Wa. 3:​1, 7.

Elihu yana sauraron Ayuba kuma ya tausaya masa, da yake ƙuraje sun rufe dukan jikinsa.

Elihu ya yi fushi sosai don abin da Ayuba ya faɗa, amma ya daina fushi kafin ya yi wa Ayuba magana. Kuma ya yi hakan cikin ban girma (Ka duba sakin layi na 15)


MU CI GABA DA NEMA DA KUMA BA DA SHAWARA

16. Wane darasi ne za mu iya koya daga Zabura 32:8?

16 Ayar da aka ɗauko jigon talifin nan ta ce, Jehobah zai ‘ba mu shawara, ba zai cire idonsa a kanmu ba.’ (Karanta Zabura 32:8.) Hakan ya nuna cewa zai ci gaba da taimaka mana. Ba shawara kawai zai ba mu ba, amma zai taimaka mana mu yi amfani da ita. Mu ma za mu iya yin koyi da Jehobah! Idan za mu ba wa wasu shawara, zai dace mu ci gaba da ƙarfafa su kuma mu taimaka musu su yanke shawarwari masu kyau.

17. Yaya muke ji saꞌad da dattawa suka ba mu shawara daga Littafi Mai Tsarki? (Ishaya 32:​1, 2)

17 Yanzu ne ya fi dacewa mu riƙa nema da kuma ba da shawara. (2 Tim. 3:1) Kamar yadda “ꞌyan rafuffuka cikin dajin yashi” suke sa mutum ya wartsake, haka ma dattawan da suke ba da shawarwari daga cikin Littafi Mai Tsarki suke ƙarfafa mu. Kuma suna taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah. (Karanta Ishaya 32:​1, 2.) Muna alfahari da abokan da ba sa jinkiri wajen ba mu shawarar da muke bukata. Shawararsu na kama da “adon zinariyar da aka yi a kan azurfa.” (K. Mag. 25:11) Bari dukanmu mu ci gaba da nema da kuma ba da shawarwari masu kyau.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya kamata mu tuna idan wani ya nemi shawara daga wurinmu?

  • Me ya kamata mu tuna idan muna ba da shawara ga wani da bai san yana bukata ba?

  • Me ya kamata mu tuna idan muna fushi?

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba