SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Ka Koyi Darasi Daga Hotuna
Littattafanmu suna da hotuna da yawa da ke ɗauke da darussa masu muhimmanci. Ta yaya za ka yi amfani da hotunan nan a hanyar da za ka amfana?
Ka duba Hotunan kafin ka karanta talifin. Hotunan za su iya sa ka yi marmarin sanin abin da ke talifin kuma hakan zai sa ka karanta shi. Idan ka ga abinci mai daɗi da aka dafa, za ka yi marmarin cin sa. Ko ba haka ba? Don haka, kafin ka soma karanta talifin ka tambayi kanka, ‘Me na gani?’—Amos 7:7, 8.
Yayin da kake karanta talifin, ka yi tunanin abin da ya sa aka sa hotunan. Ka karanta abin da aka rubuta a kan hoton da bayani a kan hoton idan akwai. Ka yi tunani a kan alaƙar da ke tsakanin hoton da talifin da kuma yadda za ka iya yin amfani da abin da ka koya daga hoton a rayuwarka.
Bayan ka gama karanta talifin, ka sake duba hotunan, kuma ka yi amfani da su don ka tuna abubuwan da ka koya. Ka rufe idanunka kuma ka yi ƙoƙari ka tuna abin da ka gani a hoton da abin da hoton ya koya maka.
Ka sake duba hotunan da ke mujallar nan don ka ga ko za ka iya tuna abubuwan da ka koya.