Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w22 Fabrairu p. 31
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Ya San Kasawarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
w22 Fabrairu p. 31

Ka Sani?

Me ya sa ya yi kyau da Jehobah ya yarda Isra’ilawa su ba da hadaya da tsuntsaye iri biyu?

A ƘARƘASHIN Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, Jehobah ya yarda Isra’ilawa su ba da hadaya da kurciyoyi da kuma tattabaru. Akan ambata tsuntsayen nan tare a dukan dokoki da aka bayar game da hadaya, kuma za a iya ba da ɗaya maimakon ɗayan. (L. Fir. 1:14; 12:8; 14:30) Me ya sa hakan yake da amfani? Dalili ɗaya shi ne domin ba a kowane lokaci ne ake samun kurciyoyi ba. Me ya sa?

Kurciya

Kurciyoyi tsuntsaye ne da suke ƙaura kuma lokacin zafi ne kawai ake samun su a ƙasar Isra’ila. A kowane watan Oktoba, suna ƙaura kudu zuwa ƙasashen da ake zafi kuma su dawo Isra’ila a lokacin damina. (W. Waƙ. 2:11, 12; Irm. 8:7) Hakan yana nufi cewa a zamanin dā a Isra’ila, yana da wuya mutum ya ba da hadayar kurciya a lokacin sanyi.

Tattabara

Amma tattabaru ba sa ƙaura. Domin haka, ana iya samun su a kowane lokaci a Isra’ila. Ban da haka, ana kiwon tattabaru. (Ka duba misalin da ke Yohanna 2:14, 16.) Littafin nan Bible Plants and Animals ya ce: “Ana kiwon tattabaru a kowane ƙauye da gari a yankin Falasdinu. Kowane mai gida yana da gidan tattabaru ko kuma rami a bango da tsuntsayen suke zama.”​—Ka duba misalin da ke Ishaya 60:8.

Tattabara a gidanta

Jehobah ya nuna cewa shi mai ƙauna ne da kuma sanin yakamata ta wajen amincewa Isra’ilawa su ba da hadayar tsuntsaye da za a iya samu a kowane lokaci a cikin shekara.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba